Yadda wasu xalibai mata suka kuvuta daga hannun ’yan Boko Haram
axansu daga cikin xalibai mata da ake zargin ’yan qungiyar Boko Haram sun yi awon-gaba da su a makarantar sakandaren ’yan mata da ke garin Chibok na Jihar Barno sun bayyana yadda suka kuvuta daga hannun waxanda suka sace su. Kakakin hedkwatar tsaro, Manjo-Janar Chris Olukolade, ya ce a shekaranjiya Laraba sojoji sun kuvutar da […]
axansu daga cikin xalibai mata da ake zargin ’yan qungiyar Boko Haram sun yi awon-gaba da su a makarantar sakandaren ’yan mata da ke garin Chibok na Jihar Barno sun bayyana yadda suka kuvuta daga hannun waxanda suka sace su.
Kakakin hedkwatar tsaro, Manjo-Janar Chris Olukolade, ya ce a shekaranjiya Laraba sojoji sun kuvutar da xalibai 107 daga cikin 129 da aka sace, ta yadda saura xalibai 8 ne ke tsare. Sannan an kama xaya daga cikin waxanda suka kai hari a makarantar.
A daren ranar Talata ne dai, maharan da ake zargin ’yan qungiyar Boko Haram ne suka kai hari makarantar sakandaren ’yan mata da ke Chibok a Jihar Borno inda suka tafi da ’yan mata kusan su 200, waxanda ke rubuta jarabawar kammala karatun sakandare (WAEC). Maharan sun tasa qeyarsu ne zuwa dajin Sambisa inda suke da sansani.
Wani jami’in rundunar tsaron ciki (SSS) ya bayyana cewa, “Mun gano wurin da motar tasu ta lalace kuma mutanenmu sun dunfari wurin da suke domin kamo ’yan bindigan, amma mun samu labarin cewa waxansu daga cikin ’yan matan sun sulale sun gudo gida.”
Haka kuma wani jami’i a Qaramar Hukumar Chibok xin da ba ya so a ambaci sunansa, ya bayyana cewa, ’yan bindigar sun zo ne a cikin motocin a-kori-kura qirar
Hilux, amma sai suka qwace wata babbar motar xaukar kaya da ke xauke da kayan abinci da za ta kai Qaramar Hukumar Askira-Uba suka sanya xaliban a ciki suka yi gaba da su.
Jami’in ya ci gaba da cewa, a kan hanyarsu ce sai waxansu xaliban suka yi qarfin hali suka riqe resunan bishiya lokacin da motar take wucewa cikin dare, suka maqale har sai da motar ta yi nisa sannan suka diro suka dawo gari.
Ya qara da cewa, “Waxansu kuma sun diro ne daga cikin motar tun da ba gudu motar take yi sosai ba, saboda rairayin da ke hanyar. Mafi yawan ’yan matan sun shiga cikin daji ne suka dawo gida, amma har yanzu ba a ji xuriyar sauran ba, amma mun samu labarin cewa shugaban Qaramar Hukumar Chibok ya jagoranci waxansu jami’an tsaro sun bi sawun motar da ta xauki xaliban.
Chibok dai gari ne na manoma da ke da nisan kilomita 130 daga Maiduguri, kuma ya haxa iyaka da dajin Sambisa wurin da aka ce nan ne ’yan Boko Haram suka yi sansaninsu.
Wata yarinya da ta shaida wa sashen Hausa na BBC yadda al’amarin ya faru ta ce: “Sun xauke mu a kan Titin Damowa, amma sai xaya daga cikin motocin da muke tafiya a cikinsu ta samu matsala, sai suka cinna mata wuta nan take. Mu kuma sai suka sanya mu a wata motar wadda take xauke da kayan abinci. Amma waxansu daga cikinmu sai bayan da suka tilasta mana ne muka shiga motar wadda ke xauke da jarkokin man-fetur, waxansu kuma sai suka sanya su a cikin waxansu motocin na daban. Daga nan ne kuma sai waxansu daga cikin maharan suka biyo sahunmu a kan babura a lokacin da muka kama wata hanyar mai cike da rairayi, wadda za ta isa dajin Sambisa.” Inji ta.
Yarinyar ta qara da cewa, “Bayan mun wuce kimanin qauyuka uku ne, sai kuma xaya daga cikin motocin da muke tafiya da su ita ma ta mutu. Daga nan sai waxansu daga cikin maharan suka koma wurinta, mu kuma muka ci gaba da tafiyarmu. Ganin abin da ke faruwa, sai waxansu daga cikinmu, waxanda ke kusa da tagar motar suka fita daga motar ta taga kuma suka nausa cikin daji. Mu ma sai muka bi sahunsu, mun zauna a cikin dajin har zuwa washegari da safe, sannan muka koma gida.” Inji ta.
Har ila yau, mahaifin xaya daga cikin ’yan matan da a halin yanzu suke ci gaba da kasancewa a hannun maharan, ya bayyana cewa: “Ba zan iya bayyana damuwar da nake ciki ba, har birnin zuciyata na tabbata cewa ba zan damu ba, idan da a ce rasuwa ta yi.” Inji shi.
Mahaifin ya kuma shaida wa sashen Hausa na BBC cewa ’yan matan da maharan suka sace sun fi 300. Daga nan ne sai ya qara da cewa, “Dukkannin ’yan matan da ke shekarar qarshe kuma suke rubuta jarrabawar kammala sakandare (WAEC) na hannun maharan, in ban da ’yan qalilan da suka tsere ta tagar motar da maharan suka sace su da ita. Saboda haka ne na bi hanyar da maharan suka nufa da su, inda kuma na yi kacivis da biyu daga cikin ’yan matan da suka kuvuta.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Daga bisani kuma na qara komawa hanyar, inda na isa wani qauye, amma sai mutanen qauyen suka gargaxe ni da kar na ci gaba da tafiya saboda an shaida musu cewa ’yan Boko Haram na qauyen da ke gaba kaxan. Na tsaya da tafiya a nan, amma daga bisani sai na ci gaba, inda na iske waxansu motoci uku da aka qona qurumus. Daga nan ne sai na xauki dangana, na kama hanyar komawa gida. Ko da na isa gida, sai na samu mai xakina a sume, muka yayyafa mata ruwa ta farfaxo, amma har zuwa yanzu ba ta iya yin magana ba saboda firgici. Ni na rasa ma wane asibiti zan kai ta saboda irin kaxuwar da na samu kaina a ciki”.
Wata mahaifiyar xaya daga cikin ’yan matan da aka sace, ita ma ta bayyana yadda aka garzaya da ita asibiti bayan samun labarin vatar ’yarta.
Wani mazaunin garin Chibok, inda aka sace ’yan matan, ya ce sun nemi jami’an tsaron da aka girke a garin, ko qasa, ko sama, a lokacin da maharan suka kai hari makarantar ’yan matan.
Mazaunin garin ya kuma shaida wa sashen Hausa na muryar Amurka cewa, “Lallai ’yan Boko Haram sun ziyarci garin kuma sun tarkata duk ’yan matan da ke rubuta jarrabawar WAEC. Maharan sun sauke kayayyakin da ke cikin motocin da suka zo da su, sai suka sanya ’yan matan a ciki daga nan kuma sai suka wuce da su daji”.
Da aka tambaye shi ko da ma akwai waxansu jami’an tsaro a garin, sai ya ce, “Akwai su, amma a lokacin da suka samu labarin cewa ’yan Boko Haram sun zo, sai suka tsere”.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Barno Lawal Tanko ya tabbatar da faruwar al’amarin, amma ya ce ba zai ce komai ba tukuna, har sai tawagar ’yan sandan da ya tura garin sun dawo.
Gwamnati za ta bayar da ladar Naira miliyan 50 ga wanda ya gano yaran
Daga Tijjani Usman Bello, a Maiduguri
Gwamnatin Jihar Borno za ta bayar da ladar Naira miliyan 50 ga duk mutumin da ya gano mavoyar ’yan bindigan da suka yi garkuwa da xalibai matan da ke makarantar sakadare a Chibok ta jihar.
Gwamna Alhaji Kashim Shettima ne ya faxi haka a lokacin da ya kira taron manema labarai don bayyana musu halin da ake ciki a dangane da garkuwa da ’yan matan, a garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar.
Gwamnan ya qara da cewa, “Ko shakka babu gwamnati na cikin baqin ciki da damuwa game da sace waxannan xalibai, kuma za mu bi duk hanyoyin da suka dace wajen qwato waxannan yaran daga hannun waxannan azzaluman ’yan ta’adda. A yanzu haka kuma jami’an tsaro sun baza komarsu don gano mavoyar waxannan mutanen a dajin nan na Sambisa domin kuvutar da yaran, don haka gwamnati za ta bayar da ladar Naira miliyan 50 ga duk mutumin da ya gano mavoyar ’yan bindigar tare da taimakawa wajen kuvutar da yaran”.
Ya ce, “Bayan mun buxe rijista domin gano yawan yaran da suka vace, mun gano cewa a yanzu haka xalibai 14 ne suka kuvuta daga hannun maharan, wato guda 4 sun diro daga motar a yayin da aka sace su, sauran 10 kuma sun biyo ta daji ne suka dawo. Kuma iyayen yara 50 ne suka bayar da rahoton cewar yansu sun vata, wato suna cikin waxanda aka sace ke nan”.
Gwamnan ya qara da cewa, “A yanzu haka mun haxa hannu da jami’an tsaro da Hakimai da malamai a yankin don gano yadda za a samu nasarar gano yaran, haka kuma k wamishinan ilimi, Alhaji Musa Inuwa Kubo zai fara tafiya can kafin ni ma in tafi, domin muna sa ran cewa za mu yi zaman dirshan har sai mun ga an sako su, ganin cewa a yanzu haka ba mu san halin da suke ciki ba, duk da cewa yaran da suka kuvuto sun shaida mana cewa an sanya su sun yi girke–girke ne, to amma muna tsoron kada su kashe su, ko kuma su yi musu fyaxe, don haka muna fata Allah Zai ba mu nasara”.
Jama’atu ta nuna damuwarta
Daga Muhammad Yaba, Kaduna
Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah wadai da sace waxansu ’yan mata xari biyu da ’yan bindiga suka yi a Jihar Borno a ranar Litinin.
A wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Kaduna, mai xauke da sanya hannun Babban Sakataren Qungiyar, Sheikh Khalid Abubakar Aliyu, Jama’atu ta ce abin damuwa ne a ce duk da jami’an tsaro da ke yankin, amma irin haka na faruwa.
Ta ce ta yaya za a ce duk da yawan kuxaxen da ake kashewa domin samar da tsaro a yankin amma kashe-kashe sai qaruwa yake? “JNI ta yi Allah wadai da wannan aika-aika, muna kuma yin kira ga jami’an tsaro da su yi duk yadda za su iya domin kuvutar da waxannan ’yan mata saboda su samu damar cigaba da karatunsu. Muna kuma jajanta wa malamansu da iyayensu da suka tsinci kansu cikin wannan damuwa, tare da fatan Allah Ya kawo qarshen wannan matsaloli da ke addabar jama’armu.
“JNI na kuma qara yin kira ga al’ummar musulmi da su cigaba da yin qunuti da sauran addu’o’i domin Allah (SWT) Ya tona asirin masu aikata waxannan kashe-kashe a yankinmu na Arewa”.
Qasar Amurka ma, ta bakin jakadanta a Najeriya James Entwistle, ta buqaci gwamnati ta tashi tsaye wajen ganin an gano waxannan xalibai mata, ba tare da vata lokaci ba.