Yadda uba ya yi wa dansa gunduwa-gunduwa
Wani magidanci ya daddatsa dan cikinsa mai shekara hudu ya kuma binne gawar a cikin gidansa. Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar ta Anambra, SP Haruna Mohammed ya ce tuni ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Azia ya cika hannu da mutumin dan garin Ihite Azia da ke jihar. “Da misalin karfe 3:21 na […]
Wani magidanci ya daddatsa dan cikinsa mai shekara hudu ya kuma binne gawar a cikin gidansa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar ta Anambra, SP Haruna Mohammed ya ce tuni ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Azia ya cika hannu da mutumin dan garin Ihite Azia da ke jihar.
“Da misalin karfe 3:21 na ranar tara ga watan Yulin 2020, ‘yan sanda a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra suka cafke wani magidanci dan kimanin shekaru 35.
“Ana zargin mutumin ne da daddatsa dan cikinsa mai kimanin shekaru hudu ta hanyar yin amfani da adda, sannan ya binne gawar a cikin wani kuntataccen kabari a cikin gidan nasa”, inji shi.
Ya ce sun samu nasarar tono gawar yaron bayan da suka gano cewa mahaifinsa ya binne shi a cikin gidansa bayan da ya kashe shi.
“Yanzu haka mun mika batun zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na hedikwatar ‘yan sanda da ke birnin Awka don fadada bincike”, inji sanarwar ‘yan sandan.