Yadda tsananin zafi ya sa Alhazai Sallah a kofar banɗaki
Ko ba komai wannan zafin ranar bai kai na ranar Lahira ba.
A Juma’ar jiya ce aka samu zafin rana mafi tsanani a birnin Makkah a kakar aikin hajjin bana, lamarin da ya sa wasu alhazai yin sallar a zauren shiga bandakin Masallacin Harami.
Tun da farko hukumomin Saudiyya sun sanar cewa zafin rana zai kai maki 50 na ma’aunin Celsius, wanda ya haura na ranar Arfa da maki biyu.
- Ejikeme Mmesoma: Dalibar da ta kara wa kanta maki a sakamakon JAMB ta magantu
- Tinubu zai halarci taron ECOWAS a Guinea-Bissau
Bisa haka ne hukumar yanayi ta kasar ta shawarci alhazai da su yi sallar Juma’a a masallatai mafi kusa da su domin kauce wa shiga tsananin ranar, ba sai sun je Masallacin Harami ba.
Yadda Alhazai suka yi sammako
Tun kafin fitar alfijir gari wasu alhazai suka yi fitar dango zuwa masallacin, inda wasunsu tun daga Sallar Asuba ba su koma gida ba, sai bayan Juma’a.
Wasu kuma da hantsi suka kama hanyar zuwa masallacin, wanda zuwa karfe 11 na safe, alhazai da saura jama’a sun cika daukacin gininsa, har da wasu sassan da ba a riga an kaddamar ba a sabon bangaren masallacin da ake aikin fadadawa na uku.
Aminiya ta ga yadda wasu suka sare a hanyarsu kafin su isa Masallacin Harami, inda suka kare da shiga masallatan cikin unguwa.
Wasunsu kuma ba su da zabi face fakewa a inuwar karkashin gadoji, wasu kuma a inuwar gine-ginen da ke kusa da masallacin.
Akwai kuma wadanda suka rakube a tsakanin jama’a da ke cikin sahu, a zauruka da barandar masallacin; bayan an kabbarta sallar wasu suka samu inuwar, wasu kuma suka yi sallar a cikin ranar mai tsananin zafi.
‘Saura kiris na fasa sallar’
Wani Alhaji daga Najeriya ya shaida wa Aminiya cewa “Gaskiya da ba mu samu inuwa ba, to da sai da mu koma gida.”
Su kuma wasu alhazai cewa suka yi, duk zafin ranar za su yi sallar ko da a cikin ranar ce, “tunda ibada ce ta kawo mu nan kasar, kuma wannan zafin ranar bai kai na ranar Lahira ba.”
Yadda muka yi sallah a kofar banɗakin Masallacin Harami
Aminiya ta gamu da wani Alhaji daga Jihar Kano, Nasir Nasir, wanda ya shaida mata cewa a farfajiyar shiga banɗakin masallacin ya yi sallar Juma’ar.
“Mun yi sa’a mun samu inuwa a kusa da banɗaki, ba don haka ba, karshenta da mu ma a rana za su yi sallar.”
Alhaji Musa daga Jihar Jigawa, ya ce, “wajen karfe 10 na safe muka fito masallaci, amma muna isa wani otel da muke yanke ta cikinsa mu bullo a masallaci, suka rufe kofa kafin mu shiga, dole muka zagaya.
“Da isarmu haraba, muka lura an riga an cika ciki, duk inda muka hangi inuwa kuma, kafin mu isa jama’a sun cika ta ko an tare hanya.
“Dole muka shiga banɗakin da ke karkashin kasa mu fake kafin a fara sallah, a nan ne muka yi sa’a muka samu wuri har muka yi sallah.”
Rige-rigen samun wuri a kofar banɗakin masallaci
Sagir Yusuf daga Jihar Kano ya ce, “Mun fi mutum 100 daga kasashe daban-daban wadanda muka yi Sallar Juma’a a harabar shiga banɗakin masallacin.
“Tun a hanyar shiga muka samu wasu sun riga mu, suna zazzaune a zauren da ke hada ɓangaren banɗakuna da na zuwa wurin ajiye motoci.
“Sai muka wuce gaba muka je ta daya bangaren da ke gaban bandakin kusa da matakalar da aka ware wa nakasassu.
“Muna zaune a wurin aka yi kiran sallar farko, kafin kira na biyu ma’aikata suka zo wanke wurin, amma shugabansu ya ce su bari, tunda jama’a sun fake wa tsananin zafin rana.”
“Akwai wadanda muna wurin suka fita da tunanin an bude wata kofar shiga cikin masallaci, karshenta suka yi biyu-babu.
“Wasu mutanen a matakalar shiga banɗakin suka fake, bayan an tayar da Sallah suka shigo sahu, saboda an samu sarari.”
Bayan sallar, wani Alhaji daga Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Idrissa, ya ce, “Gaskiya Nijar ana zafin rana, amma bai kai na nan garin ba.”
Shi kuma wani dan Najeriya cewa ya yi, bayan idar da sallar, mun shiga daya da cikin manyan shagunan da ke zagaye da masallacin muka sha sanyin AC, kafin daga bisani muka kama hanyar komawa masauki.
Duk da wannan tsananin zafin rana, alhazai da ’yan kasuwa sun ci gaba da gudanar da hada-hadarsu bayan sallar Juma’ar a yayin da daidaikun jama’a da kuma jami’ai suke ta rabon ruwan sanyi kyauta ga jama’a a kan tituna.