Yadda wani mutum ya banka wa kansa da budurwarsa wuta
Wani mutum da ake zargin cacar baki ce ta hada shi da budurwarsa, ya cinnawa kansu wuta.
Wani mutum da ake zaton na da tabin hankali ya cinna wa kansa da budurwarsa wuta a titin Inikpi da ke unguwar High Level kusa da garin Makurdi a Jihar Binuwai.
Lamarin ya faru ne a yammacin Asabar bayan mutumin da ba a san sunansa ba har yanzu, ya zuba wa kansa da budurwar tasa fetur a wani daki da ya kulle sannan ya cinna wutar.
Ganau sun ce an ga mutumin mai kimanin shekara 40 a lokacin da ya je sayen fetur, amma makwabta suka yi tsammanin zai yi amfani da shi ne wajen kunna inji.
Bayan wani lokaci sai makwabta suka fahimci abin da ke faruwa, bayan ya kyasta wutar.
Wanda lamarin ya afku a kan idonsu sun ce agajin da hukumar kashe gobara ta jihar ta kawo shi ya hana wutar kama wasu gidajen.
Makwabtan mutumin sun yi zargin cewa yana da tabin hankali kuma rikici ne ya barke tsakaninsa da budurwar tasa kafin ya dauki matakin.
Aminiya ta rawaito mutumin ya mutu nan take, ita kuwa budurwar ta kone ta yadda ba a iya gane ta ba, kafin daga bisani jami’an hukumar kiyaye hadura (FRSC) reshen jihar, su dauke ta zuwa asibiti.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Binuwai, DSP Catherine Anene, ta ce wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya shaida wa runduwar cewa sun ga mutumin yana zuwa da man fetur kuma suka dauka cewa yana son amfani da shi ne.
Ta kara da cewa rashin sabani ne da ya faru tsakaninsu ya haifar da aika-aikar.
Anene ta kara da cewa, rundunar za ta ci gaba da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa lamarin.