Yadda tazarar haihuwa za ta rage mace-macen masu juna biyu

Amfanin ba da tazarar haihuwa ga lafiyar mata daga kwararren likita.

Yadda tazarar haihuwa za ta rage mace-macen masu juna biyu

Nigeria, Katsina.
October-November 2009.
Turai Jaradua maternal and children Hospital.
Uleima (not real name) a mother with her premature baby at the special baby care unit. She is practising Kangaroo mother care. She had twins, but lost one of them 3 days after birth.

Every year about 9 million children before the age of 5 die from conditions that can easily be prevented. About 11,000 children are born daily in Nigeria. Nigeria has the highest number of newborn deaths in the whole Africa.

Wani kwararren likitan mata a Asibitin Kwararru da ke Jihar Gombe, Dokta Garba Muhammad Buwa, ya ce bayar da tazarar haihuwa na rage mace-macen mata masu juna biyu.

Dokta Garba, ya bayyana hakan ne a taron kara wa juna sani da wata kungiya mai zaman kanta, Pathfinder, ta shirya wa ’yan jarida da malaman addini domin wayar da kan jama’a kan hanyoyin ba da tazarar haihuwa domin rage yawan mace-macen mata masu juna biyu.

Likitan matan ya ce bayar da tazarar haihuwa na taimakawa wajen rage yawan mace-macen mata masu juna biyu, sai dai idan suna da wata cuta karar kwana.

Abubuwan da za a kiyaye

A cewarsa, idan aka karbi hanyoyin ba da tazarar haihuwa za a rage yawan matan da suke mutuwa a dalilin juna biyun da suke dauke da shi.

Dokta Garba ya kara da cewa idan aka kula da yadda ake ba da tazara a wani lokaci can baya hakan ya sa an samu raguwa sosai na mace-macen.

A cewarsa, ba da tazarar na sa yaran da aka haifa su samun kulawar iyaye fiye da wadanda ake shayarwa a lokacin da ake dauke da wani cikin.

Kwararren likitan ya ce za a iya takaita daukar cikin da ba a shirya masa ba idan aka bi hanyoyin ba da tazara ta yadda mace ba za ta dauki ciki ba har sai lokacin da ta shirya, saboda ta bi tsarin da ya dace.

Sai dai ya bayyana cewa idan ba a bi tsarin da kyau ba yana haifar da zubewar ciki wanda dokar Najeriya ta haramta.

“Zubar da ciki ba bisa ka’ida ba na kawo yawan zubar jini da kamuwa da cututtuka da ma, ciki har da cutar ‘infection’ ba a bi hanyar da ta dace ba kuma ba a wajen kwararru ba” inji Dokta Buwa.

Ya kara da cewa ba da tazarar haihuwa na rage hatsarin daukar cikin da ba a shirya masa ba, sannan ya ba da misali da yin amfani da kwaroron roba wanda ke iya kare mace daga kamuwa da wasu cututtuka.

Sannan ya ce ba da tazarar na matukar taimakawa wajen tattalin arziki da kuma ganin an bai wa yara ilimi mai inganci da samun kulawar iyaye sosai.

Ba da tazarar haihuwa halal ne —Sheikh Dawud

Shi ma wani malamin addinin Musulunci, Shiek Dawud Muhammad Abubakar, daga Jami’ar Tarayya ta Kashere, cewa ya yi ba da tazarar haihuwa a Musulunci abu ne da ya halasta, amma kayyade iyali shi ne laifi a wajen Ubangiji.

A nasa tsokaci Daraktan kungiyar Saif Advocacy Foundation, Alhassan Yaya, cewa ya yi manufar taron shi ne tattaunawa kan hanyoyin fahimtar da juna yadda za a cimma burin kare yawan mace-macen mata a sanadiyyar juna biyu da suke dauke da shi.

Alhasan Yaya, ya yaba wa ’yan jarida da cewa suna taka rawar gani wajen fadakar da al’umma.

Ya ce hanyar da za a bi wajen rage yawan mace-macen na mata masu juna biyu ko a lokacin haihuwa shi ne wayar da kai da kuma matsa wa gwamnati ta yi abunda ya dace dan ganin an yi wa tufkar hanci.

Ya ba da misali da cewa kimanin shekaru biyu da suka gabata mata masu ciki 66 sun taba mutuwa a cikin wata shida a asibiti daya a Gombe, ba ma a maganar sauran asibitocin jihar.

A cewarsa hakan ne yasa suke aiki kafada da kafada da cibiyoyin lafiya a matakin farko domin magance matsalar.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da ta dauki ma’aikatan jinya domin ana samun wadanda suke ritaya amma ba a daukar wasu da za su maye gurbinsu, a bangaren na lafiya da ke fama da karancin ma’aikata da kan haifar da matsaloli masu yawa.