Yadda tsarin dandalin facebook yake (45
kari a kan alkaluman da suka gabata a baya, masana sun tabbatar da cewa a duk cikin minti 20, masu mu’amala a wannan shafi na aikawa ko loda hotuna miliyan biyu da dubu 716 (2,716,000). A duk cikin cikin minti 20 sukan yada (share) rariyar likau (web links) guda miliyan daya (1,000,000). A duk minti […]
kari a kan alkaluman da suka gabata a baya, masana sun tabbatar da cewa a duk cikin minti 20, masu mu’amala a wannan shafi na aikawa ko loda hotuna miliyan biyu da dubu 716 (2,716,000). A duk cikin cikin minti 20 sukan yada (share) rariyar likau (web links) guda miliyan daya (1,000,000). A duk minti 20 sukan makala sunayen abokansu kan hotunansu sau miliyan daya da dubu 323 (1,323,000). A duk cikin minti 20 na duniya, sukan rubutu sakonni a bangon shafinsu guda miliyan daya da dubu 587 (1,587,000). A duk cikin minti 20 sukan fadi wani abu a shafinsu (status update) sau miliyan daya da dubu 851 (1,851,000). A duk minti 20, masu karatu su kara sani, akan samu amsa bukatar neman abota (Friend Rekuests accept) guda miliyan daya da 972 (1,972,000). A duk minti 20 a dandalin facebook, ya kai mai karatu ka kara sani, ana samun ta’aliki kan rubutun wani (comments) guda miliyan goma da dubu dari biyu da takwas (10,208,000). Sannan an tabbatar da cewa a duk minti 20 din nan dai har wa yau, masu mu’amala a shafin facebook na aikawa da sakonnin bayan fage (Private Messages ko Messages) guda miliyan hudu da dubu dari shida da talatin da biyu (4,632,000)! Dankari!
Uku daga cikin manyan kalubale da ke fuskantar hukumar gudanarwar dandalin facebook dai su ne: dandazon sarkakiyar da ke cikin bukatar bayanai daga masu mu’amala a shafin a kowane dakika guda, da tarin yawan bayanai da ke taruwa tuli-tuli, a duk dakika guda (ciki har da wannan sako da kake karantawa), da kuma sarkakiyar da suke fuskanta wajen jera bayanai ta la’akari da mahimmancinsu wajen masu bukata a kowane lokaci.
Kada mai karatu ya rikice. Duk da wannan sarkakiya da yake jin ina ambato, abin mai sauki ne a misalin yau da kullum. Na yi bayani a baya cewa dandalin facebook na dauke da manyan vangarori uku ne. Akwai vangaren farko, wanda shi ne kamar idon-gari; in da duk masu mu’amala da shafin ke mu’amala da shi. Wannan vangare ne ke karVar sakonka – na bukatar neman aboki, ko neman wani shafi, ko tura sakon ta’aliki, ko wata bukata dai a takaice – kuma shi ne mai maido maka da jawabi – kan abin da ka bukata!Wannan a fili ke nan; abin da kuma kake gani ke nan.Amma ba shi ne mai hakikanin aikin ba.Shi dan sako ne. Wannan vangare shi suke kira “Front-End” a Turancin kimiyyar sadarwa na zamani.
Sai vangare na uku, wanda ke dauke da dukkan bayanan da muke mu’amala da dasu a makare. Wannan vangare shi ne vangaren ma’adanar kwamfuta mai dauke da babbar manhajar taskance bayanai da aka fi sani da “Database Servers” a Turance. Wannan vangare ne ke rike da dukkan bayanan da suka shafi dukkan masu shafi a dandalin facebook, a ajiye. A Turancin kimiyyar sadarwar zamani ana kiran wannan vangare da suna: “Back-End,”ko bayan gida.
Sai vangare na biyu wanda ke tsakanin vangaren farko da vangare na uku.Aikin wannan vangare shi ne kwafo shafukan da masu mu’amala da dandalin facebook suka fi bukata a dukkan lokuta.Idan ka shiga shafinka a karon farko, wannan vangare zai taskance shafin a ma’adanarsa. Da zarar ka sake shiga shafinka sai wannan vangare ya gano cewa ai ka shigo dazu, kuma akwai makwafin shafin da ka bukata a baya, sai kawai ya ba ka shafin nan take, ba sai ya koma asalin ma’adanar da ke vangare na biyu da bayaninsa ya gabata ba.Wannan vangare shi ake kira “Caching System.” Amfanin samar da wannan vangare shi ne don rage saibi ko nawa wajen dauko bayanan da ka bukata da ke makare a wancan ma’adana da ke bayan fage, ko “Back-End.” Watakila sai na kawo misali da tsarin banki sannan mai karatu zai fahimta.
A tsarin banki, idan ka kawo musu kudi ajiya, za a karVa a jiye a taskar bankin, wanda ke Babban Bankin Najeriya. Idan ka bukata ma za a je babban banki ne a dauko kudin, sai a biya ka. To amma ganin cewa kafin a je a dauko maka wani ma ya zo bukata, wanda hakan zai kawo tsaiko wajen kaikomo tsakanin bankinka da Babban Bankin Najeriya, sai kawai aka samar da wata ‘yar karamar ma’adana ta wucin-gadi a cikin bankin. Wannan ma’adana ita ake kira “Strong Room.” Maimakon a ce duk sa’adda ka bukaci kudinka a je Babban Bankin Najeriya a dauko a biya ka, sai a je cikin wannan ma’adana ta “Strong Room” a dauko wadanda aka karva na wasu, a ba ka. Idan kuma har lokacin tashi ya yi ba a samu masu bukatar karva ba, sai a koma da su taskar bankin da ke Babban Bankin Najeriya. To haka tsarin karva da mika bayanai yake a dandalin facebook.
Kada mai karatu dai ya mance cewa muna kan bayani ne kan: “Da wani irin kayan aiki aka gina shafukan dandalin facebook?” Wannan shi ne abin da ke tafe a kasida ta gaba in Allah ya so.
Da Me Aka Gina Shafukan Facebook?
Dandalin facebook na dauke ne da wani tsari mai ban mamaki, mai ban al’ajabi, mai kayatarwa, amma ga wanda ya san tsarin sadarwar zamani da yadda yake aiki a yau. Amma ga wanda bai sani ba, sai an yi masa kwatance mai saukin saukakewa, mai saukin fahimta. Muna iya fahimtar wannan sarkakiya ne daga irin alkaluman bayanai da ke fitowa daga masana kan yadda wannan dandali ke aiki, kamar yadda muka karanta a makonnin baya. Uku daga cikin manyan kalubale da ke fuskantar hukumar gudanarwar dandalin facebook dai su ne: dandazon sarkakiyar da ke cikin bukatar bayanai daga masu mu’amala a shafin a kowace dakika guda, da tarin yawan bayanai da ke taruwa tuli-tuli, a duk dakika guda, da kuma sarkakiyar da suke fuskanta wajen jera bayanai ta la’akari da mahimmancinsu wajen masu bukata a kowane lokaci.
Kada mai karatu ya rikice. Duk da wannan sarkakiya da yake jin ina ambato, abin mai sauki ne a misalin yau da kullum. Na yi bayani a baya cewa dandalin facebook na dauke da manyan vangarori uku ne. Akwai vangaren farko, wanda shi ne kamar idon-gari; in da duk masu mu’amala da shafin ke mu’amala da shi. Wannan vangare ne ke karVar sakonka – na bukatar neman aboki, ko neman wani shafi, ko tura sakon ta’aliki, ko wata bukata dai a takaice – kuma shi ne mai maido maka da jawabi – kan abin da ka bukata! Wannan a fili kenan; abin da kuma kake gani kenan.Amma ba shi ne mai hakikanin aikin ba.Shi dan sako ne. Wannan vangare shi suke kira “Front-End” a Turancin kimiyyar sadarwa na zamani.
Sai vangare na uku, wanda ke dauke da dukkan bayanan da muke mu’amala da dasu a makare. Wannan vangare shi ne vangaren ma’adanar kwamfuta mai dauke da babbar manhajar taskance bayanai da aka fi sani da “Database Servers” a turance. Wannan vangare ne ke rike da dukkan bayanan da suka shafi dukkan masu shafi a dandalin facebook, a ajiye. A Turancin kimiyyar sadarwar zamani ana kiran wannan vangare da suna: “Back-End,” ko bayan gida.
Sai vangare na biyu wanda ke tsakanin vangaren farko da vangare na uku. Aikin wannan vangare shi ne kwafo shafukan da masu mu’amala da dandalin facebook suka fi bukata a dukkan lokuta. Idan ka shiga shafinka a karon farko, wannan vangare zai taskance shafin a ma’adanarsa. Da zarar ka sake shiga shafinka sai wannan vangare ya gano cewa ai ka shigo dazu, kuma akwai makwafin shafin da ka bukata a baya, sai kawai ya ba ka shafin nan take, ba sai ya koma asalin ma’adanar da ke vangare na biyu da bayaninsa ya gabata ba. Wannan vangare shi ake kira “Caching System.” Amfanin samar da wannan vangare shi ne don rage saibi ko nawa wajen dauko bayanan da ka bukata dake makare a wancan ma’adana da ke bayan fage, ko “Back-End.” Watakila sai na kawo misali da tsarin banki sannan mai karatu zai fahimta.
A tsarin banki, idan ka kawo musu kudi ajiya, za a karVa a jiye a taskar bankin, wanda ke Babban Bankin Najeriya. Idan ka bukata ma za a je babban banki ne a dauko kudin, sai a biya ka. To amma ganin cewa kafin a je a dauko maka wani ma yazo bukata, wanda hakan zai kawo tsaiko wajen kaikomo tsakanin bankinka da Babban Bankin Najeriya, sai kawai aka samar da wata ‘yar karamar ma’adana ta wucin-gadi a cikin bankin. Wannan ma’adana ita ake kira “Strong Room.” Maimakon a ce duk sa’adda ka bukaci kudinka a je Babban Bankin Najeriya a dauko a biya ka, sai a je cikin wannan ma’adana ta “Strong Room” a dauko wadanda aka karva na wasu, a ba ka. Idan kuma har lokacin tashi ya yi ba a samu masu bukatar karva ba, sai a koma da su taskar bankin da ke babban bankin Najeriya. To haka tsarin karVa da mika bayanai yake a dandalin facebook.
Qari a kan alqaluman da suka gabata a baya, masana sun tabbatar da cewa a duk cikin minti 20, masu mu’amala a wannan shafi na aikawa ko loda hotuna miliyan biyu da dubu 716 (2,716,000). A duk cikin cikin minti 20 sukan yada (share) rariyar likau (web links) guda miliyan xaya (1,000,000). A duk minti 20 sukan maqala sunayen abokansu kan hotunansu sau miliyan xaya da dubu 323 (1,323,000). A duk cikin minti 20 na duniya, sukan rubutu saqonni a bangon shafinsu guda miliyan xaya da dubu 587 (1,587,000). A duk cikin minti 20 sukan faxi wani abu a shafinsu (status update) sau miliyan xaya da dubu 851 (1,851,000). A duk minti 20, masu karatu su qara sani, akan samu amsa buqatar neman abota (Friend Requests accept) guda miliyan xaya da 972 (1,972,000). A duk minti 20 a dandalin facebook, ya kai mai karatu ka qara sani, ana samun ta’aliqi kan rubutun wani (comments) guda miliyan goma da dubu dari biyu da takwas (10,208,000). Sannan an tabbatar da cewa a duk minti 20 xin nan dai har wa yau, masu mu’amala a shafin facebook na aikawa da saqonnin bayan fage (Private Messages ko Messages) guda miliyan hudu da dubu dari shida da talatin da biyu (4,632,000)! Dankari!
Uku daga cikin manyan qalubale da ke fuskantar hukumar gudanarwar dandalin facebook dai su ne: dandazon sarkakiyar da ke cikin buqatar bayanai daga masu mu’amala a shafin a kowane dakika guda, da tarin yawan bayanai da ke taruwa tuli-tuli, a duk dakika guda (ciki har da wannan sako da kake karantawa), da kuma sarqaqiyar da suke fuskanta wajen jera bayanai ta la’akari da mahimmancinsu wajen masu buqata a kowane lokaci.
Kada mai karatu ya rikice. Duk da wannan sarkakiya da yake jin ina ambato, abin mai sauki ne a misalin yau da kullum. Na yi bayani a baya cewa dandalin facebook na xauke da manyan vangarori uku ne. Akwai vangaren farko, wanda shi ne kamar idon-gari; in da duk masu mu’amala da shafin ke mu’amala da shi. Wannan vangare ne ke karVar sakonka – na buqatar neman aboki, ko neman wani shafi, ko tura sakon ta’aliqi, ko wata buqata dai a taqaice – kuma shi ne mai maido maka da jawabi – kan abin da ka buqata!Wannan a fili ke nan; abin da kuma kake gani ke nan.Amma ba shi ne mai haqiqanin aikin ba.Shi dan saqo ne. Wannan vangare shi suke kira “Front-End” a Turancin kimiyyar sadarwa na zamani.
Sai vangare na uku, wanda ke xauke da dukkan bayanan da muke mu’amala da dasu a maqare. Wannan vangare shi ne vangaren ma’adanar kwamfuta mai xauke da babbar manhajar taskance bayanai da aka fi sani da “Database Servers” a Turance. Wannan vangare ne ke rike da dukkan bayanan da suka shafi dukkan masu shafi a dandalin facebook, a ajiye. A Turancin kimiyyar sadarwar zamani ana kiran wannan vangare da suna: “Back-End,”ko bayan gida.
Sai vangare na biyu wanda ke tsakanin vangaren farko da vangare na uku.Aikin wannan vangare shi ne kwafo shafukan da masu mu’amala da dandalin facebook suka fi buqata a dukkan lokuta.Idan ka shiga shafinka a karon farko, wannan vangare zai taskance shafin a ma’adanarsa. Da zarar ka sake shiga shafinka sai wannan vangare ya gano cewa ai ka shigo xazu, kuma akwai makwafin shafin da ka buqata a baya, sai kawai ya ba ka shafin nan take, ba sai ya koma asalin ma’adanar da ke vangare na biyu da bayaninsa ya gabata ba.Wannan vangare shi ake kira “Caching System.” Amfanin samar da wannan vangare shi ne don rage saibi ko nawa wajen xauko bayanan da ka buqata da ke maqare a wancan ma’adana da ke bayan fage, ko “Back-End.” Wataqila sai na kawo misali da tsarin banki sannan mai karatu zai fahimta.
A tsarin banki, idan ka kawo musu kuxi ajiya, za a karVa a jiye a taskar bankin, wanda ke Babban Bankin Najeriya. Idan ka buqata ma za a je babban banki ne a xauko kuxin, sai a biya ka. To amma ganin cewa kafin a je a xauko maka wani ma ya zo buqata, wanda hakan zai kawo tsaiko wajen kaikomo tsakanin bankinka da Babban Bankin Najeriya, sai kawai aka samar da wata ‘yar qaramar ma’adana ta wucin-gadi a cikin bankin. Wannan ma’adana ita ake kira “Strong Room.” Maimakon a ce duk sa’adda ka buqaci kuxinka a je Babban Bankin Najeriya a xauko a biya ka, sai a je cikin wannan ma’adana ta “Strong Room” a xauko waxanda aka karva na wasu, a ba ka. Idan kuma har lokacin tashi ya yi ba a samu masu buqatar karva ba, sai a koma da su taskar bankin da ke Babban Bankin Najeriya. To haka tsarin karva da miqa bayanai yake a dandalin facebook.
Kada mai karatu dai ya mance cewa muna kan bayani ne kan: “Da wani irin kayan aiki aka gina shafukan dandalin facebook?” Wannan shi ne abin da ke tafe a qasida ta gaba in Allah ya so.
Da Me Aka Gina Shafukan Facebook?
Dandalin facebook na xauke ne da wani tsari mai ban mamaki, mai ban al’ajabi, mai qayatarwa, amma ga wanda ya san tsarin sadarwar zamani da yadda yake aiki a yau. Amma ga wanda bai sani ba, sai an yi masa qwatance mai sauqin sauqaqewa, mai sauqin fahimta. Muna iya fahimtar wannan sarqaqiya ne daga irin alqaluman bayanai da ke fitowa daga masana kan yadda wannan dandali ke aiki, kamar yadda muka karanta a makonnin baya. Uku daga cikin manyan qalubale da ke fuskantar hukumar gudanarwar dandalin facebook dai su ne: dandazon sarqaqiyar da ke cikin buqatar bayanai daga masu mu’amala a shafin a kowace daqiqa guda, da tarin yawan bayanai da ke taruwa tuli-tuli, a duk daqiqa guda, da kuma sarkakiyar da suke fuskanta wajen jera bayanai ta la’akari da mahimmancinsu wajen masu buqata a kowane lokaci.
Kada mai karatu ya rikice. Duk da wannan sarkakiya da yake jin ina ambato, abin mai sauki ne a misalin yau da kullum. Na yi bayani a baya cewa dandalin facebook na xauke da manyan vangarori uku ne. Akwai vangaren farko, wanda shi ne kamar idon-gari; in da duk masu mu’amala da shafin ke mu’amala da shi. Wannan vangare ne ke karVar sakonka – na buqatar neman aboki, ko neman wani shafi, ko tura sakon ta’aliki, ko wata buqata dai a takaice – kuma shi ne mai maido maka da jawabi – kan abin da ka buqata! Wannan a fili kenan; abin da kuma kake gani kenan.Amma ba shi ne mai haqiqanin aikin ba.Shi dan sako ne. Wannan vangare shi suke kira “Front-End” a Turancin kimiyyar sadarwa na zamani.
Sai vangare na uku, wanda ke xauke da dukkan bayanan da muke mu’amala da dasu a makare. Wannan vangare shi ne vangaren ma’adanar kwamfuta mai xauke da babbar manhajar taskance bayanai da aka fi sani da “Database Servers” a turance. Wannan vangare ne ke rike da dukkan bayanan da suka shafi dukkan masu shafi a dandalin facebook, a ajiye. A Turancin kimiyyar sadarwar zamani ana kiran wannan vangare da suna: “Back-End,” ko bayan gida.
Sai vangare na biyu wanda ke tsakanin vangaren farko da vangare na uku. Aikin wannan vangare shi ne kwafo shafukan da masu mu’amala da dandalin facebook suka fi buqata a dukkan lokuta. Idan ka shiga shafinka a karon farko, wannan vangare zai taskance shafin a ma’adanarsa. Da zarar ka sake shiga shafinka sai wannan vangare ya gano cewa ai ka shigo xazu, kuma akwai makwafin shafin da ka buqata a baya, sai kawai ya ba ka shafin nan take, ba sai ya koma asalin ma’adanar da ke vangare na biyu da bayaninsa ya gabata ba. Wannan vangare shi ake kira “Caching System.” Amfanin samar da wannan vangare shi ne don rage saibi ko nawa wajen xauko bayanan da ka buqata dake makare a wancan ma’adana da ke bayan fage, ko “Back-End.” Wataqila sai na kawo misali da tsarin banki sannan mai karatu zai fahimta.
A tsarin banki, idan ka kawo musu kuXi ajiya, za a karVa a jiye a taskar bankin, wanda ke Babban Bankin Najeriya. Idan ka buqata ma za a je babban banki ne a xauko kuxin, sai a biya ka. To amma ganin cewa kafin a je a xauko maka wani ma yazo buqata, wanda hakan zai kawo tsaiko wajen kaikomo tsakanin bankinka da Babban Bankin Najeriya, sai kawai aka samar da wata ‘yar qaramar ma’adana ta wucin-gadi a cikin bankin. Wannan ma’adana ita ake kira “Strong Room.” Maimakon a ce duk sa’adda ka buqaci kuxinka a je Babban Bankin Najeriya a xauko a biya ka, sai a je cikin wannan ma’adana ta “Strong Room” a xauko waxanda aka karva na wasu, a ba ka. Idan kuma har lokacin tashi ya yi ba a samu masu buqatar karva ba, sai a koma da su taskar bankin da ke babban bankin Najeriya. To haka tsarin karVa da miQa bayanai yake a dandalin facebook.