Yadda Taron Kasa-Da-Kasa Na Bitar Hausa a Jami’ar Ahmadu Bello ya gudana

A ranar Talatar makon da ya gabata ne aka gudanar da gagarumin taron kwana uku a Jami’ar Ahmadu Bello, wanda ya tattara masana harsunan Afrika daga sassan duniya daban-daban, domin bita a kan harshen Hausa. Shugaban Sashen Harsuna Da Al’adun Afrika na jami’ar, Dakta Salisu Garba Kargi, ya gabatar da jawabin maraba, inda ya bayyana […]

Yadda Taron Kasa-Da-Kasa Na Bitar Hausa a Jami’ar Ahmadu Bello ya gudana

A ranar Talatar makon da ya gabata ne aka gudanar da gagarumin taron kwana uku a Jami’ar Ahmadu Bello, wanda ya tattara masana harsunan Afrika daga sassan duniya daban-daban, domin bita a kan harshen Hausa. Shugaban Sashen Harsuna Da Al’adun Afrika na jami’ar, Dakta Salisu Garba Kargi, ya gabatar da jawabin maraba, inda ya bayyana dalilai da makasudin shirya wannan gagarumin taro. Ga abin da ya bayyana:

Muna yi wa kowa da kowa maraba, saboda amsa kiranmu da aka yi, duk da dimbin hidimomin da ke gaban jama’a, musamman manyan kasa masu dauke da nauyin dimbin al’umma da tarin ayyukan ofis. Allah Ya kara girma da zumunci kuma ya saka wa kowa da alheri. Muna fatar yadda Allah Ya kawo kowa lafiya, Ya sa a yi taro lafiya kuma kowa ya koma gidansa lafiya.

Bayan haka, alal hakika yau rana ce mai muhimmanci kuma mai dimbin tarihi ga wannan Sashe da wannan muhimmiyar Jami’a, musamman idan aka yi la’akari da manufar wannan taro, na bayyanar da matsayin harshen Hausa a Najeriya da duniya baki daya.

Sanannen abu ne kuma tabbatacce cewa, bunkasar harshen Hausa da habakarsa a yau, ya isa ya zama harshen kasa, ta yadda za a dinga gudanar da harkokin mulki da shi, a Najeriya. Wannan dalili ya sa aka shirya taron ranar Talata, 26 ga Nuwamba, 2016 domin kara tabbatar da matsayin harshen Hausa, ba a Najeriya kawai ba, har da nahiyar Afirka baki daya.

Wancan taro ne ya bukaci lallai a kira babban taron kasa-da-kasa wanda zai game fannoni daban-daban don samar da cikakken bayani a kan al’ummar Hausawa da ire-iren albarkatun da ke jibge a cikin kasarsu.

Makasudin Taro:

Sauke nauyin da ke kanmu na raya harshen Hausa da bunkasa al’adun Hausawa. Zaburar da Hausawa game da daraja da kimar harshen Hausa. Haka kuma taron zai taimaka wajen fito da kasar Hausa da alkiblarta a sabuwar Najeriya. Musamman a wannan yanayi da ake ciki game da sake fasalta kasa a siyasa

nce, ta yadda har wasu ke kallon Arewa a matsayin ci-ma-zaune. Samar da wani babban kundi game da kasar Hausa da Hausawa, daga makalolin dam asana da manazarta daga fagagen ilimi daban-daban za su gabatar, saboda kanun taron ya game komai da komai na tasarrufin al’umma. Misali, sha’anin Mulkinsu da Tattalin Arzikinsu da Zamantakewarsu da Tarihinsu da Fasaharsu da kere-kerensu da Likitancinsu da Kimiyyarsu da Kasuwancinsu da Huldarsu da yanayin kasarsu da Muhallinsu da Sana’o’insu da kuma dukkan mu’amalarsu ta rayuwa.

Yunkurin Da Wannan Sashe Yake Yi (Nasarori):

Wannan Sashe ya dade yana yunkuri don ganin wannan mafarki ya tabbata saboda kishin harshen Hausa da kuma kokarin ’yantar da al’ummar Hausawa da kangin mulkin mallaka. Samuwar haka ne kawai zai bayar da damar cin gajiyar dimbin fasahar al’ummar Hausawa da kuma albarkatun da Allah Ya jibge a cikin kasarsu. Misali:

Sashe ya gudanar da bincike a matakin Digirin Koli (PhD) a kan harshen: Gbagy da Eggon da Kulung (Jihar Taraba) da Fulfulde da Bachama da Badanci da Ayu. Sai kuma matakin Digirin Tsakiya (MA); Teranci, C’lela (Dakkarci) da Kuramanci (Zaar) da Koro. Game da matakin Digirin Farko (BA) kuwa, an game mafiyawancin harsuna da al’adun Arewacin kasar nan da bincike tare da taskace al’adunsu da fasaharsu.

Sashe ya kokarta gabatar da bukatar kyautata Taskar Fasahar Baka, ga hukumar Jami’a tare da samar da Zayyana da kiyasin kudin da zai iya kyautata wannan taska dacewarta da zamani.

Sashe ya kokarta samar da ma’anonin kebabbun kalmomi masu yawa daga kowane fanni na wannan jami’a cikin harshen Hausa kuma har yanzu ana ci gaba da wannan aiki, don saukaka koyo da koyarwa a cikinsu.

Sashe ya kammala bitar kundin kebabbun kalmomin da aka samar a 1978, a karkashin jagorancin Farfesa Dalhatu Muhammad, don koyar da harshen Hausa cikin Hausa ga daliban Hausa, daga kalma 5000 zuwa kalma 15,000 tare da takaitaccen tsokaci a kan kowacce kalma.

Samar da wata cibiya wadda za a taskace a kuma adana kayayyakin Hausawa na gargajiya, wanda a yanzu haka har Sashe ya sami wuri, an zayyana cibiyar tare da kiyasin kudin da ake bukata, sai dai bukatar samun wadanda za su gina ta don ta fara aiki gadan-gadan.

Karfafa dangantaka da kafafen yada labarai, wanda a yanzu haka da dangantaka ta kyautatu tsakanin wannan Sashe da kafafen yada labarai, musamman FRCN Kaduna, KSMC Kaduna da Alheri Rediyo da Kungiyar ’Yan Jarida, Reshen Zariya.

Godiya ga Hukumar Jami’a saboda goyon bayan da take ba wannan Sashe a duk lokacin da ya yi wani yunkuri, Walin Hausa, Mai Shari’a Umar Abdullahi, saboda gudunmowar da yake bayarwa ta kudi da lokacinsa da jikinsa don bunkasa wannan Sashe, da Alhaji Lema Jibrilu, Dan Iyan Katsina da Gidauniyar Dakta Bukar Usman, saboda gudunmowar kudin da suka bayar don aiwatar da wannan muhimmin taro. Haka kuma ya zama dole mu mika godiyarmu ta musamman ga malamai masu gabatar da makaloli duk da dimbin aikin da ke gabansu, da sauran abokan aiki na wannan Sashe da sauran Sassan Tsangayar Fasaha, irin su Farfesa Sani Abba Aliyu da Farfesa Abubakar Aliyu Liman, sannan kuma dole mu yi godiya da jinjina ga malamai da ma’aikatan Sashe saboda jajircewarsu a kan shirya wannan taro da tsayuwarsu ba dare ba rana.

Allah Ya saka wa kowa da alheri kuma ya mayar da kowa gida lafiya.

Yadda taron ya gudana:

Masana a fannonin harsunan Afrika da suka halarci babban taron, sun bayyana cewa lokaci ya yi da za a fara amfani da harshen Hausa a matsayin harshen kasa a Najeriya, musamman ganin yadda ya samu amsuwa a dukkan sassan kasar nan da Afrika da ma duniya baki daya.

Taron mai taken ‘Al’ummar Hausa: Jiya Da Yau Da Gobe’ an gudanar da shi ne tsawon kwanaki uku, ya hada masana harsuna daga sassa daban-daban na duniya, wadanda suka nuna cewa bisa la’akari da yadda harshen ya samu amsuwa, lokaci ya yi da za a dabbaka shi domin ya zama harshen kasa, wanda al’umma za su rika gudanar da al’amuransu na yau da kullum a cikinsa, wanda haka zai taimaka wajen kawo hadin kan kasa da bunkasa tattalin arziki da saukaka al’amuran mulki da siyasa a Najeriya.

Shugaban taron, Walin Hausa, Mai Shari’a Umaru Abdullahi ya kalubalanci masana harshen na Hausa da su maida hankali wajen gudanar da bincike sosai ta yadda harshen zai kara bunkasa, ta yadda za a daina ganin al’ummar Hausawa a matsayin cima-zaune, alhalin kuwa su ne ma suka gina kasar nan, tare da tabbatar da hadin kanta, balle kuma a yanzu harshen ya bunkasa, yadda ya buwaya a duniya, ba ma Najeriya ko Afrika kadai ba.

Shi kuwa a nasa jawabin, Farfesa Dandatti Abdulkadir a matsayinsa na Shaihun Malami a fannin Hausa, ya bayyana yadda harshen ya samu tagomashi a duniya, yadda manyan kasashe, musamman Birtaniya, Amurka, Jamus, Faransa da China da sauransu suke amfani da shi wajen bunkasa mu’amalarsu da kasashen Afrika. Ya yi kira da babbar murya ga gwamnonin Arewa da sauran masu rike da madafun iko da su hanzarta sanya harshen Hausa a matsayin harshen hukuma a dukkan fadin Arewa, daga bisani kuma a yi hobasa domin ganin ya zama harshen kasa baki daya.

“Harshen Hausa ya bunkasa a duniya, yana daya daga cikin harsunan Afrika na sahun farko da BBC suka fara amfani da shi wajen watsa labarai a duniya, wanda kuma yake da miliyoyin masu saurare a dukkan fadin duniya. Harshen yana da dukkan abubuwan da ake bukata domin ya zama harshen kasa. Don haka, ya kamata ’yan siyasarmu, musamman gwamnonin Arewa da su sanya shi ya zama harshen hukuma a dukkan fadin Arewa, sannan kuma su yi kokarin ganin ya zama harshen kasa, nan ba da jimawa ba.” Inji Farfesa Dandatti.

Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Ibrahim Garba, shi ma a nasa jawabin, ya bayyana bukatar a yi kokarin tabbatar da harshen Hausa ya zama harshen kasa, musamman saboda yadda ya bunkasa kuma ya mamaye ko’ina a Najeriya da nahiyar Afrika. Kamar yadda ya ce: “Mu nan a Jami’ar Ahmadu Bello, mun amince da cewa harshen Hausa yana da kima da daraja, yadda ya karade ko’ina, musamman makwabtan kasashe da al’ummomin Afrika. Harshe ne na koyo da koyarwa, kuma yana taimakawa wajen samar da hadin kai tsakanin mabambantan al’umma.”

A nasa jawabin, Shugaban Sashen Nazarin Al’adu Da Harsunan Afrika na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Dokta Salisu Garba Kargi, ya bayyana cewa sun shirya wannan gagarumin taro ne da nufin jaddada wa al’ummar duniya matsayin da harshen Hausa ya kai. “Sanannen abu ne kuma tabbatacce cewa, bunkasar harshen Hausa da habakarsa a yau, ya isa ya zama harshen kasa, ta yadda za a dinga gudanar da harkokin mulki da shi, a Najeriya. Wannan dalili ya sa aka shirya taron ranar Talata, 26 ga Nuwamba, 2016 domin kara tabbatar da matsayin harshen Hausa, ba a Najeriya kawai ba, har da nahiyar Afrika baki daya.

“Wancan taro ne ya bukaci lallai a kira babban taron kasa da kasa, wanda zai game fannoni daban-daban don samar da cikakken bayani a kan al’ummar Hausawa da ire-iren albarkatun da ke jibge a cikin kasarsu.” Inji Dokta Kargi.

Sauran masanan da suka gabatar da takardu kuma suka jaddada inganci da buwayar harshen Hausa, sun hada da Farfesa Isma’ila Junaidu, Babban Sakataren Hukumar Tsara Manhaja ta kasa (NERDC), Abuja da Farfesa Al-amin Abu Manga, na Cibiyar Nazarin Al’amuran Afrika da Asiya, Jami’ar Khartoum, Sudan da Farfesa Nina Pawlak ta Cibiyar Nazarin Kasashen Gabas, Sashen Harsuna da Al’adun Afrika, Jami’ar Warsaw, Poland da kuma Malam Abubakar Mahamman, Shugaban Kungiyar Marubuta Harsunan Kasa (ASSAUNIL), Niamey, Jamhuriyar Nijar.