Yadda taron rantsar da shugabannin Gizagawan Kudancin Najeriya ya gudana

Wakilinmu a Ibadan, Kabir Yayo Ali ya halarcin zauren taron rantsar da shugabannin Gizagawan jihohin Kudancin Najeriya kuma ya aiko mana da rahoton yadda taron ya gudana kamar haka:A ranar Asabar da ta gabata ce Shugaban kungiyar Gizagawa na kasa baki daya, Alhaji Sheriff Auwal Falala ya rantsar da sababbin shugabanni tara da za su […]

Yadda taron rantsar da shugabannin Gizagawan Kudancin Najeriya ya gudana
Yadda taron rantsar da shugabannin Gizagawan Kudancin Najeriya ya gudana

Wakilinmu a Ibadan, Kabir Yayo Ali ya halarcin zauren taron rantsar da shugabannin Gizagawan jihohin Kudancin Najeriya kuma ya aiko mana da rahoton yadda taron ya gudana kamar haka:
A ranar Asabar da ta gabata ce Shugaban kungiyar Gizagawa na kasa baki daya, Alhaji Sheriff Auwal Falala ya rantsar da sababbin shugabanni tara da za su jagoranci kungiyar na tsawon shekaru 3 a sashen Kudu Maso Yamma mai kunshe da jihohin Legas da Ogun da Oyo da Osun da Ondo da Ekiti.
An gudanar da bikin rantsar da sababbin shugabannin ne a unguwar Sabo cikin birnin Ibadan. Bikin na yini daya ya samu halartar Gizagawa daga sassa daban-daban na kasa.
An rantsar da Shugaban kungiyar Gizagawa na Jihar Ondo, Malam Aminu Ibn Umar, a matsayin sabon Shugaba na shiyyar Kudu-Maso-Yamma. Sauran Gizagawa takwas da za su rufa masa baya kuma suka yi rantsuwar fara aikin sada zumunta sun hada da Shugaban kungiyar na Jihar Oyo, Alhaji Yusuf Salisu da Malam Mansur A. Inuwa da Aminu Isa, dukkansu daga Jihar Oyo da Malam Sama’ila Muhammea Madawa da Auwal Garba danfari da Salisu Shehu Shanono, su kuma daga Jihar Ogun da Muhammed Tijjani daga Jihar Ondo da Malam Idris Nagora daga Jihar Legas.
Cikin jawabinsa ga mahalarta bikin, Shugaban kungiyar Gizagawa na kasa Alhaji Sheriff Awal Falala, ya tunatar da sababbin shugabannin a game da hakuri: “Domin shugaba ko jagora shi ne majibincin jama’a saboda haka sai mu rika hakuri da jama’a da kyautata musu tare da yin manuniya cewa, zumunci shi ne makasudin haduwarmu da muke kashe dimbin kudadenmu da jingine ayyukanmu domin gudanar da wannan aiki na ibada kamar yadda Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) ya ce, wanda yake son a tsawaita masa rayuwarsa kuma a yalwata masa arzikinsa, to, ya sadar da zumuncinsa.”
Saboda haka sai ya nemi dukkan ’ya’yan kungiyar su zage damtse wajen yin aiki da wannan ingattaccen hadisi. “Kuma ya kamata mu tabbatar da ganin mun sauke nauyin da muka dora wa kanmu wajen aiwatar da manufofin kungiyar Gizagawa ta fannin yawaita ziyartar manyan malamai da attajirai domin karuwa da shawarwarinsu da tallafa wa gajiyayyu da marayu da ziyartar marasa lafiya a asibitoci da ziyartar gidajen yari, domin yi musu nasiha da bayar da tallafin abun da ya sawwaka.”
Shugaban wanda ya jinjina wa Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Aminiya da Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust, musamman jaridar Aminiya wacce ita ce ta fito da kungiyar Gizagawa a idon duniya, ya ce babu ruwan kungiyarsu da harkokin siyasa domin kowa nata ne. “Babu ruwan kungiyarmu da siyasa ko neman mukami amma, wannan ba zai hana mu kai ziyara ga dukkan dan siyasa da ke goyon bayan kowace jam’iya wanda ya zama mutumin kirki da yake gudanar da ayyukan alheri domin ci gaban jama’a ba, domin mu karfafa masa gwiwar ci gaba da aikin alheri.”
Bayanan irin nasarorin sada zumunci da kungiyar ta gudanar tun daga kafuwarta sun yi kicibis da wasu manyan matsaloli da kungiyar ta samu kanta a ciki wanda Shugaba Sheriff Awal Falala, ya nuna takaici dangane da haka. “Babbar matsalarmu a yanzu ita ce rashin babban ofis ko sakatariya da kungiya za ta rika gudanar da harkokinta a ciki kuma masu sha’awar shiga cikin kungiya sun waye da wurin da za su tuntube ta. Wani ofishin wucin gadi mallakar tsohon Sakataren kungiyar Malam Kabiru Sakaina da ke garin Malunfashi, shi ne muke amfani da shi a yanzu. Na gabatar da wannan kuduri ga wakilan majalisata da muka fara tattaunawa a game da zabar daya daga cikin garuruwan Abuja ko Kano ko kuma Kaduna da zai zama hedkwatar Gizagawa ta kasa baki daya.” Inji shugaban.
Sai kuma batun katin shaida wato (ID Card) na bai daya da kungiyar ke fafutukar ganin kowane memba ya fara amfani da shi ba kamar yadda kowane reshen jiha yake amfani da irin nasa daban ba. A nan sai ya nemi ’ya’yan kungiya da dukkan al’ummar kasa, musamman masu hannu da shuni su taimaka wa kungiyar domin cin ma burinta.
Shi ma Mataimakin Shugaban kungiyar Gizagawa na kasa, Malam Auwal Ahmad LK, ya nuna farin cikinsa ne da zabar birnin Ibadan da kungiyar ta yi a matsayin wurin taron rantsar da sababbin shugabannin. Ya karanto ayoyin Alkur’ani da hadisan Annabi Muhammad (SAW) da suka shafi alherin da ke cikin sada zumunta a tsakanin al’umma.
Daga cikin manyan baki da suka halarci taron na Ibadan sun hada da Malam Musa Aliyu Na Musamman, wanda ya wakilci Shugaban reshen shiyyar Arewa ta tsakiya da Shugaban reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Sama’ila Muhammed da Sakataren shiyyar Arewa ta tsakiya kuma Shugaban Jihar Kogi, Alhaji Ahmed Sulaiman da Shugaban riko na Jihar Legas, Malam Sabo Agege.