Yadda wasu ‘kamfanonin waje’ ke koya wa matasan Najeriya damfara
Cikin kankanin lokaci ya tabbatar da cewa Kamfanin QNET ne ya damfari abokinsa.
Daga lasa masa zuma a baki cewa za a sama masa aiki da wani kamfanin kasar waje mai bayar da tallafi, kuma za a rika biyan sa Dala 225 a duk mako, sai Francis Essien ya sayar da motarsa da yake neman na abinci da ita, inda aka saya a wulakance kan Naira 450,000 domin ya biya Naira 530,000 da ake bukata a sama masa aikin, wanda abokinsa ne ya tallata masa.
Cikin sauri, ya kama hanya daga Kaduna zuwa Mowo, a Badagry da ke Jihar Legas a kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin inda ya shafe kusan kilomita 943, kuma yake tsammanin fara aiki da kamfanin kamar yadda abokin nasa ya yi masa alkawari.
Kusan wata biyu da barin aikinsa na tuki da kuma iyalinsa don nemo dukiya da zimmar samar musu da rayuwa mai kyau ta hanyar aiki da babban kamfani mai biya da daloli a Amurka, kwatsam sai Essien ya fara shiga cikin bakin ciki da da-na-sani da ya kasa boyewa.
Cikin kankanin lokaci ya tabbatar da cewa abokinsa wanda ya yi zargin cewa yana aiki da Kamfanin QNET ne ya damfare shi; kamfanin da aka ce masa ke aikin ba da tallafi ga mabukata, kuma suke biyan ma’aikatansu da daloli.
“Da aikin da kuma biyan Dalar Amurkan da aka ce za a yi duk mako, ashe duk zancen gizo da koki ne.
“Kuma abin takaicin shi ne abokin da na yarda da shi ne ya yi min haka,” in ji Essien.
Ya kara da cewa, Kamfanin QNET, ko Quest International Company da ma’aikatansu, sun ce za su dauke shi a matsayin ma’aikacinsu ne, inda ya ce sun bukaci ya fara zuwa “wajen horarwa” a Badagry, inda a cewarsa ya ga yadda ake koya wa matasa salon damfara ta hanyar jawo abokai da ’yan uwa ta hanyar ba su aiki.
Kamar yadda aka yi wa Essien, Haruna Suleiman, ya ce shi ma hakan aka yi masa ta kamfanin dai na Quest International Company.
Shi ma ya bar Minna a Jihar Neja zuwa Badagry, bayan surikinsa, Bilyaminu, ya tabbata masa cewa zai sama masa aiki a kamfanin inda ya hadu da Essien.
Bilyaminu ya bai wa Suleiman takardar shaidar samun aiki a matsayin wakilin kamfanin mai zaman kansa, wato Independent Representative, sai dai takardar ta nuna cewa sai Suleiman ya biya Dalar Amurka 1000 sannan zai fara aikin.
Da bai samu kudin da suka bukata ba, sai surikin nasa ya bar shi a gidan horon na Badagry ya kama gabansa.
Francis Essien da Suleiman mutum biyu ne kawai cikin daruruwan ’yan Najeriya da suka fada tarkon ’yan damfara ta hanyar sama masu aiki kamar yadda ma’aikatan kamfanin na Quest International suke yi.
A Najeriya, kididdigar marasa aikin yi ta kai kashi 33 kuma an yi kiyasin za ta kai kashi 41 kafin karshen shekarar 2023, kuma masana sun ce rashin kula da shige-da-fice ya sa ’yan damfara ke cin karensu ba babbaka da kuma samun nasararsu ta damfarar masu neman aiki.
Wannan salo da ma’aikatan Kamfanin QNET ko Quest International ke amfani da shi, Hukumar EFCC, ta ce ya yi daidai da harkar damfara ta Intanet, sannan ta kara da cewa sanin adadinsu na da wahala saboda yawansu.
Irin wadannan kamfanonin sun janyo wa Najeriya asarar biliyoyin Naira bayan sun damfari ’yan kasar nan.
Hukumar Kula da Hannun Jarin Bankuna (NDIC), a bara ta bayyana cewa, Najeriya ta yi asarar sama da Naira biliyan 900 ta hanyar kamfanonin ’yan damfara a cikin shekara 23.
Kamfanin QNET dai ya nisanta kansa da ma’aikatansa daga damfara ko yin abin da zai karya doka.
“Ina tabbatar maka cewa duk mutanen nan da suke amfani da sunan kamfaninmu suke ba jama’a aiki don a ba su kudi, ba ma’aikatanmu ba ne,” in ji Biram Fall, Shugaban Kamfanin Mai kula da Harkokin Nahiyar Afirka.
Mista Fall a tattaunawarsa da Aminiya ya ce sun san akwai bata-gari da ke amfani da sunan kamfanin.
Ya ce sun samu irin wannan mastala a kasar Ireland da shafukan sada zumunta, kuma abin na ci masu tuwo a kwarya.
Da aka tambaye shi game da gidan horarwar da ke Badagry, sai ya ce ba su da ofishi a Badagry.
Yadda ‘ma’aikatan QNET’ ke damfarar masu neman aiki
Haruna Suleiman da Francis Essien sun yi bayani iri daya; mutanen da suka sani kuma suka yarda da su ne masu aiki da kamfanin ne suka janyo su har Badagry.
Essien dai ya yarda da jawabin abokinsa, har ya biya Naira 230,000.
Biyan da ya yi ne ya ba shi damar zuwa wajen horon da ke Badagry, inda ya ce “Akwai sama da matasa 500 masu burin samun ‘horon’.”
“A lokacin da na fahimci harkar kawo mutane ne na tsarin yawan mutanen da ka kawo, yawan kudin da za ka samu, sai na tunkari abokina cewa me ya sa ya yi min karya?
“Sai ya ce wai haka tsarin aikin yake kuma ba a fada wa mutum duka bayanin har sai ya biya kudi.
“Sun fada min cewa zan fara samun kudi ne idan na kawo mutum biyu ta yadda aka kawo ni, kuma sai sun biya Naira 600,000.
“Su kuma mutanen da na kawo, kowanensu zai kawo mutum biyu kuma su biya irin kudin.
“Nan take na ki kuma na turje sai an biya ni kudina,” in ji shi.
Idan aka yi amfani da tsarin dalar gyada, ana sa ran idan mutum shida suka kawo Naira 600,000 in aka tara su za su kai Naira miliyan 3,600,000.
Idan ma’aikata 10 suka yi nasara, za su samu kudin da zai kai kimanin Naira miliyan 360,000,000.
Kuma ba shakka, wannan kudin zai bar Najeriya ba tare da biyan haraji a kansu ba.
Idan mutum ya hada mutum shida, Essien ya ce, a lokacin ne za a biya shi Dala 225 duk mako tare a la’adar Dala 50.
Shi ma Haruna Suleiman ya samu masauki a Badagry amma bai samu damar shiga dakin horon ba.
Shigar burtu zuwa wajen horo Domin fahimtar yadda ma’aikatan Kamfanin QNET ke aiki, wakilin Aminiya ya yi bad-da-kama, inda Suleiman ya hada shi da wata mai suna Bilkisu Zakari, wadda daya ce daga cikin ma’aikatan kamfanin.
Gaisawa ke da wuya, Bilkisu ta fara tambayar wakilin Aminiya aikin da yake yi.
Bayan ya fada mata cewa yana kasuwanci ne a Abuja, amma babu kasuwa, sai ta ce masa tana aiki da wani kamfanin kasar waje ne mai shigo da magungunan kara lafiyar jiki da kuzari da hadin gwiwar Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) da Kungiyar Manchester City ta Ingila.
Ta ce, kudin da zai biya, za a yi amfani da su ne wajen bude masa asusun ajiyar banki na kudaden kasashen waje da sama masa wajen zama da biya masa kudin motar zuwa aiki da yi masa bizar tafiya kasar waje.
Bayan kwanaki kadan, ta bukaci ya biya Naira 600,000, sannan ya tafi Badagry.
A nan wakilin Aminiya ya ce ya ga takardar shaidar daukar aiki daga kamfanin kafin ya biya kudin.
Sai Bilkisu ta aika masa da takardar shaidar daukar aiki, mai dauke da tambarin ‘Qi’ kuma aka rubuta ‘Quest International Company’ a sama.
Takardar sak irin wadda aka ba Suleiman ce, kuma kamar yadda Essein da Suleiman suka yi bayani, takardar ta nuna an dauke shi aiki kuma za a rika biyan sa Dalar Amurka 225, inda zai biya ladar Dala 50.
Amma sai ya biyan kudin kafin a ba shi horo na musamman.
Bilkisu ta shafe kwanaki tana damun wakilin Aminiya ya turo kudin. Da ta ga ya ki sauraren ta, sai ta goge takardar aikin da ta turo.
QNET: Kamfanin da ake tuhuma da laifuffaka daban-daban
A yayin tattara bayanai, Aminiya ta gano cewa, Qi group shi ne babban kamfanin da QNET wanda a da ake kira GoldQuest da ke karkashin Bijay Eswaran, wani dan kasuwa dan kasar Malesiya.
Bincike ya nuna cewa, ana tuhumar kamfanin da damfarar mutane kudade da kuma fitar da kudi ba bisa ka’ida ba a kasashen Iran, Indiya, Philippines da kuma wasu kasashen Afirka kamar Ghana.
A 1998 aka kirkiri kamfanin da suna GoldQuest kuma suna ba da sulallan zinare ne kawai a wannan lokaci.
Daga bisani sun canja sunan kamfanin zuwa QuestNet tare da kara bunkasa shi. A shekarar 2010 QuestNet ya koma QNET.
Mutane da dama sun ce, akwai alamar tambaya a kan yadda suke ta canja sunan kamfanin.
Sai dai kamfani ya kare kansa da cewa, canjin ya zo ne sakamakon bunkasar kasuwancinsu.
A kasar Indiya, wannan kamfanin ya yi kaurin suna domin kuwa ya haifar wa miliyoyin mutane mummunar matsalar tattalin arziki.
Wani rahoto da Cibiyar Binciken Kwakwaf ta kasar ta fitar ya ce, “Ayyukan kamfani babbar mastala ce ga kasar baki daya.”
A Afirka kuma, jami’an tsaro a kasar Ghana sun kama mutum takwas masu alaka da Kamfanin QNET.
A watan Janairun 2022, jami’an tsaro sun kama ma’aikatan Kamfanin QNET a Jihar Gombe, bisa zargin damfara da sa matasa sama da 100 cikin harkar a jihar karya doka .
Domin dakile ayyukan masu damfarar mutane ta hanyar fakewa da kamfanonin zuba jari da sauransu a Najeriya, ’yan Majalisar Wakilai sun bayyana kudirinsu na samar da dokar Zuba Jari da Tsare Dukiya ta 2023 (Investment and Security Bill 2023).
Idan an sa hannu a dokar, za ta dakatar da duka kamfanonin damfara da duk wani salon damfara na zamani a kasar nan.
Dokar za ta kuma ba da dama a daure duk wanda aka kama da hannu a harkar na tsawon shekera 10 ko sama da haka a gidan kaso.
Sai dai dokar kasa ba ta ba wa kowane kamfani damar fara harkokin kasuwanci ba tare da yin rajista ba, domin yin hakan na nufin kamfanin ba zai biya haraji ba.
“Ba zai yiwu ka biya haraji ba idan ba ka da cikakkiyar rajista,” in ji Umar Yakubu, masani a kan harkan tsaron kudi kuma Shugaban Fiscal Transparency and Integrity Watch.
Binciken Aminiya ya gano cewa, Qi group ba ya cikin jerin sunayen kamfanoni masu rajista a shafin Hukumar Kula da Kamfanoni (CAC).
Duk da cewa sunan QNET ya zama gama-gari a Benin, Fatakwal da Legas, inda ba a nuna cewa kamfani ne na harkokin saye da sayarwa ta hanyoyin zamani.
Biram Fall ya bayyana wa Aminiya cewa, QNET ya fara kasuwanci a Najeriya ne a watan Afrilun 2022 ta hanyar hadaka da wani kamfanin Najeriya mai suna Transblue Nigeria Limited.
Transblue Nigeria Limited ne mai kula da harkokin abokan hulda, safara da raba kayayyaki da kuma dafa wa QNET a ofisoshinsu da ke Abuja, Legas da Fatakwal.
Kamfanin Transblue na wani mai suna Abiodun Akeem Ajisafe ne kuma yana da rajista da CAC tun a 2021.
Amma kafin hadakarsu da Transblue, binciken Aminiya ya nuna cewa, sama da mutum 100 masu alaka da kamfanin da suka hada da ’yan Jamhuriyar Benin ne suka shiga hannun ’yan sanda a Jihar Gombe a watan Janairun bara.
Rahotanni sun ce, shugaban kamfanin mai kula da harkokin Afirka, Biram Fall ya karfafa wa wadanda aka kama gwiwa tare da cewa, Kamfanin QNET na iya kokarinsa wajen bin dokokin Najeriya da sauran inda suke aikinsu.
Sannan ya bukaci jami’an tsaro su yi aiki da gaskiya don gano inda matsalar take.
Da Aminiya ta tambaye shi dalilin da kamfanin ke harkokin kasuwanci ba tare da rajista ba, Fall ya musanta haka da cewa, “Ni dai ban taba mara wa wani mai laifi ba.”
Dalilin da ke jawo hakan — Masana
Masana kan harkokin kudi sun ce, kamfanonin damfara na yin binciken don bin diddigin yanayin ’yan kasa da kuma yin kididdigar marasa aikin yi.
“Sun fi mayar da hankali a kan kasashen da hanyoyin shigarsu ba ta tsauri sosai, ta yadda mutane za su shiga su ci karensu babu babbaka su fice.
“Kuma suna harin kasashe marasa karfi sosai, inda babu ayyukan yi kuma mutane na neman aiki ruwa a jallo,” in ji Umar Yakubu.
Ya ce, Hukumar CAC ta fitar da jerin sunayen kamfanonin da aka taba samun su da laifi a wasu kasashen kafin su shigo Najeriya.