Yadda wani matashi ya sha guba saboda ’yar fim
Dan a mutun jarumar ya kasa yin ido hudu da ita bayan ya yi mata takakkiya daga Yobe zuwa Kano.
Wani dan gani-kashenin jarumar fina-finan Hausa Maryam Yahaya, da ya tako daga Jihar Yobe zawa Kano domin ganinta ya sha fiya-fiya, saboda hakarsa ba ta cimma ruwa ba.
Matashin wanda ya yi takanas-ta-Kano daga Yobe ya yi yunkurin kashe kansa ne saboda takaicin rashin haduwa da jarumar da ya dade yana fatan yin ido hudu da ita.
Rahotanni sun ce tuni jami’an hukumar Hisba ta jihar kano suka garzaya da matsahin da ba kai ga tantance sunansa ba zuwa asibiti domin ceto rayuwarsa.
‘Abin da ya hana arumar ganawa da shi’
Da yake tabbatar da lamarin ga Aminiya, shugaban kungiyar jaruman fina-finan Hausa, Alhasan Kwalle ya ce matashin ya tsinci kansa ne a halin da yake ciki saboda kalubalen tsaron da ake fama da shi kuma ya zo ba tare da ya sanar da ita ba.
Alhassan Kwalle ya ce, “A labarin da na samu, Maryam ba ta san matashin ba, shi ma kawai a talbijin ya san ta. Ba su taba magana da ita cewa zai zo ba, kawai dai ya san Kano ce sansanin jaruman fina-finai ya kuma yi shahada ta taho.
“Da ya zo Kano bai ma san inda zai same ta ba, saboda haka kuma ka san yanayin tsaro, babu wani mai hankali da zai yarda kawai a ce wani ya zo daga wani wuri ganin sa kai tsaye ba tare da ya san da zuwansa ko manufarsa ba.
“A kan haka ne kowa ya ki yarda ya kai shi inda zai ga jarumar, shi ne ya yanke shawarar shan fiya-fiya don ya huce takaici ya kashe kansa.
“Amma cikin ikon Allah muka yi sauri muka kira jami’an hukumar Hizbah inda suka garzaya da shi asibiti.
“Daga bisani ne sai na kira Ali Nuhu kasancewar shi ne mai gidanta a masana’antar na shaida masa abin da ya faru inda ya aika mutane asibitin don su duba shi.
“Alhamdulillah yanzu an ce yana murmurewa kuma na tabbatar da zarar ya warke Hizbar za su mai da shi gida”, inji Alhassan.
To sai dai Aminiya ta gano cewa daga baya jaruma Maryam ta yanke shawarar bin Kamal har jiharsa ta Yobe, amma Alhassan Kwalle ya ce ba za ta sabu ba.
“Ni a karan kaina ban yarda da shawarar ba saboda za ta jawo wasu fassarorin daban-daban da za su iya zamar mata matsala.
“Ni ina ba da shawarar cewa tunda ya zo a kuskure kuma hakan ta faru kawai ya koma ya sake bin ka’ida har ya sami ganin nata”, inji Alhassan.
Ana ta ce-ce-ku-ce
Da yake tsokaci a kan lamarin, shugaban wata kungiya mai zaman kanta mai suna Islamic Thinkers in Northern Nigeria, Aliyu Dahiru Aliyu ya bayyana matakin da jarumar ta dauka a matsayin rashin kyautawa ga masoyin nata.
Aliyu wanda ya bayyana hakan a wani dandali mai suna ‘Kannywood a yau’ na kafar Facebook, ya ce, “Ya mutum zai yi tattaki tun daga Yobe ya zo ganin ki amma ki ki saurar sa? Wannan ai rashin sanin mutuncin masoyi ne. A ce saboda sonki har fiya-fiya bawan Allah ya sha amma ko a kula ta gagara?!
“Idan yanzu kin ga kina tashe to ki tambayi yau ina Safiya Musa? Ina Fati Muhammed? Ko Mansura Isah da ta auri Sani Danja ina take yanzu? Ban da ma tana ayyukan tallafi wa zai tuno da labarinta? Su Hadiza Kabara …Duk wadannan an so su fiye da ke.
“Shi masoyinka ai naka ne ko daga wani kauye yazo. Kin gan ni nan wallahi zan iya haduwa da Messi ko Ronaldo ya yi gaba na yi gaba don ba su dame ni ba. To bai kamata kuma idan kun shiga cikin jama’a ku rika wulakanta wadanda suke nuna kun isa ba”, inji Aliyu.
Wace ce Maryam Yahaya?
Ita dai Maryam Yahaya daya ce daga cikin matasan jarumai a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood da tauraruwarsu ke haskawa.
‘Yar kimanin shekaru 23, Maryam ta fara tashe ne a masana’antar bayan da ta fito a wani fim mai suna ‘Mansoor’ wanda Ali Nuhu ya ba da umarni a ciki.
Haifaffiyar unguwar Goron Dutse da ke Kano, jarumar ta yi karatunta na firmamare a unguwar Yelwa, sai sakandare a makarantar barikin sojoji ta Bukavu, kafin daga bisani ta tsunduma masana’antar, abin da ta dade tana burin yi.
Ta fara fita ne a wani fim mai suna ‘Gidan Abinci’ a matsayin karamar jaruma kafin daga bisani tauraruwarta ta haska bayan rawar da ta taka a fim din Mansoor.