Yadda wani direba ya aika ‘yan bindiga lahira
Wani direban motar haya ya yi ta maza inda ya mutsuke wasu ‘yan bindiga tare da yin ajalinsu a kan hanyar Takum zuwa Wukari da ke jihar Taraba. Direban na tsaka da tuki ne a kan hanyar a karshen mako lokacin da ‘yan bindigar suka bullo daga cikin daji tare da umartarsa da ya tsaya. […]
Wani direban motar haya ya yi ta maza inda ya mutsuke wasu ‘yan bindiga tare da yin ajalinsu a kan hanyar Takum zuwa Wukari da ke jihar Taraba.
Direban na tsaka da tuki ne a kan hanyar a karshen mako lokacin da ‘yan bindigar suka bullo daga cikin daji tare da umartarsa da ya tsaya.
Wani ganau mai suna Malam Audu Bello wanda fasinja ne a cikin motar lokacin da lamarin ya faru ya shaida cewa kiris ya rage direban ya tsaya kafin daga bisani ya fahimci cewa masu garkuwa da mutane ne.
Malam Audu ya ce ko da direban ya tunkaro su sai ya rage gudu, wanda hakan ya alamta musu cewa tsayawa zai yi kafin daga bisani kuma ya dauki numfashinsu ya tsinke da gudu tare da mutsuke biyu daga cikin ‘yan bindigar da ke tsaye a tsakiyar hanya.
Kazalika, direban wanda bai so a bayyana sunansa ba ya ce lamarin ya faru ne tsakanin garuruwan Chanchangi da Abakwa wadanda da ma tuni suka yi kaurin suna a ‘yan kwanakin nan wajen garkuwa da mutane.
Ya ce ‘yan bindigar sun tilastawa direbobi da dama tsayawa tare da sace mutane domin neman kudin fansa a daidai wannan wurin.
Direban ya kuma ce da zuwansa Wukari bai yi wata-wata ba ya shaida wa jami’an tsaro inda suka bazama garin, ko da yake ya ce ba su samu gawarwakinsu ba lokacin da suka je.
Ya kuma ce alamar jini kawai suka iske lokacin da su a isa wajen.
Da aka tuntube shi, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta Taraba, David Misal ye ce zuwa yanzu rundunar ba ta kai ga samun rahoton lamarin ba.