Yadda tsayi ko gajartarka za su iya shafar lafiyarka

Kasashen Arewacin Turai irin su Sweden da Holland da Rasha su suka fi kowa tsayi a duniya.

Yadda tsayi ko gajartarka za su iya shafar lafiyarka

Dogo da gajeren mutum

Tsayi ko gajarta na iya shafar lafiya. Matsakaicin tsayi shi ne mita 1.7 a maza, a mata kuma mita 1.6.

Sama da wannan maki mutum za a iya ce masa/mata dogo ko doguwa, kasa da haka gajere ko gajera.

Kasashen Arewacin Turai irin su Sweden da Holland da Rasha su suka fi kowa tsayi a duniya, inda yawancinsu sun kai mita 1.8.

Kasashen Gabashin Asiya kuma irin su Thailand da Myanmar da Timor ta Gabas su suka fi kowa gajarta, inda masu tsayin mita 1.7 ba su da yawa.

Kowace irin halitta Allah Ya yi wa mutum akwai cututtukan da hakan zai iya zama kariya daga su.