Yadda tsarin dandalin Facebook yake (1)

Mabudin KunnuwaA yau, cikin yardar Allah, za mu fara kawo bayanai kan yadda tsarin Facebook ke aiki a kimiyyance. A baya mun yi ta bayanai ne kan dandalin a jimlace; asali da samuwa, da yadda ake rajista, da yawan jama’a masu rajista, da wadanda suka samar da dandalin da kuma sauran al’amura. Amma a wannan […]

Yadda tsarin dandalin Facebook yake (1)

Mabudin Kunnuwa
A yau, cikin yardar Allah, za mu fara kawo bayanai kan yadda tsarin Facebook ke aiki a kimiyyance. A baya mun yi ta bayanai ne kan dandalin a jimlace; asali da samuwa, da yadda ake rajista, da yawan jama’a masu rajista, da wadanda suka samar da dandalin da kuma sauran al’amura. Amma a wannan fili, in Allah Ya so, bayanai ne kan yadda aka gina shafin, da yadda aka tsara shafukan, da tsarin manhajoji ko masarrafan da ke cikin wannan dandali da sauran abubuwan da suka sawwaka.  Saboda ganin mu yi ta kawo bayanai kan asali da samuwar wannan dandali, a yau za mu fara ne da babbar manufar da ta sa aka samar da wannan dandali.
Manufar Samar da Dandalin Facebook
Daga bayanan da suka gabata kan tarihin wannan dandali masu karatu za su fahimci babbar manufar samar da wannan dandali; wato sadarwa irin ta abota ko zumunta.  Wannan shi ake kira “Social Networking.”  Wannan tsari a fili yake, amma ba kowa ke iya fahimtar hikimarsa ba, sai wanda ya mayar da hankalinsa kan dukkan ababen da masu shafin ko dandalin suka samar wajen aiwatar da wannan sadarwa a tsakanin jama’a.  Daga cikin tsare-tsaren wannan dandali da za mu duba cikin jerin kasidun da za mu kawo nan gaba, akwai manhajar sakonni, wato “Messages”, da manhajar neman abota, wato “Friend Rekuest,” da manhajar hirar ga-ni-ga-ka, wato “Chat,” da manhajar sanarwa, wato “Notifications,” inda za ka ga sanarwa da ake maka kan duk wani abin da kake da sila da shi.  Wasu daga cikin wadannan tsare-tsare sun hada da manhajar Zaure ko Dandali, wato “Groups,” inda jama’a ke tattaunawa kan al’amuran rayuwa baki daya.  Akwai manhajar shafukan tallace-tallace, wato “Pages,” wadanda ke bayar da damar tallata hajoji ko wani gwarzo, kamar yadda muka sani.
Bayan haka, akwai kuma tsare-tsare da aka samar wa mai shafi a Dandalin don inganta masa sadarwa tsakaninsa da jama’a.  Daga cikin tsare-tsaren akwai manhajoji, wato “Apps,” da kuma kafar samar da labaru, wato “News Feed,” da bangaren tallata wa mai shafi shafukan wasu, wato “Suggested Pages,” da “Suggested Friends,” da kuma “Suggested Groups.” Har wa yau, akwai hanyar taimaka wa mai shafi neman mutane, ko duk wani abin da ya shafe su: hotuna ne, soye-soyensu ne (likes), abokansu ne, garuruwansu ne, kasashensu ne, ko makarantu da wuraren ayyukansu.  Manhajar da ke taimakawa wajen yin hakan kuwa ita ce manhajar “Matambayi Ba Ya bata”, wato “Graph Search” da ke saman shafin kowane mai shafi a dandalin Facebook.
Wadannan kadan ne daga cikin abubuwan da ke inganta sadarwa a tsakanin jama’a a dandalin Facebook. Bayanai na nan zuwa kan kowannensu, daya bayan daya.

Na’ukan Shafin Dandalin Facebook
Dandalin Facebook ba gidan yanar sadarwa ba ne mai dauke da shafuka ’yan kididdigaggu da ke sarkafe a Uwar-garke (Serber) kwaya daya.  Nesa da haka.  Dandali ne da aka kera ko aka gina a tsari nau’i biyu; tsarin shiga ta kafar kwamfuta (na kan tebur ko na tafi-da-gidanka) – wato: “Desktop App” – da kuma tsarin shiga ta kafar wayar salula, wato: “Mobile App.”  Duk da cewa idan kana da wayar salula kana iya amfani da ita wajen shiga ta hanyar mashigar kwamfuta, wato: “Desktop App,” amma ba za ka iya shiga dandalin facebook da kwamfutarka ta amfani da mashigar wayar salula ba, wato: “Mobile App.”
Akwai nau’ukan masarrafar shiga shafukan yanar gizo da a Turancin kimiyyar sadarwa ake kira “Browser,” nau’i biyu.  A Hausance nakan kira su “Masarrafar lilo.”  Akwai wadanda aka gina don amfani da su a kwamfuta, da wadanda aka gina don amfanin wayar salula.  Kowanensu kana iya amfani da shi wajen shiga shafuka ko Dandalin Facebook cikin sauki.  
Sannan kana iya shiga dandalin Facebook ta hanyoyi guda biyu a wayar salula. Ko dai ta hanyar manhajar facebook da ke wayarka, wato: “Facebook Mobile App,” ko kuma ta amfani da masarrafar lilo, wato “Browser” ke nan.  Cikin mutane biliyan daya da miliyan dari daya da hamsin da ke da shafi a dandalin Facebook, an kiyasta cewa a duk wata daya, mutum miliyan dari takwas da hamsin (850m) na shiga shafukansu na Facebook ne ta hanyar wayar salula.
Tsarin Shiga Shafin Facebook
A tsarin mu’amala da shafukan yanar gizo (web pages), da zarar ka shigar da adireshin gidan yanar sadarwa ka matsa maballin “Enter” daga jikin allon shigar da bayananka (keyboard) ko na jikin wayarka, nan take masarrafar lilo (browser) za ta nemo maka bayanan wannan gidan yanar sadarwa daga Uwar-garken (Serber) da ke dauke da shafukan, sai su bayyana a shafin kwamfutarka ko wayarka. Amma a tsarin dandalin Facebook ba haka lamarin yake ba.
Idan kana son isa ga shafinka a dandalin facebook, da zarar ka shigar da adireshin shafin, abu na farko da wayarka ko kwamfutarka za ta fara isa gare shi shi ne babbar manhajar dandalin Facebook, wato “Facebook Platform.”  Daga nan sai wannan manhaja ta mika sakonka ko bukatarka ga babban rumbun bayanan dandalin, wato “Database.”  Idan kana da shafi a dandalin, Suna (Username) da Kalmar iznin shiga (Password) da ka shigar za su sa shaida ka, sai nan take rumbun bayanai ya cillo shafinka ga babbar manhajar dandalin, ita kuma ta cillo wa wayarka ko kwamfutarka, sai nan take ka ga shafinka ya bayyana.
Za mu cigaba