Yadda tsadar man gyada ta jawo hauhawar farashin Awara a Kano
Yanzu haka wasu masu sayar da awara a Kano sun fara sayar da uku kan N50.
A wasu sassa na jihar Kano, bincike ya gano yadda tashin gwauron zabin da farashin man gyada ya yi ya jawo karin farashin Awara a Kano.
Masu sayen awarar dai sun koka matuka kan yadda masu sayar da ita suka kara farashinta.
- COVID-19: Majalisar dokokin Kano ta jingine dawowa zamanta
- Batanci ga Annabi: Kotu ta warware hukuncin kisa da aka yanke wa Matashi a Kano
- An kama mota dauke da tabar wiwin N30m an Kano
- Shaye-Shaye: Hisbah ta kama ‘yan mata 19 a birnin Kano
Sai dai daga nasu bangaren, masu sayar da awarar sun bayyana dalilinsu na yin hakan, inda suka ce farashin mai ne ya karu, shi yasa su ma suka kara nasu farashin.
A wasu yankunan na Kano, tuni suka fara sayar da awarar guda uku kam farashin N50, wasu kuma suka barta a farashin da ta ke, amma suka rage hannu.
Yayin tattaunawarmu da wani mazaunin Kano, Yahaya Sa’id ya ce ya damu matuka kan yadda masu sayar da awarar suka rage hannu.
“Ban ji dadin yadda masu awara suka rage girmanta a ‘yan kwanakin nan ba.
“A unguwarmu ba su kara farashin nata ba, amma sun rage mata girma,” cewar Sa’id.
Me yasa farashin ya tashi?
Bincike ya nuna cewa tashin farashin na da laka da tashin farashin man gyada da na waken suya wadanda sune ginshikai wajen yin awarar.
A baya, ana sayar da kwalbar man gyada a farashin N400 zuwa N450, amma yanzu ta koma N500.
Mukhtar Hayaya Sani, mai sana’ar sayar da man gyada, ya ce a baya ana sayar da jarkar man gyada kan N12,500, amma yanzu ta koma N18,000.
Sani ya ce “Karuwar farashin man gyada tabbas zai shafi abubuwa da dama.
“Amma bana tunanin hakan zai sa lamarin ya ta’azzara, duba da yadda kusan komai ya yi tsada a yanzu.
“Kullum sai ka ji karin kudi a kan wasu abubuwan, kuma har yanzu ba mu san dalilin karin ba,” in ji Sani.
Wuraren sayar da awara
Da dama daga cikin masu sana’ar awara a wasu yankuna, na Kano sun dakata da sana’ar har zuwa wani lokaci.
Aisha Ali, wata mai sayar da awara, ta ce “Da dama daga cikin masu sayar da awara sun koma sayar da dankali, shi yasa nima na sauya akala.”
Ta kara da cewa yanayin yasa ba ta jin dadi, amma tana fatan samun sauki na saukar farashin kayan.
Wani mai sayen awara, Auwalu Mohammed, ya shaida mana cewa tuni yarinyar da suke sayen awara a wajenta ta daina saboda ba za ta juri yin asara a dalilin karin kudin man gyada ba.
Rukayya Muhammad, wata mai sayar da awara, ta shaida mana cewa tuni suka fito da tsarin sayar da awara uku kan farashin N50.
“Kowa yasan yadda waken suya da man gyada suka kara kudi.
“Shi yasa muka koma sayar da guda uku kan N50.
“Tabbas mun damu, saboda hakan ya shafi kasuwancinmu, amma muna fatan komai ya daidaita,” cewar Rukayya.