Yadda tsadar man fetur ta ƙara jefa rayuwar ’yan Nijeriya cikin ƙunci
Farashin kaya sun yi tashin gwauron zabo mafi girma a cikin shekara 8.
Direbobi da ke safarar fasinjoji a cikin birane da kuma masu zuwa garuruwa na sahun gaba wajen fuskantar matsalar karin kudin mai da ’yan Nijeriya suka wayi gari da fuskanta a ranar Talata ta makon jiya.
Farashin wanda a hukumance ya tashi daga Naira 568 a gidajen man Kamfanin NNPCL da ke birnin Lagos da kuma Naira 617 a na yankin Birnin Tarayya Abuja, inda ya koma zuwa Naira 855 a birnin na Ikko, sannan Naira 897 a Abuja.
- Zaɓen Edo: Za mu kare ƙuri’unmu da jininmu — PDP
- Kotu ta hana Aminu Bayero yi wa Fadar Nassarawa kwaskwarima
Sai kuma karin mabambantan farashin kudi a sauran daidaikun gidajen mai da ke biranen biyu da kuma wasu jihohi da farashin ke kaiwa har zuwa Naira dubu 1 da 300, gwargwadon yankin da kuma wanda ke sayar da man a bangaren masu gidajen man.
Direbobi da dama da Aminiya ta zanta da su sun ce, lamarin ya mai da sana’arsu ba riba, kasancewar yadda jama’a ke bijere wa karin kudi da suka yi, ga kuma yawaitar masu sana’ar a kan titi ciki har da masu motoci da ba na haya ba da su ma suka koma daukar fasinja, don rage radadin tsadar man.
A yayin da wasu masu motoci da dama suka gwammace barin motocinsu a gida, inda suke shiga na haya a yayin zuwa wurin aiki ko kasuwa ko sana’a ko balaguro, wanda direbobin suka yi korafin cewa, a bangarensu ba su da zaɓi da ya wuce su bi hanyar a haka.
Wani direba mai suna Ibrahim Aiyo da ke bin hanyar Abuja zuwa Kano daga tashar mota ta garin Zuba Abuja ya ce, dan karin da suka yi ya sa fasinjoji sun ja da baya, inda sukejimawa a tasha kafin su samu lodi.
Ibrahim ya ce, ‘‘yanzu kwanana huɗu da zuwa Abuja, amma sai yau na samu lodi kuma ka ga dai a yanzu dai misalin karfe 11 na rana, ni ne na yi lodi na biyu a tashar nan.’’
Binciken Aminiya ya gano cewa, farashin kudin mota daga tashar ta Zuba zuwa Kano da a baya ake biyan Naira dubu 8, a yanzu ya koma Naira dubu 11.
Binciken ya kuma gano cewa, lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kayayyaki na amfanin yau da kullum su ma farashinsu ya kara tashi a sakamakon yankewarsu a lokacin zangazanga, wanda a baya suka fara saukowa, sai dai akwai yiwuwar za su kara tashi a dalilin karin kudin man da aka yi.
Wata ’yar kasuwa a garin Kubwan Abuja da ke sayar da kayan masarufi mai suna Madam Stella Asiegbu ta ce, tuni suka fara fuskantar karancin wasu kayayyaki da suke saya, inda ta yi zargin an boye kayan ne da nufin jiran farashinsu ya karu a dalilin karin kudin sufuri da a ka samu.
Madam Stella ta ce, a duk lokacin da aka samu karin kudin mai, wasu ’yan kasuwa na yin irin hakan, lamarin da ta ce na haddasa tashin farashin kaya a dalilin karancinsu a kasuwa.
A Jihar Kano al’umma kamar sauran ’yan Nijeriya na ci gaba da kokawa game da karin farashin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi a makon jiya.
Kanawan na cewa lamarin ya ƙara jefa rayuwar mutane a cikin ƙuncin da bakin talauncin da ake fama da shi, don haka suka nemi mahukunta da su sake duba wannan lamari tare da daukar matakin rage farashin man cikin gaggawa.
Malam Ado Iliyasu ma’aikaci ne a Jihar Kano ya ce, bai ji dadin karin kudin man ba, inda ya ce, ‘‘abu ne da ba zai haifar da da mai ido ba. Abu ne da bai yi wa kowa dadi ba.
“Wannan fa yana nufin an kara jefa rayuwar talaka a cikin kunci.
“Sanin kowa ne cewa a duk lokacin da aka kara kudin man fetur, kai-tsaye farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi zai karu, a yanzu ma ka duba yadda mutane ke fama da wahala.
“Mutane suna mutuwa da yunwa ba sa iya cin abinci sau uku a rana. Wanda yake cikin wannan wahalar an kuma kara masa wata. Yaya kike gani?”
Malam Iliyasu ya kuma kara da cewa, a yanzu haka ma’aikata ba za su iya zuwa wurin aikinsu a kullum duba da tsadar kudin mota.
“A yanzu ina tabbatar miki da cewa, ma’aikata da yawa ba za su rika zuwa aiki a kullum kamar da ba.
“Misali, ni da nake zaune a Bachirawa ina zuwa aiki Sakatariyar Audu Bako, a da ina kashe Naira 700 ko 800 a kullum, amma a yanzu zan rika kashe Naira dubu daya, kin ga kuwa dole na rage zuwa ofis domin albashin ba zai isa na yi hakan ba,’’in ji shi.
Sai ya yi kira ga gwamnati da ta rage farashin man domin saukaka rayuwa ga talakawan kasar nan.
Ita ma wata malamar makaranta da ke koyarwa a Karamar Hukumar Rimin Gado ta bayyana cewa, tana cikin fargaba duba da cewa an yi karin farashin man ne a daidai lokacin da dalibai ke komawa makaranta bayan dogon hutun da suka yi.
‘‘Babbar fargabana shi ne yadda zan rika zuwa wurin aiki a wannan lokaci da aka yi karin kudin man fetur, wanda idan ba a yi sa’a ba zai zama mai mota kawai nake yi wa aikin,’’in ji ta.
Ma’aikatan Jihar sun nemi Gwamnatin Jihar Kano da ta rage musu lokacin zuwa aiki domin su sami saukin rayuwa.
Haka abin yake a bangaren ’yan kasuwa, inda wani mai sayar da labule a Kasuwar Sabon Gari mai suna Malam Nafi’u Khalid Gezawa ya bayyana takaicinsa game da wannan karin kudin man fetur da aka yi, inda ya ce idan har ba a yi da gaske ba lamarin zai haifar da karuwar masu aikata laifuka a tsakanin matasa.
‘‘Gaskiya ban ji dadin wannan karin da aka yi ba, yanzu yaran shagona dan kudin da nake sallamar su a kudin mota yake karewa domin a cikinsu akwai masu zuwa daga Minjibir da wasu unguwanni masu nisa a cikin garin Kano.
“Kudin ba ya isa su ci abinci ballantana su dan ajiye wani abu.
“Ni da kaina idan aka yi ciniki na dauki kudin na yi hidimar gida sai ki ga babu komai, to wannan ma fa ga ni kaina ke nan, ina ga yarana da suke jiran sai abin da na kawo na ba su’’, in ji ta.
Sai ta yi kira ga Shugaban Kasa Ahmed Bola Tinubu da ya duba halin da talakawa ke ciki a wannan kasa.
‘‘Babu wanda yake jin dadin wannan karin kudin da aka yi idan ba shugabanni ba.
“Ana cewa ana yakar ta’addanci, to wannan tsadar rayuwar da aka shiga maimakon a sami raguwar ta’addanci to sai dai ya karu, wanda ya zama ba shi da wata hanyar samun kudi to zai iya sa kansa a cikin kowane irin hali.
“Don haka ina kara yin kira ga shugabanni da su sake duba wannan lamari da idon basira tare da janye karin da aka yi don jama’a su sami saukin rayuwa’’.
Masu sana’ar tuka Keken Napep sun ce lamarin karin farashin man ya shafe su kai-tsaye, ya kuma jefa rayuwarsu cikin halin ni-’yasu domin wasu daga cikinsu ba za su iya ci gaba da gudanar da sana’ar ba a irin wannan yanayi da ake ciki.
Wani mai sana’ar tuka keken NAPEP mai suna Malam Ibrahim Haruna ya bayyana karin kidin man fetur din a matsayin lamarin da ya fara haifar da rikici tsakaninsu da fasinjoji.
‘‘Sanin kowa ne aikinmu ya ta’allaka kacokan a kan man fetur, ga shi kuma ya yi tashin gwauron zabo.
“Dole a yadda na sayi man fetur a haka zan nemi fasinja ya biya kudinsa, to a nan rigimar take domin shi fasinja ba zai so karin da za mu yi masa ba.
“A yanzu ma kina gani a kullum fada muke da su ballantana a yanzu da aka yi wannan karin,’’in ji shi.
Ya ce, “da yawa wasu da dama daga cikin fasinjojin da za ka dauka sai kun tsaya kuna kai-ruwa-rana, don babu issashen kudin da za su biya ka, wani kuma ta dole ne sai ka taimaka kawai domin ba za su iya biyan mutum hakkinsa daidai ba.
“Wasu da yawa ma kyauta ake daukar su, saboda kai kana ganin mutun ka san ba shi da shi.
“Idan muka ga irin wannan muna daga musu kafa, mu kai su kyauta ko mu yi hakuri mu karbi dan abin da ke hannunsu.
Shi ma dai ya yi kira ga gwamnati da ta dube su, ta yi abin da ya dace.
Ya ce, ‘‘a lokuta da dama kudin da za ka kai wa mai keken ba ya haduwa.
“Hakan ma masu kekunan suna tausayawa, suna karbar abin da ya samu. Sai dai mu yi musu addu’ar Allah Ya kawo mana sauki’’
Malam Salisu Adamu shi ma mai sana’ar Keken NAPEP ne da ya bayyana cewa, idan har gwamnati ba ta rage kudin mai ba, shi dai ya yi bankwana da tuka mashin domin ire-iren matsalolin da yake ciki.
‘‘Ai abin ba zai yiyu ba. Na sha man Naira dubu biyar sai da kyar za ka iya samu ka hada Naira dubu shida, to me mutum zai ci, me kuma zai kai wa mai keken?
“Abin da yake faruwa yanzu shi ne, fasinjoji ba sa iya biyan kudin da ya kamata su biya.
“Idan ka gaya wa fasinja kudin da zai biya sai ya nemi ragi, a karshe dai dole ce ke sanyawa ka dauke shi a haka domin idan ba ka dauke shi ba ma, sai dai ka tafi, ka yi ta kona man a banza.
“Domin idan ka yi gaba ma haka abin yake, ta yaya mutum zai ci gaba da yin aiki a haka?”
Wasu fasinjoji da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana rashin jin dadinsu game da karin kudin man fetur din, inda suka yi kira ga gwamnati da ta rage kudin don tausaya wa rayuwar talaka.
Wani fasinja mai suna Malam Adamu Abubakar ya bayyana cewa, ‘‘a da yana biyan Naira 350 daga Kabuga zuwa Gidan Zoo, amma yanzu ya koma Naira 500 idan zan koma gida ma haka, to kin ga akwai damuwa sosai’’.
Ita ma wata fasinja cikin fushi ta zargi shugabannin kasar nan da kokarin ganin bayan talakawa inda ta ce, ‘‘ni sai yanzu na fahimci shugabannin Nijeriya so suke su ga bayan talakawa domin a kullum suna fito da abubuwan da ke kara jefa rayuwar talaka cikin kunci.
“Shi fa karin kudin man nan da aka yi kamar ana kukan targade ne sai ga karaya ta zo.
“Sanin kowa ne ana kukan tashin farashin kayayyaki a yanzu kuma ga an kara kudin man, su ma ’yan kasuwa har sun kara farashin kayayyakinsu.
“Ina sayen sabulun wanki Naira 100 a yanzu ya koma Naira 150. Ga masu Keken Napep duk sun kara. Allah dai ya yi mana maganin wannan musiba,’’in ji ta.
Sai dai Aminiya ta lura da yadda mutane a Jihar Kano suka rungumi tafiyar kasa saboda tsadar kudin mota.
Wasu da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana cewa, sukan rage tsawon tafiya da za su yi ta hanyar tafiya a kasa.
A Jihar Kaduna ma haka lamarin yake, inda jama’a ke kokawa a kan karin kudin man.
Imam Hussaini Udawa Malamin Addinin Musulumci ne a Karamar Hukumar Chikun, wanda bayyana cewa, al’umma na cikin matsanancin yanayi a sakamakon karin kudin man da Gwamnatin Tarayya ta yi.
Ya kuma nemi jama’a da su ci gaba da yin addu’a domin neman sauki a wurin Allah.
Imam ya kara da cewa, hakika jama’a na cikin wahala domin yanzu wasu bata-gari sun koma suna sace-sace, kai hatta tukwannen mata a cikin gida shiga ake ana kwashewa, a je a sayar.
Ya ce shi kansa an shiga gidansa an kwashe murafen tukwanen matansa gaba daya.
Sannan kuma ya ce, ga ’yan uwa a kullum suna da bukata a wurinka, inda fiye da mutum 30 suke zuwa rokon abinci, wasu kuma kudi.
“Bala’i ne ya riga ya fadawa kasa. Gwamnati ce ke da hanyar janye wannan bala’in.
“Saboda haka gwamnati ta ji tsoron Allah ta dawo da tallafin man fetur kamar yadda yake a can baya, wanda haka shi ne kawai abin da zai kawo sauki da zama lafiya a kasa.
A cewarsa, idan gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba, abin da zai faru a nan gaba zai fi wanda ya faru a baya.
Shi ma tsohon Kansilan Unguwar Sarki, Malam Zubairu Shan’una ya bayyana alhininsa dangane da irin tsadar rayuwa da al’umma ke cikin a sakamakon karin kudin man fetur.
“Al’umma na cikin tsanani da har takai a yanzu ba sa ma iya bayyana halin da suke ciki.
“Sai dai duk wanda ka kalla ka san yana cikin damuwa. Kuma mafi akasarin masu motocin haya duk sun ajiye saboda tsadar man, kuma idan ka sayi man ba dole ne, ka mayar da kudinsa ba, ballantana ka samu riba.”
A cewarsa, “a yanzu kaso 40 sun gwammace su shiga motar haya, su je inda za su, in ba ya kama za su fita da iyalinsu ba ne, shi ne za ka gan su a motarsu, duk abin da ake yi ke nan fa a yanzu, komai ya kara tsada har da kayan abinci, ga kuma abinci Allah Ya hore mana a kasa, amma saboda tsadar kudin sufuri abin ya gagara a shigo da shi kasuwa,’’ inji Zubairu.
Malam Shan’una ya kara da cewa, a yanzu dai ta tabbata cewa, gwamnati ba ta tausayin talakawa don haka sai ya roki Allah da Ya tausaya wa talakawan Nijeriya domin a samu saukin wannan matsanancin hali da ake ciki.
Malam Adamu Hassan Mazaunin Zariya ne da ke aiki a Kaduna ya ce, su dai talakawa a kullum wahala suke sha.
“Abin ya kure domin kuwa man fetur din nan fa muna da shi,ba wai ba mu da shi ba ne a kasar nan, sannan gamu da matatun man, maimakon a gyara su, a samar da man ga al’umma cikin sauki, amma an ki sai a kai waje a dawo mana da shi a sayar da tsada.
“Al’amarin nan fa na shugabanin Nijariya babu Allah a zuciyarsu sannan kuma kowa ya sani.
“Saboda haka mu dai muna cikin wani yanayi. Yanzu fa rayuwa ta canza domin kuwa abin da kake saya a shekarun baya a kan Naira 700 yanzu ya koma Naira dubu 3.
“Sannan kuma su ma ’yan kasuwa su kara kudin kaya domin da tsadar suka sayo.
“Kuma man fetur babu sauki, idan da ana samu man fetur da sauki dole ne komai ya sauka,’’in ji shi.
A cewarsa, a shekarun baya kafin zuwan Gwamnatin Buhari, Naira 400 ne kudin mota daga Zariya zuwa Kaduna, amma a yanzu sai ka biya Naira dubu biyu.
Malam Adamu ya kara da cewa, a yanzu ba ta kansa ya ke yi ba, sai ta ’ya’yansa domin babba na iya hakuri, amma yaro bai san da haka ba dole a nemo a bai wa yara.
Ya haifar da rudani a tattalin arzikin kasa — Masani
Wani masanin tattalin arzikin kasa, Malam Yusha’u Aliyu ya ce, karin kudin man da gwamnatin ta yi, ya haifar da rudani a tattalin arzikin kasa.
Ya ce, bayanan da Ma’aikatar Kula da Albakatun Mai da kuma wanda Kamfanin NNPCL suka fitar bayan ganawarsu da mataimakin Shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima na cewa, yanayin kasuwa ce ta haifar da karin kudin ba hannun gwamnati a ciki akwai rudarwa a cikinsa.
Ya ce, babbar illar da karin ya yi ita ce na dakushe fatan al’umma kan saukowar farashin kayan abinci da aka noma a dalilin shigowar kaka, inda ya ce a dalilin karin abu ne mawuyaci farashin amfanin gona ya yi kasa kan yadda ake saya a yanzu.
Ya ce, lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da Babban Bankin Kasa yake ikirarin cewa, wasu matakai da ya dauka ya sa farashin kaya sun yi kasa a karo na farko cikin ’yan watanni.
Ya ce, dan saukin da a ka samu a bangaren saukar farashin kayayyaki, a yanzu dole ya kara tashi idan ma har akwai.
Malam Yusha’u Aliyu ya ce babbar matsalar da ke damun tattalin arzikin Nijeriya ita ce hauhawar farashin kayayyaki da ke da nasaba da karancin aikin yi.
Idan ya zamana kayan da masana’antu suke sarrafawa sun ci gaba da hauhawa, dole ne al’umma su takaita sayan kayan, to rashin sayan zai sa dole masana’antun su rage yawan ma’aikata, wasunsu kuma su rufe gaba daya.
Wadannnan alkaluman na da nasaba da ci-gaban tattalin arzikin kasa ko akasin hakan, kuma bisa ga dukkan alamu an shiga wannan mataki.
Haka lamarin yake idan aka koma bangaren sufuri, inda masu motocin haya ke kukan cewa, suna aikin ne kawai ba tare da samun riba ba.
Masanin ya ce, farashin kaya sun yi tashin gwauron zabo tun gabanin karin albashi da kashi 34 cikin 100 da ke a matsayin mafi girma a cikin shekara 8.
“sai kuma ga shi gwamnatin ta kara kudin mai, duk da cewa ta yi karin albashi a dalilin karin kudin man fetur na baya da ta yi, to amma ga shi karin albashin ko fara karba ma’aikatan ba su yi ba, an sake kara kudin man, wannan shi ne an ba ka da dama an karbe da hagu.”
Ya ce, kasar nan na fuskantar gagarumar matsalar karancin abinci a dalilin matsalar tsaro da ’yan ta’adda suka haifar, musamman a yankunan da aka fi noma abincin a lokacin da adadin al’ummarsu ke karuwa, sai kuma ga annobar ambaliyan ruwa a wuraren da aka yi noman ruwa ya shafe shi.
Ya ce, wata karin matsalar ita ce tsadar kayan noma kamar taki da maganin feshi da yake shafar harkar noman.
Ya ce, a fadin kadada miliyan 90 da al’ummar Nijeriya za su iya nomawa, ya ce ba a iya noma ko da kaso 5 a ciki 100 na filin noma tun a can baya, ballantana kuma a yanzu da ake fuskantanr matsalar tsaro da kuma rashin kudin aikin.
Masanin ya kara da cewa, akwai takaici ganin yadda ’yan ta’adda suka bayyana a kafar sada zumunta, suna barazana ga manoma cewa wanda suka noman ma za su lalata shi.
Ya gargadi gwamnati da ta mai da hankali wajen samar da aikin yi a maimakon nakasa shi ko da kuwa nawa za ta kashe a kai, inda ya ce idan ba a yi taka-tsantsan ba zangazangar da aka yi a baya game da tsadar rayuwa a kan iya fuskantar fiye da hakan a nan gaba.
‘‘Wadda kuwa zai ta iya kaiwa ga durkusar da tattalin arzikin kasar gaba daya da ma ita gwamnatin kanta,’’ inji shi.