Yadda wanda ake zargi da fyade ya yi mutuwar fuju’a
Wani tsohon Kwamishinan Yada Labarai da ke fuskantar shari’a kan aikata fyade ya yanke jiki ya fadi matacce. Mutumin wanda tsohon mai taimaka wa Gwamna Ben Ayade na Jihar Kuro Roba ne, ya yanke jiki ya fadi ne a cikin motorsa a daren Talata, inda ya ce ga garinku. A shekarar 2019 ne aka zargi […]
Wani tsohon Kwamishinan Yada Labarai da ke fuskantar shari’a kan aikata fyade ya yanke jiki ya fadi matacce.
Mutumin wanda tsohon mai taimaka wa Gwamna Ben Ayade na Jihar Kuro Roba ne, ya yanke jiki ya fadi ne a cikin motorsa a daren Talata, inda ya ce ga garinku.
A shekarar 2019 ne aka zargi Edet Okon Asim da yi wa ‘yar aikinsa fyade, kuma shari’ar na gaban kotu.
Majiya mai karfi ta tabbatar da cewa Asim ya rasu ne a unguwar Eta Agbo da ke garin Kalaba, kafin daga baya aka kai gawarsa dakin ajiyar gawa a garin.