Yadda tashar talabijin na BBC Hausa zai gudanar da aikinsa

A ranar Litinin ne tashar BBC ta kaddamar da gidan talabijin din da zai rika yada shirye-shiryensa da Hausa, Aminiya ta tattauna da Shugaban sashen Hausa na BBC Mansur Liman, inda ya yi bayanin yadda za su rika gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin din. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: A ranar Litinin Tashar BBC […]

Yadda tashar talabijin na BBC Hausa zai gudanar da aikinsa

A ranar Litinin ne tashar BBC ta kaddamar da gidan talabijin din da zai rika yada shirye-shiryensa da Hausa, Aminiya ta tattauna da Shugaban sashen Hausa na BBC Mansur Liman, inda ya yi bayanin yadda za su rika gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin din. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: A ranar Litinin Tashar BBC ta kaddamar da gidan talabijin da zai rika yada shirye-shiryensa da Hausa, shin akwai wani tsari da kuka yi ne da zai bambanta da gidan rediyo, kuma ta yaya talakawa za su rika gani a ko’ina ba tare da wahala ba?
Mansur Liman: Tsarin ya bambanta da na rediyo, za a iya kama rediyo ne a gajeren zango (short wabe), amma wannan sabon tsari na gidan talabijin na BBC Hausa, an shi ne ta hadin gwiwa da wadansu gidajen talabijin da ke Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Ghana, da su za mu kulla yarjejeniya don su rika daukar shirye-shiryen da za mu rika gabatarwa, saboda haka za a rika ganin shirye-shiryenmu ta gidajen talabijin din wadannan kasashen da na ambata kamar yadda aka saba.
Aminiya: Da wadanne gidajen talabijin kuka kulla kawancen a Najeriya da kuma sauran kasashe?
Mansur Liman: A halin yanzu mun kulla kawance da gidan talabijin na Adom Tb da ke Ghana, za a iya kallon wannan tashar a kasashen Yammacin Afirka da dama, musamman ma kasashen da suke da tsarin Multi-Tb. A Nijar muna da yarjejeniya da gidan talabijin din Sarauniya, a Najeriya muna da yarjejeniya da gidan talabijin na Capital Tb da ke Kaduna, sannan muna kokarin kulla yarjejeniya da wadansu gidajen talabijin da ke arewacin Najeriya.
Aminiya: Ta bangaren ma’aikata fa, shin ma’aikatanku na rediyo ne za su rika gabatar da shirye-shirye, ko kuwa wadansu ne daban?
Mansur Liman: Shi gidan watsa labarai na BBC makaranta ce guda, saboda haka babu wani irin horo da ba za a iya ba mutum ba, don haka mutanen da suke aikin gidan talabijin na BBC Hausa dama ma’aikatan da suke aikin gidan rediyo ne, sakamakon sabon tsarin gidan talabijin din da tashar BBC ta bullo da shi, sai aka ba su horon yadda za su zama ma’aikatan gidan talabijin, kowa ya san Aishatu Moussa ma’aikaciyar gidan rediyon BBC Hausa da take gabatar da shirye=shirye ce, yanzu haka ita ce mai gabatar da shirye-shirye na wannan gidan talabijin din, akwai Elhadji Diori Coulibaly shi ma ma’aikacin gidan rediyo ne kamar yadda kowa ya sani, akan ji muryarsa sosai kamar yadda akan ji ta Aishatu, shi ne zai rika gabatar da shirye-shirye idan Aishatu Musa ba ta nan, kuma yana daya daga cikin masu tsara shirye-shirye a gidan talabijin din, akwai kuma sauran ma’aikata kamar Isah Sanusi, shi ma ma’aikacin gidan rediyo ne da Djimi Saleh. Ma’aikata ne da suke aiki a gidan rediyo, amma an ba su horon da ya dace, abin da muke sa rai a nan gaba shi ne, duk wani ma’aikacin gidan BBC ko da na Online ne zai samu horon da ake bukata don ya shiga aikin gidan talabijin din,
Aminiya: Yaya za a rika gabatar da shirye-shiryen; za su kasance ba dare ba rana ne, ko an ware wadansu lokuta ne da za a rika gabatar da shirye-shiryen?
Mansur Liman: A yanzu dai muna gabatar da shirin minti 10 ne a kowace rana, wato daga ranar Litinin zuwa Juma’a, a can Landan za mu rika watsa shirye-shirye ne da karfe 9 na dare, wadanda za su kalle shi a Adom Tb za su iya kallonsa karfe 9 agogon Najeriya, wato karfe 8 na dare agogon GMT ke nan, amma sauran abokan kawancenmu na Najeriya, ba za su iya nuna shi kai tsaye ba, za su dauki shirin sai bayan awa daya ko yadda yarjajeniyarmu ta kasance tare da su, sannan su watsa shi, saboda akwai ka’idar da Hukumar  kula da tashoshin rediyo da talabijin (NBC) ta gindaya cewa kafafen yada labarai ba za su rika watsa labarai kai-tsaye daga kafafen yada labarai na kasashen waje ba, don tabbatar da mun cika ka’idar wannan yarjejeniya da hukumar NBC ta gindaya, shi ya sa dukkan gidajen talabijin da muka kulla kawance ba za su iya watsa shirin kai tsaye a Najeriya ba.
Aminiya: A halin yanzu za a rika gabatar da shirye-shiryen ne daga can Landan ko kuwa za ku rika yi daga Najeriya, kamar yadda kuke yi na rediyo?
Mansur Liman: Ko shi kansa rediyo daga Landan muke yi, amma akwai tsare-tsare ko shirye-shirye da muke cewa a yi shi a Najeriya, kamar yadda aka sani, muna da ma’aikata a Najeriya idan suna da labari sai su tura mana, to shi ma haka na gidan talabijin din akwai mutanen da muka ba su horo a Najeriya, idan akwai labarin da muke ganin zai iya shiga cikin shirye-shiryen gidan talabijin din, to sai su tura mana.