Yadda tsanani da yawan aiki ke halaka ma’aikata a Japan – Rahoto

Babbal kamfanin tallat hajana kasar Japan kotu ta cci shi tarar Dala 3,784 wato daidai da Naira miliyan 1,362,240 sakamakon mutuwar ma’aikacinsa da yawan aiki ya halaka. Matsuri Takahashi mai shekara 24 ta mutu ne a wajen aikinta da ke birnin Tokyo ranar Kirsimetin ssheklarar 2015, al’amarin da dokar aiki da masu sa’ido suka tabbatar […]

Yadda tsanani da yawan aiki ke halaka ma’aikata a Japan – Rahoto

Babbal kamfanin tallat hajana kasar Japan kotu ta cci shi tarar Dala 3,784 wato daidai da Naira miliyan 1,362,240 sakamakon mutuwar ma’aikacinsa da yawan aiki ya halaka.

Matsuri Takahashi mai shekara 24 ta mutu ne a wajen aikinta da ke birnin Tokyo ranar Kirsimetin ssheklarar 2015, al’amarin da dokar aiki da masu sa’ido suka tabbatar da sanadiyyar yawan aiki ne ya halaka ta.

“Na yamutse na shiga damuwa,” kamar yadda wannnan amta ta rubuta a shafinta na zumunta a intanet makonni kadan kafin ta halaka kanta, cewa “ina son in mutu.”

Yadda aka yankee hukuncin shi ne, tsakanin Oktoba da disambar 2015, kamfanin Dentsu Inc ya tursasa wa Takahashi da wasu ma’aiaktansa uku yin aiki a tsakanin sa’o’i uku zuwa 19 da minti 23, al’amarin da ya wuce karin lokacin aiki da aka kayyade na sa’o’i 50 a wata, wanda dokoki da yarjejeniyar kwadago ta amince da su, kamar yadda jaridar Kyodo ta ruwaito.

Takashi ta mutu ne bayan ta kama aiki da Dentsu na wasu ’yan watanni, al’marin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a fadin kasar kan yadda ake tsanantawa da mummunan yanayi wajen aiki da ake fama da shi a kasar Japan.

Ma’aikatar Lafiya da ta kwadago a kasar Japan sun ce a wata makalar da suka gabatar cewa akwai mace-mace har 191 da tsananin aiki ya haifar da su, kamar yadda ytake kunshee a wani rhaoton shekara dda aka tattara zuwa karshen Maris din 2017, al’amarin da aka ce ya dan karu a kan alkaluman shekarar da ta gabata, wadanda kimarsu ta tsaya a 189.

Kuma rahoton ya yi nuni d aceewa, kasha 7.7 cikin 100 na yin karin lokacin aiki na fiye da sa’o’i 20 a mako.