Yadda tsagerun Bakassi suka jawo halakar dan Arewa

Mutum uku suka  rasa  ransu ranar Liitinin  sakamakon wani kwanton bauna da tsagerun yankin Neja-Delta suka yi wa wasu mutum biyu  da suka tuba suka bar kungiyar suke zaton su ne suka bai wa jami’an tsaro sirrin su, har aka kawo musu hari, inda a kalla mutum  40 cikin tsagerun aka kashe. Mutumin na uku  […]

Yadda tsagerun Bakassi suka jawo halakar dan Arewa

Mutum uku suka  rasa  ransu ranar Liitinin  sakamakon wani kwanton bauna da tsagerun yankin Neja-Delta suka yi wa wasu mutum biyu  da suka tuba suka bar kungiyar suke zaton su ne suka bai wa jami’an tsaro sirrin su, har aka kawo musu hari, inda a kalla mutum  40 cikin tsagerun aka kashe. Mutumin na uku  da ya rasa ransa ciki har da wani dan asalin Jihar Zamfara ne mai suna Murtala Isma’il da tsagerun suka yi wa kwanton bauna suka kashe su.

Malam Yakubu Ibrahim yayan mahaifin murtala Isma’il  da ya  rasa ransa ya yi wa Aminiya karin bayanin yadda dan nasa ya hadu da ajalinsa.

“To ni dai kamar yadda ka tambaya  dan kanena ne yana sana’ar saye da sayar da karfe ne a Bakassi, shi ne sai mutum biyu ’yan asalin Bakassin suka zo suka kirawo shi ya zo ya sayi karfe, to ashe wadanda suka kirawo shi tubabbun tsagerun Bakassin ne; ashe sauran abokan su da ba su tuba ba suna neman su ruwa a jallo za su kashe su saboda suna zargin  su ne suka gaya wa sojoji suka kai musu farmaki har aka kashe musu mutum kusan 40. To shi Murtala yana biye da su suna cikin tafiya ba tare da sun sani ba, sai kurum suka ji an bude musu wuta ana ta harbin su.

Ka san tun da an gansu tare ba za su iya sanin ko shi yaron ba dan kungiyar su ba ne ko ba ya daga cikin wadanda ake zargi suka kashe su,”inji Malamin.

Da aka tambaye shi ko sun ga gawar Murtalan sun samu daukota, domin yi mata sutura, Malam Ibrahim ya ce: “Mun je da sojoji wurin da abin ya faru ba mu ga gawar ba, amma mun iske sun zuba bakin mai a wurin don kada a ga jinin su, harsashi kadai muka gani a kasa an kewaya da mu ko’ina ba mu ga gawarsa ba, ko inda suka yar da ita, amma muna zato ko sun jefa gawar cikin ruwa ne haka dai muka dawo,” inji shi.

Malam Yakubu Ibrahim ya tabbatar wa wakilinmu cewa sun sanar da hukumar ’yan sanda lamarin kana kuma wakilinmu ya tuntubi Irene Ugbo, kakakin rundunar ’yan sandan Kuros Riba ta ce sun samu labari, kuma suna bincike da zarar sun samu ganin gawarwakin ko kama wadanda ake zato suka aikata haka za su kama su a bincike su.