Yadda uwa ta kashe ’yarta kan yawon ta-Zubar

Matar ta caka wa budurwar wuka saboda yawon gantalin.

Yadda uwa ta kashe ’yarta kan yawon ta-Zubar

’Yan sanda a Jihar Ogun sun kama wata uwa da ta aika ’yarta lahira kan yawon ta-zubar.

Mahaifiyar budurwar ta yi wannan aika-aika ne a lokacin da take yi wa ’ya’yanta dukan kawo-wuka saboda yawon ta-zubar da suke yi.

Matar ta shaida wa ’yan sanda cewa yawon ta-zubar da ’ya’yan nata ’yan mata su biyu, mai shekara 19 da mai shekara 17 suke yi ne ya sa ta takaici har ta hau dokin zuciya da ya kai ga daukar matakin da ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikinsu.

Ta ce tun shekara tara da suka gabata aurenta da mahaifin ’yan matan ya mutu, kuma tun daga lokacin ita ke kula da dawainiyarsu.

Ta bayyana cewa a ranar Sallah Babbar da ta gabata ’yan matan sun fita waje kuma ba su dawo gida ba har sai da gari ya waye.

Hakan ne ya fusta ta, har ta yi yunkurin lakada musu duka amma makwabta suka shiga tsakani suka hana ta.

Washegari kuma ’ya’yan nata suka kara fita wani yawon gantalin, ba su suka dawo ba, sai bayan kwana daya.

Hakan ne ya kara harzuka ta har ta kulle su a daki ta yi ta jibgar su.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa a lokacin da matar take dukan ’ya’yan nata ne ta caka wa babbar ’yar tata kwalba a hannu.

Bayan nan kuma ta caka wa karamar ’yar kwalba a kirji, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta bayan an garzaya da yaran zuwa asibiti.

Abimbola Oyeyemi ya ce rukumar ’yan sandan na binciken matar da ake zargi da kashe ’yar tata a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja