Yadda wata budurwa ta yaudari kanta (1)
Masu bibiyar wannan shafi ina muku sallama irin ta addinin Musulunci, Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu. Kamar kullum a duk lokacin da na samu dama nakan yi rubutu ne a kan al’amurran da suka shafe mu, don ganin mun fadakantu da wa’azantuwa da kuma kokarin nemar wa kanmu mafita don mu dace a rayuwarmu ta duniya […]
Masu bibiyar wannan shafi ina muku sallama irin ta addinin Musulunci, Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu. Kamar kullum a duk lokacin da na samu dama nakan yi rubutu ne a kan al’amurran da suka shafe mu, don ganin mun fadakantu da wa’azantuwa da kuma kokarin nemar wa kanmu mafita don mu dace a rayuwarmu ta duniya da kuma ta lahira. Ba niyyata ba ne in muzanta ko yi wa wani ko wata ko wasu kazafi ko tozarta su ba, ina yin fadakawarce don mu gyara irin kura-kuran da muke yi don mu gudu tare sannan mu tsira tare. Kuma ina godiya ga yadda nake samun sakonninku ta waya walau ta hanyar kira ko aiko da sakonnin tes na yabawa a kan irin rubutun da nake yi, hakan na matukar kara karfafa mini gwiwar ci gaba da yin rubutu. Ga wadanda ma ba su aiko mini sako ko kira ba, su ma ina yaba musu.
A yau zan tabo wani batu ne mai muhimmanci da ke faruwa a tsakanin al’umma musamman matasa samari da ’yan mata. Wannan batu shi ne “Yaudara a tsakanin samari da ’yan mata”. Da farko dai ya kamata mu fahimci mene ne yaudara? Za mu iya fassara yaudara a kan wani nau’i na karya, inda zai kasance ka ga kamar an gina wani abu a kan gaskiya amma a zahiri abin ba haka yake ba, karya ce tsagwaronta. Sai dai masu yin haka suna da nasu dalilin da ya sa suke aikata haka amma ko a bangaren addini yaudara haramun ce.
Yaudara takan faru a kowane irin fanni na rayuwa, walau a bangaren kasuwanci ko na zamantakewa ko kuma na soyayya ga samari da kuma ’yan matan da ba su yi aure ba.
Dalilai da dama kan sa wasu samari da ’yan mata yin yaudara. A bangaren samari, da yawa daga ciki suna yin haka ne saboda a ganinsu idan suka fito fili suka bayyana wa yarinya ainihin kalarsu, ma’ana su talakawa ne, to irin wadannan ’yan mata ba za su saurare su ba, hasalima suna yin karya da yaudara ne don su mallaki matan ko ta wane irin hali. Hakan ke sa ka ga sun yi duk mai yiwuwa wajen rudar irin wadancan ’yan mata wajen aurensu ko yin lalata da su da makamancin haka. A bangaren matan kuwa, za ka iske mata da yawa suna yaudarar samari ne wajen karbe musu kudi ko sanya su yin wasu abubuwan da ba a son ransu ba, da niyyar za su aure su alhali suna da wadanda suke da niyyar aure a boye. Da zarar sun gama tatse irin wadancan samari sai ka tarar sun lallaba sun auri wadanda suke so, don haka ko da samarin da suka yaudara sun gano daga baya, babu yadda za su yi don a ganinsu wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa, don haka tilas samarin su hakura, ko suna so, ko ba sa so.
A kan haka ne nake so na bayar da wani labari a game da yadda wata yarinya garin neman yaudarar wani saurayi abhin abin ya kare a kanta, inda ta yaudari kanta ta koma tana cizon yatsa. Ga yadda labarin ya kasance:
Wani saurayi ne da bai taba yin aure ba, amma Allah Ya hore masa abin duniya. Sai dai kafin ya yi kudi ya sha wahala a rayuwa. Babu irin gwagwarmayar rayuwa da bai gani ba. Hasalima sai da ya hada da ayyukan karfi irin dakon kaya da tura baro da sauran sana’o’in karfi iri daban-daban a lokacin da yake neman ilimin addini da na boko kafin ya iya biyan kudin karatu tun da mahaifinsa ya rasu ne tun yana dan shekara 2. A wajen mahaifiyarsa ya taso, ita ma Allah Ya yi mata rasuwa a lokacin da yake dan shekara 5 da hakan ta sa ya taso a wajen kannuwar mahaifiyarsa. Ita ta rike shi har ya yi girma, kuma ta ba shi tarbiyya gwagwadon hali kamar dan da ta haifa.
To Allah da ikonSa wannan yaro bayan ya gama karatu sai ya samu aiki har ya kai ga samun babban mukami. Ya gina katafaren gida, ya sayi motoci na hawa da kuma wadanda ake nema masa kudi. Ya gina kamfanoni da dama inda ya samar wa matasa ayyukan yi. Sannan mutum ne mai matukar taimako. Hasalima irin alherin da ya yi wa mahaifiyarsa (kanwar mahaifiyarsa) da ta rike shi abin sai sam-barka. Hakan ce ta sanya mahaifiyarsa ta rika ba shi shawarar cewa a duk lokacin da ya tashi neman aure, to ya auri ’yar mutunci, wato ya auri yarinyar da ta fito daga gidan tarbiyya. Kuma ta hore shi da a duk lokacin da zai tafi zance wajen yarinyar da yake son ya aura, to kada ya nuna mata yana da kudi, ya tafi a matsayinsa na talaka wanda ba shi da komai, don hakan ne zai sa ya gane ko yarinyar tana son sa tsakani da Allah ko a’a. Ta ce ya bari sai bayan auren sai ya sanar da matarsa halin da yake ciki, wato Allah Ya yi masa arziki.
Za mu cigaba a mako mai zuwa insha Allah
Ahmed Garba Mohammed 08028797883