Yadda wasu dalibai mata suka kubuta daga hannun ’yan Boko Haram I

Wadansu daga cikin dalibai mata da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram sun yi awon-gaba da su a makarantar sakandaren ’yan mata da ke garin Chibok na Jihar Barno sun bayyana yadda suka kubuta daga hannun wadanda suka sace su. Kakakin hedkwatar tsaro, Manjo-Janar Chris Olukolade, ya ce a shekaranjiya Laraba sojoji sun kubutar da […]

Yadda wasu dalibai mata suka kubuta daga hannun ’yan Boko Haram I

Wasu daga cikin ’yan matan da aka taba sacewaWadansu daga cikin dalibai mata da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram sun yi awon-gaba da su a makarantar sakandaren ’yan mata da ke garin Chibok na Jihar Barno sun bayyana yadda suka kubuta daga hannun wadanda suka sace su.

Kakakin hedkwatar tsaro, Manjo-Janar Chris Olukolade, ya ce a shekaranjiya Laraba sojoji sun kubutar da dalibai 107 daga cikin 129 da aka sace, ta yadda saura dalibai 8 ne ke tsare. Sannan an kama daya daga cikin wadanda suka kai hari a makarantar.

A daren ranar Talata ne dai, maharan da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari makarantar sakandaren ’yan mata da ke Chibok a Jihar Borno inda suka tafi da ’yan mata kusan su 200, wadanda ke rubuta jarabawar kammala karatun sakandare (WAEC). Maharan sun tasa keyarsu ne zuwa dajin Sambisa inda suke da sansani.

Wani jami’in rundunar tsaron ciki (SSS) ya bayyana cewa, “Mun gano wurin da motar tasu ta lalace kuma mutanenmu sun dunfari wurin da suke domin kamo ’yan bindigan, amma mun samu labarin cewa wadansu daga cikin ’yan matan sun sulale sun gudo gida.”

Haka kuma wani jami’i a karamar Hukumar Chibok din da ba ya so a ambaci sunansa, ya bayyana cewa, ’yan bindigar sun zo ne a cikin motocin a-kori-kura kirar

Hilud, amma sai suka kwace wata babbar motar daukar kaya da ke dauke da kayan abinci da za ta kai karamar Hukumar Askira-Uba suka sanya daliban a ciki suka yi gaba da su.

Jami’in ya ci gaba da cewa, a kan hanyarsu ce sai wadansu daliban suka yi karfin hali suka rike resunan bishiya lokacin da motar take wucewa cikin dare, suka makale har sai da motar ta yi nisa sannan suka diro suka dawo gari.

Ya kara da cewa, “Wadansu kuma sun diro ne daga cikin motar tun da ba gudu motar take yi sosai ba, saboda rairayin da ke hanyar. Mafi yawan ’yan matan sun shiga cikin daji ne suka dawo gida, amma har yanzu ba a ji duriyar sauran ba, amma mun samu labarin cewa shugaban karamar Hukumar Chibok  ya jagoranci wadansu jami’an tsaro sun bi sawun motar da ta dauki daliban.

Chibok dai gari ne na manoma da ke da nisan kilomita 130 daga Maiduguri, kuma ya hada iyaka da dajin Sambisa wurin da aka ce nan ne ’yan Boko Haram suka yi sansaninsu.

Wata yarinya da ta shaida wa sashen Hausa na BBC yadda al’amarin ya faru ta ce: “Sun dauke mu a kan Titin Damowa, amma sai daya daga cikin motocin da muke tafiya a cikinsu ta samu matsala, sai suka cinna mata wuta nan take. Mu kuma sai suka sanya mu a wata motar wadda take dauke da kayan abinci. Amma wadansu daga cikinmu sai bayan da suka tilasta mana ne muka shiga motar wadda ke dauke da jarkokin man-fetur, wadansu kuma sai suka sanya su a cikin wadansu motocin na daban. Daga nan ne kuma sai wadansu daga cikin maharan suka biyo sahunmu a kan babura a lokacin da muka kama wata hanyar mai cike da rairayi, wadda za ta isa dajin Sambisa.” Inji ta.

Yarinyar ta kara da cewa, “Bayan mun wuce kimanin kauyuka uku ne, sai kuma daya daga cikin motocin da muke tafiya da su ita ma ta mutu.  Daga nan sai wadansu daga cikin maharan suka koma wurinta, mu kuma muka ci gaba da tafiyarmu. Ganin abin da ke faruwa, sai wadansu daga cikinmu, wadanda ke kusa da tagar motar suka fita daga motar ta taga kuma suka nausa cikin daji. Mu ma sai muka bi sahunsu, mun zauna a cikin dajin har zuwa washegari da safe, sannan muka koma gida.” Inji ta.

Har ila yau, mahaifin daya daga cikin ’yan matan da a halin yanzu suke ci gaba da kasancewa a hannun maharan, ya bayyana cewa: “Ba zan iya bayyana damuwar da nake ciki ba, har birnin zuciyata na tabbata cewa ba zan damu ba, idan da a ce rasuwa ta yi.” Inji shi.

Mahaifin ya kuma shaida wa sashen Hausa na BBC cewa ’yan matan da maharan suka sace sun fi 300. Daga nan ne sai ya kara da cewa, “Dukkannin ’yan matan da ke shekarar karshe kuma suke rubuta jarrabawar kammala sakandare (WAEC) na hannun maharan, in ban da ’yan kalilan da suka tsere ta tagar motar da maharan suka sace su da ita. Saboda haka ne na bi hanyar da maharan suka nufa da su, inda kuma na yi kacibis da biyu daga cikin ’yan matan da suka kubuta.” Inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Daga bisani kuma na kara komawa hanyar, inda na isa wani kauye, amma sai mutanen kauyen suka gargade ni da kar na ci gaba da tafiya saboda an shaida musu cewa ’yan Boko Haram na kauyen da ke gaba kadan. Na tsaya da tafiya a nan, amma daga bisani sai na ci gaba, inda na iske wadansu motoci uku da aka kona kurumus. Daga nan ne sai na dauki dangana, na kama hanyar komawa gida. Ko da na isa gida, sai na samu mai dakina a sume, muka yayyafa mata ruwa ta farfado, amma har zuwa yanzu ba ta iya yin magana ba saboda firgici. Ni na rasa ma wane asibiti zan kai ta saboda irin kaduwar da na samu kaina a ciki”.

Wata mahaifiyar daya daga cikin ’yan matan da aka sace, ita ma ta bayyana yadda aka garzaya da ita asibiti bayan samun labarin batar ’yarta.

Wani mazaunin garin Chibok, inda aka sace ’yan matan, ya ce sun nemi jami’an tsaron da aka girke a garin, ko kasa, ko sama, a lokacin da maharan suka kai hari makarantar ’yan matan.

Mazaunin garin ya kuma  shaida wa sashen Hausa na muryar Amurka cewa, “Lallai ’yan Boko Haram sun ziyarci garin kuma sun tarkata duk ’yan matan da ke rubuta jarrabawar WAEC. Maharan sun sauke kayayyakin da ke cikin motocin da suka zo da su, sai suka sanya ’yan matan a ciki daga nan kuma sai suka wuce da su daji”.

Da aka tambaye shi ko da ma akwai wadansu jami’an tsaro a garin, sai ya ce, “Akwai su, amma a lokacin da suka samu labarin cewa ’yan Boko Haram sun zo, sai suka tsere”.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Barno Lawal Tanko ya tabbatar da faruwar al’amarin, amma ya ce ba zai ce komai ba tukuna, har sai tawagar ’yan sandan da ya tura garin sun dawo. 

Gwamnati za ta bayar da ladar Naira miliyan 50 ga wanda ya gano yaran

Daga Tijjani Usman Bello, a Maiduguri

Gwamnatin Jihar Borno za ta bayar da ladar Naira miliyan 50 ga duk mutumin da ya gano maboyar ’yan bindigan da suka yi garkuwa da dalibai matan da ke makarantar sakadare a Chibok ta jihar.

Gwamna Alhaji Kashim Shettima ne ya fadi haka a lokacin da ya kira taron manema labarai don bayyana musu halin da ake ciki a dangane da garkuwa da ’yan matan, a garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya kara da cewa, “Ko shakka babu gwamnati na cikin bakin ciki da damuwa game da sace wadannan dalibai, kuma za mu bi duk hanyoyin da suka dace wajen kwato wadannan yaran daga hannun wadannan azzaluman ’yan ta’adda. A yanzu haka kuma jami’an tsaro sun baza komarsu don gano maboyar wadannan mutanen a dajin nan na Sambisa domin kubutar da yaran, don haka gwamnati za ta bayar da ladar Naira miliyan 50 ga duk mutumin da ya gano maboyar ’yan bindigar tare da taimakawa wajen kubutar da yaran”.

Ya ce, “Bayan mun bude rijista domin gano yawan yaran da suka bace, mun gano cewa a yanzu haka dalibai 14  ne suka kubuta daga hannun maharan, wato guda 4 sun diro daga motar a yayin da aka sace su, sauran 10 kuma sun biyo ta daji ne suka dawo. Kuma iyayen yara 50 ne suka bayar da rahoton cewar yansu sun bata, wato suna cikin wadanda aka sace ke nan”.                              

Gwamnan ya kara da cewa, “A yanzu haka mun hada hannu da jami’an tsaro da Hakimai da malamai a yankin don gano yadda za a samu nasarar gano yaran, haka kuma k wamishinan ilimi, Alhaji Musa Inuwa Kubo zai fara tafiya can kafin ni ma in tafi, domin muna sa ran cewa za mu yi zaman dirshan har sai mun ga an sako su, ganin cewa a yanzu haka ba mu san halin da suke ciki ba, duk da cewa  yaran da suka kubuto sun shaida mana cewa an sanya su sun yi girke–girke ne, to amma muna tsoron kada su kashe su, ko kuma su yi musu fyade, don haka muna fata Allah Zai ba mu nasara”.

Jama’atu ta nuna damuwarta

Daga Muhammad Yaba, Kaduna

Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah wadai da sace wadansu ’yan mata dari biyu da ’yan bindiga suka yi a Jihar Borno a ranar Litinin.

A wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Kaduna, mai dauke da sanya hannun Babban Sakataren kungiyar, Sheikh Khalid Abubakar Aliyu, Jama’atu ta ce abin damuwa ne a ce duk da jami’an tsaro da ke  yankin, amma irin haka na faruwa.

Ta ce ta yaya za a ce duk da yawan kudaden da ake kashewa domin samar da tsaro a yankin amma kashe-kashe sai karuwa yake? “JNI ta yi Allah wadai da wannan aika-aika, muna kuma yin kira ga jami’an tsaro da su yi duk yadda za su iya domin kubutar da wadannan ’yan mata saboda su samu damar cigaba da karatunsu. Muna kuma jajanta wa malamansu da iyayensu da suka tsinci kansu cikin wannan damuwa, tare da fatan Allah Ya kawo karshen wannan matsaloli da ke addabar jama’armu.

“JNI na kuma kara yin kira ga al’ummar musulmi da su cigaba da yin  kunuti da sauran addu’o’i domin  Allah (SWT) Ya tona asirin masu aikata wadannan kashe-kashe a yankinmu na Arewa”.

kasar Amurka ma, ta bakin jakadanta a Najeriya James Entwistle, ta bukaci gwamnati ta tashi tsaye wajen ganin an gano wadannan dalibai mata, ba tare da bata lokaci ba.