Yadda wasu ’yan biyu suka auri junansu cikin sirri
Ita kuwa ‘yar uwarsa ta kekashe da cewar ba za ta iya rabuwa da shi ba.
Wasu ’yan biyu mace da namiji sun auri junansu cikin sirri babu wanda ya sani har suka sami yara biyu sanadiyar auren da suka yi.
Amos da Juliana ’yan biyu ne da mahaifansu suka mutu suka bari su biyu sakamakon wani rikicin manoma da makiyaya da ya auku a garin Awe da ke Jihar Nasarawa.
- An gano likitan da yake zuba wa marasa lafiya maniyyinsa a mahaifa
- Dan Majalisa na cikin masu daukar nauyin IPOB —Buhari
Bayan mutuwar iyayen nasu ce a kauyen Doku da ke Karamar Hukumar Doman ta Jihar Nasarawa, ’yan biyun suka yi kaura zuwa kauyen Gumu inda suke zaune abinsu babu wanda ya sani.
Labarin wanda Jaridar The Nation ta wallafa ya fito fili ne bayan Amos ya nemi auren wata matar daban da ba shakikiyarsa ba, sakamakon dogon nazari da nadama da ya yi a kan kuskuren da suka tafka shi da ’yar uwarsa.
Sai dai ita kuwa Juliana ta kekashe da cewar ba ta ga aibu a abin da suka ba, kuma a cewarta ba za ta iya rabuwa da shi ba saboda ba ta taba sanin wani namiji ba bayansa.
Ta kara da cewa, ya yi alkawarin cewa zai zauna da ita a matsayin mata kuma ba zai kara aurar wata matar ba, amma kuma sai gashi yanzu ya zo da batun aurar wata daban.