Yadda Trump ya sallami Sakataren Harkokin wajen Amurka kwana daya bayan ya ziyarci Najeriya

Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami Sakataren Harkokin Wajen Amurka Red Tillerson daga mukaminsa kwana daya bayan ya ziyarci Najeriya sannan ya maye gurbinsa da Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA) Mike Pompeo. Shugaba Trump ya sanar da sallamar Tillerson ne a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana godiyarsa gare shi bisa yadda ya […]

Yadda Trump ya sallami Sakataren Harkokin wajen Amurka kwana daya bayan ya ziyarci Najeriya

Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami Sakataren Harkokin Wajen Amurka Red Tillerson daga mukaminsa kwana daya bayan ya ziyarci Najeriya sannan ya maye gurbinsa da Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA) Mike Pompeo.

Shugaba Trump ya sanar da sallamar Tillerson ne a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana godiyarsa gare shi bisa yadda ya yi kasar Amurka hidima. Sannan ya ce yana da yakinin sabon Sakataren Wajen Amurkan da ya nada Mista Pompeo  zai yi aiki mai kyau.

A wani bangaren kuma, Donald Trump ya  amince da nada Gina Haspel a matsayin Daraktar Hukumar  CIA, wanda hakan ya sa ta zama mace ta farko da ta rike wannan mukami.

Idan ba manta ba, Tillerson ya kawo ziyarar aiki  Najeriya ce a ranar Litinin da ta gabata, sannan ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda har ya nanata kudurinsu na taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta’addanci, sannan ya bukaci a yi duk mai yiwuwa wajen ceto ’yan matan makarantar Dapchi da ake zargin Boko Haram ta sace su.