Yadda wakar ‘Ban San Tsoro Ba’ ta hada kan ’yan fim a Instagram
A kwanakin baya ne fitaccen mawakin fina-finan Hausa, Nazifi Asnanic ya fitar da sabuwar wakarsa mai suna ‘Ban San Tsoro Ba’ inda hakan ya sanya masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finan Hausa suka rika yayinta a kafar sada zumunta ta Instagram.Wakar mai tsawon minti 5 da sakan 17, wadda aka yi ta da kidan […]
A kwanakin baya ne fitaccen mawakin fina-finan Hausa, Nazifi Asnanic ya fitar da sabuwar wakarsa mai suna ‘Ban San Tsoro Ba’ inda hakan ya sanya masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finan Hausa suka rika yayinta a kafar sada zumunta ta Instagram.
Wakar mai tsawon minti 5 da sakan 17, wadda aka yi ta da kidan kalangu da kuma busar sarewa mai ratsa jiki, Ali Nuhu ne ya fara sanya bidiyonsa a Instagram yana rera ta. Jarumin ya dauki kansa a bidiyo yana bin wakar ta tsawon sakan 30. Hakan ya sanya mabiya shafin Instagram kimanin 1,567 suka latsa alamar son wakar, inda aka yi magana a kanta sau 127.
Daga nan ne fitaccen jarumi Adam A. Zango da tawagarsa da ta hada da darakta Falalu dorayi da jaruma A’isha Tsamiya da Kabir Zango suka dauki bidiyo, suna kwaikwayon wakar sannan suka sanya a Instagram.
Ali Jita da Umar Gombe sun sanya hoton bidiyonsu suna gwada karfi hade da bayyana cewa ba su san tsoro ba.
Jaruma Nafisa Abdullahi ma ta sanya bidiyon da ta dauka a cikin mota inda take bin wakar.
Halima Atete da Isa Alolo da Sadik N. Mafiya da Umar M. Shareef da Bello Muhammad Bello da Nuhu Abdullahi da Sani Maikatanga da Yakubu Muhammad da sauransu sun sanya bidiyonsu a Instgaram a lokacin da suke kwaikwayon wakar.
Darakta Kamal S. Alkali wanda ya sanya hotonsa a Instagram, inda yake sanye da jar riga da bakin tabarau, sannan a jikin hoton ya rubuta ‘Ban San Tsoro Ba’ ya bayyana wa Aminiya cewa wakar ta hada kan ’yan fim a Instagram ne saboda sakon da take dauke da shi, sannan mawakin yana zaune da kowa lafiya.
Mawaki Umar M. Shareef ya ce wakar tana dauke da dimbin sakonnin da idan mai sauraro ya yi amfani da su, to ba zai ji tsoron kowa ba idan ba Allah ba, domin mawakin ya bayyana duk wanda ya dogara ga Allah ba zai fadi kasa ba.
Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana jin dadinta dangane da yadda mawakin ya yi amfani da kyawawan lafuzza wajen jan hankalin mata dangane da illar canja launin fata (bleaching), sanya A-Cuci-Maza da kuma kiran su daina shigar tsiraici.
Shin yaya wakar take ne? Ga baitukanta kamar yadda Asnanic ya rera ta:
Amshin wakar:
Ban san tsoro ba.
Ban san tsoro ba.
Ban san tsoro ba.
Ban san wannan ba.
Tsoron Allah shi ne ba wai na mutum ba.
Ba za na ji tsoron marar tsoron Allah ba.
Ya za na yi in yi Sallah, Alwala ban yo ba?
Sakona shi ne ban san tsoro ba.
1-Gaskiya dokin karfe ce babba,
Mai gaskiya ba za ya fado kasa ba,
Ko da ka fadi ma ba sa cin maka ba,
Tsoron Allah shi ne ribar babba,
Soyayyar Allah ita ce na sa a gaba,
Idan wani ya ki ka wani zai so ka a gaba,
Wani bai so ba wani bai ma tanka ba,
Takena shi ne ban san tsoro ba.
(Ban san tsoro ba)
2-Eye, na zaune an ce bai ga gari ba.
Bai san ana kai wa kawowa ba.
Matsoraci ba zai taba yin suna ba,
Domin ba zai burge dan kowa ba.
Ni dai na furta ban san tsoro ba.
3-Allah bai hana bawa sai in bai roka ba.
Ba ai maka illa in ba ka bar Allah ba.
In ka yarda da Allah ba za ka rasa ba.
Ko abin tsoro ya zo ba za ka gani ba.
Dogarana Allah ban san tsoro ba.
Gunsa muke nema ba wani kato ba.
Ban san sharri ba, ban san tsoro ba.
4-Ina kira ka rika Allah nan daya,
Abin nufi ka yarda shi Ya yi samaniya,
Yai kasa yai gabas da yamma baki daya,
Yai Kudu yai Arewa ba wani sai Shi daya.
Yai mutane da aljanu a duniya.
A kai fari, a kai baki cikin duniya.
Mu dai mun gode ma Allah Ka iya.
Ka ba mu babban masoyin nan mai gaskiya,
Fiyayye khairul anbiya.
Ni din nan darajarsa nake ci ban boye ba.
Ban boye ba, ba zan boye ba.
Farar tafiya sa’a ban kasa ba.
(Ban san tsoro ba).
5-Na gane komai yau ya kare, tun da duniyar ta kare,
Ban san tsoro ba.
Wallahi ni dai yau na more, tun da ga gyada na bare.
(Ban san tsoro ba).
A rayuwar aure sai an jure, amarya daure, daure.
(Ban san tsoro ba).
Fage na zance kaina an tare, tun da Rabbana ya hore.
(Ban san tsoro ba).
Zan je na kai aike can Bunkure, Zahrah zo mu jera tare.
(Ban san tsoro ba).
(Takena shi ne ban san tsoro ba).
6-Rashi da samunsa ka yarda daga Allah ne.
Idan ka samu ba za a tankwafe ma ba.
Da nasara da rashinta daga Allah ne.
Ka sani cewa mutum ba zai yi komai ba.
Ka yarda cewa shi lokaci na Allah ne.
Da naka ya zo kai ma ba a ki kalla ba.
To ni kirana ka tuna da kai da Allah ne.
Kar ka shantake ka ce ba za ka kauce ba.
Ba zan ki fada ba, wata ran ba wata ran ba.
Ban san tsoro ba, ban san tsoro ba.
7-Ga ni ga ku nan mu je mu gani.
Ni dai na fada kun ji kun gani.
Ko na mutu ma na san kwa tuna da ni.
Ni dai aikina in fada in tuni.
In ka yi da ni Allah Yana gani.
Mai hakuri shi ke da magani.
A je a dama da sansani.
Zance jarina, ban san tsoro ba.
8-Duhun dare nake ni dai ban san tsoro ba.
Ko da a filin daga ba za na guje ba.
Ana daka ana kida ba zan ki waka ba.
Mata kar ku ce ban sa da ku a waka ba.
Mata adon gari ku ma ban kyale ba.
Mata ku tuna ku ake gani a yi duba.
Mata kar da ku yi dinki da bai tsari ba.
Kar da ku daye fata don bai dace ba.
Sa wa kanki cuci maza bai zama sunnah ba.
Sanyi hijabi ki gani ba kya ki kyawu ba.
Kun ga ban ji tsoro ba, tun da ban yi barna ba.