Yadda tashe ya hada kan Hausawa da Yarabawa a Legas

Ga dukkan alamu wasan tashe da Hausawa ke yi duk shekara a cikin watan azumi ya samu karbuwa ga kabilar Yarabawa, inda yaran Yarabawa da na Hauswa ke yin tashen a tare.Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa wani lokaci mutum ba zai ya bambance yaran Yarabawa a cikin Hausawan da ke yin tashe […]

Yadda tashe ya hada kan Hausawa da Yarabawa a Legas
Yadda tashe ya hada kan Hausawa da Yarabawa a Legas

Ga dukkan alamu wasan tashe da Hausawa ke yi duk shekara a cikin watan azumi ya samu karbuwa ga kabilar Yarabawa, inda yaran Yarabawa da na Hauswa ke yin tashen a tare.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa wani lokaci mutum ba zai ya bambance yaran Yarabawa a cikin Hausawan da ke yin tashe a Legas ba saboda irin yadda suke yin komai tare ba tare da nuna alamar bambanci ba.
Aminiya ta gano cewa a kan yi tashen ne a yankunan da Hausawa suke zaune a sassa da dama na Jihar Legas kamar unguwar Agege da Idi Araba da cikin birnin Ikko da sauran wurare da dama.
Wani matashi da Aminiya ta tattana da shi mai suna Nura Muhammad, ya bayyana cewa Yarabawa suna nuna mutukar sha’awar tashe a Legas.
Ya ce: “Tare muke tafiya kuma tare muke yin komai. Da ma suna jin Hausa saboda da yawa a gida daya muke zaune ko a unguwa daya. Saboda haka idan muna yin amshi ko yin waka duk tare muke yi suma sun iya.”
Shi ma wani Bayarabe mai suna Kayode, ya bayyana cewa babu tashen da bai iya ba kuma ba wakar tashen da bai iya amshinta ba.
“Na iya dukkan wakokin tashen Hausawa, na iya koroso, na iya dan Kokawa, na iya wakar Ka Yi Rawa Malam da wakar Mairama ga Daudu da sauransu da yawa. Na taso tare da Hausawa, tare muke zaune a gida daya, tare muke cin abinci, tare muke kwanciya, tare muke zuwa makaranta ba wani bambanci.”
Da Aminiya ta tuntubi mai unguwar Markaza kuma magatakardar masarautar Hausawan Agege, Alhaji Abubakar Aliyu Na’ibi, ya bayyana cewa ba kabilun Yarabawa ne kawai ke bin Hausawa tashe ba har da sauran kabilun Arewa baki daya.
“Ba Yarabawa ba ne suke yin tashe, kabilunmu na Arewa kamar Igala da Ibira da Nufawa duk suna tashe tare da Hausawa kuma an samu haka ne saboda majalisa daya da sarkin Hausawan Agege ya kafa wacce ta kunshi dukkanin sauran kabilun Arewa a cikinta. Kuma dangantakar da ke tsakanin ’yan Arewa da kabilun Yarabawa tun fiye da shekaru 200 ta taimaka wajen samar da wannan zumunci a tsakani.” In ji shi.