Yadda Wahalar Man Fetur Ta Yi Tsanani A Najeriya

’Yan bumburutu na sayar da litar man fetur a kan Naira 1,300

Yadda Wahalar Man Fetur Ta Yi Tsanani A Najeriya

Yadda ababen hawa ke bin layin shan man fetur a Abuja

Har yanzu man fetur na wahala a Najeriya, abin da ya janyo masu bumburutu suke sayar da  lita guda a kan N1,200 zuwa N1,300.

Binciken da muka gudanar a sassan ƙasar ya nuna cewa gidajen mai da dama suna rufe, waɗanda suke ɗan buɗewa kuma ana shan baƙar wahala a layi kafin a samu.

Ana ci gaba da shan wahalar ne duk da iƙirarin Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi na cewa ya shawo kan matsalar tun ranar Juma’a da ta gabata.

Wakilanmu a Abuja da wasu jihohi sun tabbatar mana da cewa gidajen man da ke sayar da fetur ɗin sun ƙara kuɗin lita zuwa N750, wasu kuma Naira 800.

Sai dai kuma, gidajen mai mallakin NNPCL suna sayarwa a kan N617, amma akwai dogon layin da sai mai rabo ke iya samu.

Kawo yanzu dai ma’aikata da ’yan kasuwa a jihohin Najeriya na takawa a ƙasa, wasu kuma suna biyan ninkin abin da a baya ake biya saboda wahalar da direbobi ke sha wurin samun man.

A Dutse da ke Jihar Jigawa, an rufe gidajen mai da dama, sai ’yan bumburutu ne ke cin kasuwarsu, inda suke sayar da lita ɗaya a kan Naira 1,100.

A yankin Maryland da ke Ikeja a Jihar Legas, sakamakon rufe gidajen mai na NNPC da ke can, ’yan bumburutu na sayar da lita biyar kan Naira 5,500.

Shugaban kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta (IPMAN) da ke Ejigbo a Legas, Akinrinade Akinade, ya ce yawancin dafo ɗin man da ke Legas ba su da mai.

“Matsala ce da ke shafar kusan ko’ina. A zahirin gaskiya ba mu da mai a dafo. Ba mu da inda za mu samo kuma.

“Idan babu to kawai  babu. Idan akwai ai dole mutane za su yi lodi. Ba na tsammanin hakan ya faru ne saboda wani shiri na rage farashin,” in ji shi.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta