Yadda tsofaffi 3 ke fasa gidajen mutane suna sata

Tsofaffin sun haɗa tawaga bayan fitowa daga gidan yari, inda suka shiga aikata sata.

Yadda tsofaffi 3 ke fasa gidajen mutane suna sata

Wasu tsofaffi uku da adadin shekarunsu ya kai 227, sun shiga hannu kan zargin aikata fashi da makami.

Wanɗanda ake zargin masu suna, Hideo mai shekara 88 da Hidemi Matsuda mai shekara 70 da Kenichi Watanabe mai shekara 69, sun shiga hannu kan zargin aikata fashi da makami.

Labarin ya zama tamkar wani shirin wasan kwaikwayo na Hollywood, inda tsofaffin uku suka haɗu a kurkuku kuma daga baya suka haɗa kai don yin fashi.

Irin wannan yanayi ne, ya faru a Japan kuma ya janyo hankalin duniya.

Abin mamaki shi ne dukkanin tsofaffin uku sun kusa haura shekara 70.

Saboda haka, aka kira su da “tawaga ko gungun kakanni” a Japan.

A cewar rahoton da Jaridar The South China Morning Post ta wallafa tsofaffin uku, sun zama masu fuskokin da ba a taɓa ganin irinsu ba a Japan.

’Yan sanda sun yi masu laƙabi da “G3S”- ana yi masu laƙabin barkwanci a Japan da grandpas wato kakanni – bayan an zarge su da aikata jerin sata a Tsibirin Hokkaido da ke Arewacin ƙasar.

Ana zargin Hideo Umino, Hidemi Matsuda da Kenichi Watanabe da kitsa yadda za su aikata laifuffuka ne a lokacin da suke zaman gidan yari.

Bayan sakin su, sai tsofaffin uku suka karkatar da hankalinsu ga abin duniya, suna kai hari gidajen da ba kowa da sunan sata.

An yi zargin cewa tawagarsu ta kutsa cikin wani gida da ba kowa a yankin Sapporo, babban birnin Hokkaido a watan Mayun bana.

Sai dai harin nasu bai samu nasara ba, domin satar Dala 1.3 (kimanin Naira dubu 2,126 da kwabo 74 da kwalaba uku na giyar wiski da aka kimanta kuɗinta kan Dala 65 (kimanin Naira dubu 163 da 36 da kwabo 75 suka sata.

An kuma zargin su da sake kai hari a watan jiya a wannan karon sun saci kayan ado 24 da darajarsu ta kai Dala 6,400 a wani gidan da ba kowa a ciki.

Labarin laifuffukan da ake zargin gungun tsofaffin na aikatawa ya riƙa yaɗuwa, inda nan da nan suka zama abin mamaki da ke ɗaukar hankalin jama’a saboda lamarin nasu ya zama sabon abu.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja