Yadda tifar yashi ta yi taho-mu-gama da jirgin kasa a Kano

Shaidun gani da ido sun alakanta hatsarin da gudun da tifar ke yi.

Yadda tifar yashi ta yi taho-mu-gama da jirgin kasa a Kano

Wurin da hatsarin jirgin ya faru a Kanoa Kano

A Jihar Kano, wani jirgin kasa da ke dauke da fasinjoji da kaya ya yi taho-mu-gama da wata tifar dakon yashi a Kano.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na safe a kan titin Ahmadu Bello da ke unguwar Nassarawa a birnin Kano, lokacin da tifar wacce ke gudun wuce sa’a ta yi karo da jirgin.

Hakan, a cewar ganau, ya tilasta wa jirgin tsayawa, yayin da ita kuma motar ta yi kaca-kaca, direban kuma ya ji rauni a fuska.

Da yake yi wa Aminiya bayanin yadda abin ya faru, wani ganau a wajen, Sama’ila Umar, ya ce ba a sami asarar rai ba, in ban da direban da ya ji rauni da kuma motar da ta yi kaca-kaca.

Ya ce, “Lokacin da jirgin ya taho, ya yi ta yin hon da karfi, da muka ji karar sai muka fito muka tsayar da ababen hawa.

“Wasu sun tsaya, wasu kuma suka ki tsayawa suka tsallaka da sauri. A lokacin shi direban tifar yana zabga gudu, sai ya kasa rike ta, hakan ya sa ta zo ta daki jirgin kafin ya yi fatali da ita a gefen hanya.

“Direban ya ji rauni a fuskarsa, ya rika zubar da jini a hancinsa, amma tifar ta yi kaca-kaca gaskiya,” inji Sama’ila.

Aminiya ta gano cewa hatsarin ya tilasta rufe hanyar na tsawon wasu sa’o’i, yayin da masu ababen hawa suka koma amfani da wasu hanyoyin, kafin jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) su zo su janye taragon jirgin da kuma motar.

Kwamandan Shiyya na FRSC a Jihar Kano, Mato Zubairu, ya tabbatar da faruwar hatsarin, wanda ya alakanta da tukin ganganci da kuma gudun wuce sa’a.

Ya ce, “Lokacin da muka sami rahoton hatsarin, mun tura jami’anmu inda suka tare hanyar sannan muka sa mota ta janye tifar da taragon jirgin daga kan hanya.

“Amma ba a sami asarar rai ba, in banda ta dukiya sakamakon tifar da ta lalace gaba daya, amma direban yana nan kalau, babu abin da ya same shi.

“Abin takaicin shi ne direban yaro ne da bai wuce shekara 20 ba, watakila karancin shekarunsa sun taimaka wajen hatsarin; Yaro mai shekaru irin nasa bai kamata a ce an ba shi tuka irin wannan motar ba,” inji Kwamandan na FRSC.

Daga nan sai ya gargadi iyaye da su guji ba wa yara masu karancin shekaru ababen hawa su tuka.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno