Yadda taron Kungiyar Lauyoyi ya hada ’yan takarar Shugaban Kasa
Taron ya gudana ne ranar Litinin a Otel din Eko Hotels and Suites da ke yankin Victoria Island a Legas.
Jiga-jigan ’yan takarar Shugaban Kasa na manyan jam’iyyun Najeriya a babban zaben 2023, sun halarci taron shekara-shekara na Kungiyar Lauyoyi ta Najerita (NBA).
Taron wanda shi ne karo na 62 ya gudana ne ranar Litinin a Otel din Eko Hotels and Suites da ke yankin Victoria Island a Legas.
- Idan Atiku ya yi wasa zai sha kasa a Zaben 2023 —Wike
- Burin neman matsayi bai kai dan takara ga nasara a Najeriya- Kashim Shetima
Mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ne ya soma bude taron da jawabi.
A bayyana taken taron na bana a matsayin taro mafi girma na Lauyoyi a doron kasa.
Babban Alkalin Jihar Legas, Mai shari’a Kassim Alogba da ya wakilci mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya CJN, ya yaba wa Shugaban Kungiyar NBA, Olumide Akpata bisa halayensa na jagoranci nagari.
Wadanda suka halarci bikin bude taron sun hada da: Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, kuma dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023. Sai Peter Obi, dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP da kuma Mataimakin Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Kashim Shettima.