Yadda uwa da da suka kashe dan shekara biyar suka binne a daki

An kama wata mata mai suna Lalai da danta mai suna Bala bisa zarginsu da kashe wani yaro dan shekara biyar mai suna Adamu Walid a Unguwar Hayin danmani kusa da garin Kaduna da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna. Lalai da danta Bala ana zargin sun sace yaron ne a ranar 23 ga […]

Yadda uwa da da suka kashe dan shekara biyar suka binne a daki

An kama wata mata mai suna Lalai da danta mai suna Bala bisa zarginsu da kashe wani yaro dan shekara biyar mai suna Adamu Walid a Unguwar Hayin danmani kusa da garin Kaduna da ke karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Lalai da danta Bala ana zargin sun sace yaron ne a ranar 23 ga Janairun da ya gabata a hanyarsa ta zuwa makarantar Islamiyya da ke unguwarsu sannan suka kashe shi suka binne a dakin Bala, kafin asirinsu ya tonu.

A cewar iyayen Walid sa’o’i kadan da sace shi, sai aka kira su a waya ana neman su biya fansar Naira dubu 300. Sun ce matar da ake zargin ’yar uwar kakar Walid ne kuma ta yi amfani da sanayya ce wajen sace shi.

Mahaifin yaron wanda sana’arsa tuka motar ruwa ce, mai suna Abubakar Ya’u ya ce “dana ne kuma shi ne na uku daga cikin ’ya’yana hudu. Hakika abin bakin ciki ne da takaici domin bayan an shirya shi ya tafi makarantar Islamiyya ne ta bi shi can ta dauke shi. Bayan ’yan uwansa sun koma gida sai suka ce ba a ga Walid ba, daga nan mahaifiyarsa da makwabta suka fita nemansa amma ba su gan shi ba, sai da misalin karfe uku, wacce ake zargin suka kira wayar yayana suka ce sun sace dan kanensa kuma sai an ba su Naira dubu 300 kafin su sako shi ko kuma su kashe shi.”

Ya kara da cewa “Da ya fada min haka sai na ce da shi a ina zan samo Naira dubu 300. Domin sana’ar tuka motar sayar da ruwa nake yi, ni ba wani mai kudi ba ne. Muna ta kokarin nemo kudin sai suka sake kira suka ce a ba su Naira dubu 150, kai har suka dawo suka bukaci a aika musu da Naira dubu 20.”

Ya ce, “Bayan mun sanar da ’yan sanda sai suka ce ba za a kai kudin ba sai an hada mu da ’yan sanda. Da suka sake kira sai suka aiko da lambar asusun ajiyarsu na banki suka ce a tura musu kudin. Bayan an aika musu da kudin ne sai aka ce Bala ya je ya sayi wayar hannu a wajen wani yaro ya fada masa cewa za a aiko masa da Naira dubu 20 don haka ya je ya ciro Naira dubu 15 ya kawo masa ragowar Naira dubu biyar a banki. Dama kafin su je bankin an sanar da ma’aikatan bankin halin da ake ciki. Da suka je cire kudin ne aka kama mai wayar daga nan bincike ya kai ga kama mahaifin Bala da mahaifiyarsa da aka yi amfani da wayarta wajen yin kiran.

Abubakar ya ce ’yan uwan Bala ne suka taimaka wajen kama shi bayan ya yi kokarin gudu lokacin da ya samu labarin ’yan sanda sun tsare mahaifinsa. 

Daga baya an sako mahaifin Bala da mai wayar saboda an fahimci ba su da masaniya a kan lamarin.

Game da abin da yake so a yi wa wadanda suka kashe dansa, Abubakar Ya’u ya ce, “Duk abin da Allah Ya kaddara zai faru sai ya faru saboda haka mun bar wa Allah komai. Amma gwamnati ina son ta aiwatar da duk hukunci da take yi wa masu aikata irin wannan mugun hali.”

Aminiya ta samu labarin cewa matar da ake zargi tana da ’ya’ya tara.

Lokacin da wakilin Aminiya ya ziyarci sashin binciken manyan laifuffuka na Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, inda suke tsare an hana shi ya yi magana da su, amma wani bidiyo da Aminiya ta samu ta ga inda aka tattauna da wadanda ake zargin suna nuna inda suka binne yaron a cikin dakin Bala sannan suka shafe da siminti Bala ya mayar da komatsansa a kai ya ci gaba da zamansa a ciki. 

Bayanai sun ce, Lalai ta bukaci danta Bala ya yanka Walid saboda suna ganin ya gane su, amma ya ce ba zai iya yanka yaron ba, don haka sai Lalai ta ba shi guba a cikin abinci ya ci. Da ya rasu sai suka binne shi a cikin dakin Bala kuma ya ci gaba da kwana a ciki abin sa.

Bayan an kama su ne suka je suka nuna wa ’yan sanda inda suka binne yaron aka hako gawarsa. Bala ya fada wa ’yan sandan cewa da fartanya ya haka ramin a cikin dakin kafin ya binne yaron.

Kakan yaron na wajen uba, Alhaji Ya’u Yahaya ya ce saboda iya makirci da Lalai ake zuwa gidan iyayen yaron jaje ba tare da ta nuna cewa yaron na wajenta ba.

Sai dai ya ce ba su da wata alaka ta jini da ita illa aure da ya hada iyayenta da gidan mahaifiyar kakar Walid a can Dawakin Tofa da ke Jihar Kano shekaru masu yawa.

“Wannan ne ya sa ake ta zumunci tare amma babu wata alaka ta jini da su. Amma dai a ce wai mutumin da ka dauka dan uwa shi ne kuma zai aikata maka irin wannan mummunan aiki akwai ta da hankali. Don haka muna fata hukuma ta yi mana adalci,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Aliyu Muktar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce za su mika wadanda ake zargi zuwa kotu da zarar sun kammala bincikensu.