Yadda Tinubu zai gabatar da kasafin 2025
Me kuka fi so kasafin 2025 na Naira tiriliyan 26.1 da Tinubu zai gabatar wa majalisa ya fi ba wa muhimmanci?
A ranar Laraba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kasafin shekarar 2025 a zauren Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Kasafin kuɗin na Naira tiriliyan 26.1 da Tinubu zai gabatar kimanin makonnin biyar kafin karshen shekarar 2024 da muke ciki, na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Nijeriya ke neman sauƙi daga tsadar rayuwa da durƙushewar harkokin tattalin arziƙi.
Daraktan Bincike da Yada Labarai na Majalisar, Ali Barde Umoru, ya ce za a gabatar da kasafin ne a taron haɗin gwiwar Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa. Tun kafin wannan zama Tinubu ya riga ya aike wa zaurukan majalisar dokokin ƙasar daftarin kasafin kuɗi.
Kasafin kudi na biyu ke nan da Tinubu zai gabatar, a daidai lokacin da matsalar tsadar rayuwa da ta tattalin arziki, da rashin tsaro ke ci gaba da addabar ƙasar, sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi.
Bayan gabatarwar da Tunubu zai yi, kwamitocin majalisar za su yi aikin tantance tare da sauraron bayanai da kasafin hukumomi da ma’aikatun gwamnati.
Bata nata gyare-gyaren, daga ƙarshe majalisar za ta aike wa fadar shugaban ƙasa domin shigar da gyare-gyare, idan a akwai, inda daga ƙarshe zai sa hannu kasafin ya zama doka.