Yadda wa ya yi wa ƙanwarsa yankan rago bayan ya yi garkuwa da ita
Wanda ake zargin, ɗan yar mahaifin yarinyar da ya kashe ne da dukkansu ke zaune a Zariya.
A makon jiya ne aka wayi gari da mummunan labari na yadda wani yaya, ya yi garkuwa da ƙanwarsa, sannan ya yi mata yankan rago da reza.
Aminiya ta gano cewa wanda ake zargin, ɗan yar mahaifin yarinyar da ya kashe ne, da dukkansu suke zaune a Zariya.
Mahaifin yarinyar A’isha, Malam Sa’idu Ɗahiru ya bayyana wa Aminiya halin da suka samu kansu lokacin da ta ɓace har yazuwa lokacin da suka tabbatar da cewa ba ta raye.
Ya ce Abdul’aziz wanda ɗa ne a wurinsa shi ne ya yi garkuwa da ’yarsa kuma ya kashe ta ya jefa gawarta a rijiya kimanin wata huɗu da suka gabata.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Ceto Yaron Da Ya Kamu Da Jijjiga
- An soma aikin ceto bayan Shugaban Iran ya yi hatsarin jirgin sama
Malam Sa’idu ya ce da farko wani da bai san wane ne ba ya kira shi ta waya yana neman kuɗin fansar ’yarsa har Naira miliyan takwas matuƙar yana son a dawo masa da ita cikin aminci ba tare da wata illa ba.
Mahaifin ya ce an kama Abdul’aziz Idris ne a Ƙaramar Hukumar Makarfi lokacin da dubunsa ta cika, kuma a yanzu yana Sashin Kula da Laifuffukan Garkuwa da Mutane ana gudanar da bincike a kan lamarin.
Ya ce Abdul’aziz Idris ya bayyana wa ’yan sanda yadda ya yi wa yarinyar yankan rago da reza bayan ta gane shi.
A cewar mahaifin, a ranar da ya ɗauki A’isha, ranar ce amaryarsa ta haihu, kuma dukkan hidimar suna, shi ya ɗauki nauyi, hasali ma sunansa aka sanya wa ɗan.
Ita ma da take bayyana alhininta cikin kuka mahaifiyar A’isha, Malama Maijidda Sa’idu ta ce sun samu kansu a cikin yanayi na ɗimuwa da firgici a kan inda yarinyarsu ta shiga amma sai suka duƙufa da addu’o’in Allah Ya bayyana ta.
Maijidda ta ce A’isha yarinya ce mai hankali da natsuwa saboda duk lokacin da mahaifinta zai fita sai ta yi masa addu’o’in Allah Ya tsare shi Ya ba shi nasara kuma ya dawo lafiya.
A halin da ake ciki mutane suna ci gaba da nuna alhini da juyayi bisa yadda cin amana ke neman hallaka ’yan uwa sakamakon kisan A’isha Sa’idu mai shekara 6 da ɗan uwanta ya yi.
Waɗanda suka san marigayiyar, da irin halayen da take tasowa da su, sun nuna cewa an yi rashin ƙaramar yarinya da ta fara tasowa da halaye na ƙwarai.
Aminiya ta gano cewa a ranar da lamarin ya faru, A’isha tana kan hanyarta ta zuwa makarantar Islamiyya ce sai ɗan uwanta nata Abdul’aziz Idris ya ɗauke ta ya nufi garin Maƙarfi da ita ya ɓoye da sunan ya yi garkuwa da ita.
Bayan ya ɓoye ta, sai ya nemi a ba shi kuɗin fansar Naira miliyan 8, domin ya sako ta, inda aka yi tata-ɓurza tsakaninsa da mahaifinta, inda wanda yake ta ƙoƙarin samun kuɗin fansa domin a sako ta.
Aminiya ta gano cewa daga bisani ya yi mata yankan rago da reza saboda ya fahimci ba zai samu kuɗin da ya nema ba, sannan yana tunanin ta gane shi.
Wani shugaban al’umma, Malam Kabiru Musa ya ce sai al’umma sun tashi da addu’o’i domin lamarin na neman wuce gona-da-iri kasancewar ɗan gida ne ya ɗauki ’yar gidansu ya nemi kuɗin fansa kuma ya hallaka ta.
Da yake tsokaci kan yawaitar aikata irin wannan mummunan laifi, wani tsohon alƙali, Malam Shehu Salisu, ya ce rashin zartar da hukunci bayan alƙalai sun kammala shari’a a kan mai laifi ne ke daɗa jawo haka.
Ya ce, sai a kai mutum gidan yari a ajiye shi tsawon lokaci idan wani mai mulki ya hau sai a ce a yi masa afuwa, hakan na cikin abubuwan da suke mayar da hannun agogo baya.
Ya ce shi kansa ya taɓa yanke irin wannan hukunci kamar shekara 20 da suka wuce, amma har zuwa yau ba a zatar da hukuncin ba.
“Don haka kullum za ka ga irin waɗannan munanan laifuffuka na ƙaruwa,” in ji shi.
Shugaban Majalisar Malamai ta Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iƙamatis Sunnah (JIBWIS) ta Jihar Kaduna, Imam Aliyu Abdullahi Teleɗ, ya yi kira ga mahukunta su riƙa zartar da hukunci idan aka tabbatar da laifi a kan mutum domin hakan zai kawo aminci da zaman lafiya a ƙasa.
Ya ce idan aka riƙa siyasantar da shari’a, dole ne a kasance a cikin irin wannan yanayi na fargaba da rashin kwanciyar hankali.
Ya ce watsi da shari’a na haifar da bala’i iri-iri a ƙasa.
Sai ya shawarci al’umma musamman matasa su saki al’adun da ba nasu ba su koma ga Allah domin komai ya koma daidai.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir ya ce ’yan sanda sun kama Abdul’aziz Idris a Ƙaramar Hukumar Maƙarfi da ke jihar, inda a yanzu Sashen Kula da Laifuffukan Garkuwa da Mutane ke bincike a kan lamarin.
A sanarwar da ya fitar, ya ce matashin ya bayyana wa ’yan sanda yadda ya yi wa yarinyar yankan rago bayan ta gane shi.
Kakakin ’yan sandan ya ce matashin ya ce ya yi wa yarinyar yankar rago da reza ne sannan ya jefar da gawarta a cikin wata rijiya.
Ya ce, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Audu Ali Dabigi, ya bai wa al’umma tabbacin bin diddigin lamarin cikin tsanaki domin tabbatar da an bi wa yarinyar da iyayenta haƙƙinsu.
“Nan gaba kaɗan za a miƙa matashin ga kotu da zarar ’yan sanda sun kammala bincike,” in ji sanarwar.