Yadda tsarin dandalin Facebook yake (2)

Da Me Aka Gina Shafukan Facebook? Kafin bayani kan da me aka gina shafukan dandalin facebook da muke mu’amala da su a kullum; ko dai ta wayoyin salularmu, ko ta shafukan kwamfutarmu, zai dace mu fahimci irin nauyi da wannan dandali ke dauke da shi.  Wannan ne zai taimaka mana wajen fahimtar dalilan da suka […]

Yadda tsarin dandalin Facebook yake (2)

Da Me Aka Gina Shafukan Facebook?

Kafin bayani kan da me aka gina shafukan dandalin facebook da muke mu’amala da su a kullum; ko dai ta wayoyin salularmu, ko ta shafukan kwamfutarmu, zai dace mu fahimci irin nauyi da wannan dandali ke dauke da shi.  Wannan ne zai taimaka mana wajen fahimtar dalilan da suka sa hukumar facebook suke amfani da irin masarrafai ko kayan aiki da ba kowane irin gidan yanar sadarwa ba ne ke dauke da su; a bayyane ne ko a boye, wadanda ba ma iya ganinsu da idanunmu.  
Bayanai sun gabata cewa a halin yanzu dandalin facebook na dauke ne da mutane miliyan dubu daya da dari biyu, wato biliyan daya da miliyan dari biyu ke nan (1,200,000,000).  Wannan dimbin jama’a na lilo ne a kan wannan dandali a kullum.  A yayin da ake samun masu shiga wannan shafi ta amfani da kwamfuta, kusan kashi 80 na shiga ne ta wayoyin salularsu, ko ta na’urorin sarrafa bayanai irin su iPad, da Samsung Galady Note ko Tab, da Google Nedus da dai sauran ire-irensu.  Wannan ke nuna irin girma, da sarkakiya da kuma tarin “kwazo” da wannan dandali ke da shi, musamman wajen karbar sakon bukatun jama’a (User Rekuests) a kullum.
Shekaru hudu da suka gabata, sadda mambobin wannan dandali ba su shige miliyan 800 ba, an kiyasta cewa a kowace dakika guda (second), dandalin facebook na samun bukatun jama’a sama da miliyan 15! – tsakanin masu kokarin shiga (log in), da masu kokarin fita (sign out), da masu budo hotuna, da masu lodawa, da masu zuba sakonni (posts), da masu nemansu don karantawa, da masu aika bukatar abota ga wasu (friend rekuests), da masu amsa bukatar abota, da masu loda wakoki, da masu nemansu don karantawa, da masu budo shafukan wasu don sanin tarihinsu, da masu rubuta tarihinsu a shafukansu, da masu yin rajista a farkon lokaci, da masu rufe shafukansu saboda wasu dalilai, da masu leken asiri kan wasu, da masu turo wa wasu sakonni ta manhajar sako (Message), da masu karanta sakonnin da wasu suka aiko musu.  A kowace dakika, ire-iren wadannan abubuwa ne ke faruwa a wannan dandali.
kari a kan alkaluman da suka gabata a baya, masana sun tabbatar da cewa a duk cikin minti 20, masu mu’amala a wannan shafi na aikawa ko loda hotuna miliyan biyu da dubu dari bakwai da goma sha shida (2,716,000).  A duk cikin minti 20 sukan yada (share) rariyar likau (web links) guda miliyan daya (1,000,000).  A duk minti 20 sukan makala sunayen abokansu kan hotunansu sau miliyan daya da dubu dari uku da ashirin da uku (1,323,000).  A duk cikin minti 20 na duniya, sukan rubuta sakonni a bangon shafinsu guda miliyan daya da dubu dari biyar da tamanin da bakwai (1,587,000).  A duk cikin minti 20 sukan fadi wani abu a shafinsu (status update) sau miliyan daya da dubu dari takwas da hamsin da daya (1,851,000).  A duk minti 20, masu karatu su kara sani, akan samu amsa bukatar neman abota (Friend Rekuests accept) guda miliyan daya da dubu dari tara da saba’in da biyu (1,972,000).  A duk minti 20 a dandalin facebook, ana samun ta’aliki kan rubutun wani (comments) guda miliyan goma da dubu dari biyu da takwas (10,208,000).   Sannan an tabbatar da cewa a duk minti 20 din nan dai har wa yau, masu mu’amala a shafin facebook na aikawa da sakonnin bayan fage (Pribate Messages ko Messages) guda miliyan hudu da dubu dari shida da talatin da biyu (4,632,000)!  Dankari!
Ga duk mutumin da ya san tsarin sadarwa ta kwamfuta, da yadda kwamfuta ke aika sako, da yadda take karbar sakon mai neman sako daga gare ta, idan Uwar Garke ce (Web Serber), ya san wannan ba karamin aiki ba ne. Sannan ba kowace irin kwamfuta ba ce za ta iya gabatar da ire-iren wadannan ayyuka a wannan zamani.  In kuwa haka ne, to da wadanne irin kwamfutoci ne Hukumar Dandalin facebook ke amfani da su wajen aiwatar da wannan aiki gagarumi?
Rothschild, daya daga cikin jami’an hukumar Facebook, ya ce wannan dandali na facebook na ajiye kwamfutocinsa ne a manyan biranen kasar Amurka guda uku. Birnin farko shi ne birnin San Francisco, birni na biyu Santa Clara, sai birni na uku, wato birginia.  Ya ce hukumar Facebook na amfani ne da kwamfutoci masu dauke da babbar manhajar Linud, masu dauke da masarrafar Uwar Garke (Serber) na manhajar Linud, wato Linud Serbers ke nan a Turance.  Wadannan kwamfutoci dai kowannensu na dauke ne da na’urar sarrafa bayanai da ake kira Processor, guda takwas!  Tirkashi!!  Wani aikin sai mai shi.   A yayin da kwamfutar zamanin yau na dauke ne da na’urar sarrafa bayanai guda daya, ko biyu, ko hudu, idan abu ya yi zafi.   Ba nan aka tsaya ba. Roth ya ce a kalla suna da irin wannan kwamfuta mai aikin aikawa da karbar bukatun masu mu’amala da dandalin facebook sama da guda 800!  Su ne a warwatse a wadannan birane, dauke da bayanan jama’a.   Mizanin wadannan kwamfutoci ya kai terabyte 40 (40 terabytes), wato Gigabyte biliyan 40 ke nan.  Wannan mizanin babbar ma’adana ke nan, wato Hard Disk Dribe.  Ma’adanar wucin-gadinsu kuma, wato RAM, ya kai terabyte 15, ko ka ce Gigabyte biliyan 15 ke nan.  Wannan ma’adana ta wucin-gadi ce ke dauke da shafukan da aka fi bukata, wadanda da zarar an tashi sake bukatarsu, a wannan ma’adana ake dauko su, ba sai an koma can cikin babbar ma’adana ba, don kauce wa tsaiko.