Yadda wata budurwa ta yaudari kanta (2)

Saboda da’a da kuma yi wa mahaifiyar da ta rike shi biyayya sai ya dauki shawarar da ta ba shi na cewa a duk lokacin da ya tashi yin aure to zai yi duk mai yiwuwa ya je wa yarinyar a matsayin shi talaka ne.  Hasalima ya yanke shawarar ba zai yi aure a unguwar […]

Yadda wata budurwa ta yaudari kanta (2)

Saboda da’a da kuma yi wa mahaifiyar da ta rike shi biyayya sai ya dauki shawarar da ta ba shi na cewa a duk lokacin da ya tashi yin aure to zai yi duk mai yiwuwa ya je wa yarinyar a matsayin shi talaka ne.  Hasalima ya yanke shawarar ba zai yi aure a unguwar da aka san shi ba.

Wata rana ya kai wa wani abokinsa ziyara a wata unguwa mai nisa inda ba a san shi ba.  Sai ya nemi wuri ya ajije motarsa tun da mota ba ta shiga unguwar saboda lungu ne.  Da ya je bai iske abokin ba, don haka a kan hanyarsa ta komawa wajen motarsa sai ya ci karo da wata kyakkyawar budurwa.  Tana tafe tana laste-latsen waya.  Budurwar ta burge shi saboda kyauwunta da kuma irin kirar da Allah Ya yi mata.  Har ya wuce sai ya koma ya yi wa budurwar sallama, ita kuma ta amsa masa a ciki-ciki da hakan ya nuna ba ta gamsu da shi ba.    Riga da wando ya sanya ba masu tsada ba.  A lokacin ma yana sanye ne da silifas da wata karamar wayar hannu wacce ba ta wuce Naira dubu 2 da 500 ba.  

Da ya kara yi wa yarinyar magana ne sai ta sake kallonsa sama da kasa, wani irin kallo na wulakanci, sannan ta amsa masa da cewa “Malam, lafiya kuwa kake ta bi na?”  Sai ya amsa mata da cewa yana so ne ya san sunanta sannan inda hali ta ba shi adireshin gidansu da kuma lambar wayarta, don ya same ta a can don su tattauna, saboda ya ganta ne kuma ta kwanta masa a rai.  Ta sake kallonsa sannan ta ce a gaskiya ita ba za ta fada masa sunanta ba, tun da shi bai kai ajin ma da za ta kula shi ba, ma’ana tun da bai da kudi, ita kuwa a gaskiya ba ta harka da wanda bai da kudi. Da ya yi mata raha cewa to ya aka yi ta gane cewa shi ba mai kudi ba ne?  Nan take ta yi masa kallon biyu-ahu (sama da kasa) ta ce in kai mai kudi ne ai da ya nuna a irin kayan da kuma wayar da kake rike da ita.  Ai masu kudi ba sa buya duk inda aka gansu za a iya gane su.  Nan ya yi dariya a  zuciyarsa yana fadin “yarinya kin yi kuskure da kin san ni kowane ne da ba ki fadi haka ba”.  

Bayan ya nace sai ta ce sunanta Halima (sunan karya) sannan ta ba shi wata lambar waya (ta karya).  Shi kuma ya karba ya ce insha Allah nan gaba kadan zai neme ta a waya, ya juya ya kama gabansa, ita ma ta kama gabanta tana wadansu ’yan surutai da ke nuna ya bata mata lokaci ne kawai. 

Bayan sun rabu da budurwar sai ya labe sai da ya tabbatar ba ta hangensa sai ya lallaba ya je wajen dankareriyar motarsa ya shiga ya bar unguwar cikin sauri, don bai son budurwar ta hango shi har ta gane cewa a mota yake.

To ashe a lokacin da ta ba shi lambar wayar ta yi kuskuren ba shi lambar wata kawarta ce da suke kud-da-kud ba tare da saninta ba.  Shi kuwa bayan kwana biyu sai ya kira lambar sai ya ji wata murya inda ya nemi adireshi ita kuma ta yi masa kwatance cikin lumana da farin ciki.  Wannan abu ya ba saurayin mamaki, amma duk da haka ya nufi inda aka yi masa kwatancen.

Ya ajiye motarsa ce a gida inda ya hau babur din haya (acaba), kuma aka sauke shi kusa da gidan.  Yana isa ya daga waya ya kira yarinyar da suka yi magana a waya.  Fitowarta sai ya lura lallai ba Halima (yarinyar da suka hadu kwanakin baya ba ce).  Hasalima ya lura wannan za ta fi kamun kai da kuma mutunci, don irin tarbar da ta yi masa ya tabbatar ba waccan ba ce.  Ya gabatar da kansa a wajen wannan budurwa inda ta shaida masa sunanta A’isha kuma ba ta dade da kammala karatun sakandare ba, yanzu tana fata idan ta samu miji ta yi aure in kuma hakan bai yiwu ba za ta ci gaba da yin karatu ne.  Ta tambaye shi yadda aka yi ya samu lambar wayarta.  Bai boye mata ba, ya shaida mata cewa wata buduwa ce suka hadu a hanya ya nemi ta ba shi lambar wayarta shi ne ta ba shi wannan lamba, ashe ba ainihin lambarta ba ne.  A’isha ta yi mamakin yadda aka yi waccan budurwa ta yaudare shi wajen ba shi lambar karya maimakon ta fada masa gaskiya cewa ba ta son sa.

Bayan sun gaisa sai ya shaida mata sunansa da kuma unguwar da ya fito, kuma ya ce insha Allah idan sun daidaita yana da sha’awar ya aureta.  Sai dai ya nuna mata shi ba mai kudi ba ne, amma dai yana da rufin asiri daidai gwargwado. Nan take A’isha ta ce ta amince kuma ta nuna masa ai arziki nufin Allah ne, don haka kada ya damu kansa da shi mai kudi ne ko talaka kafin ya nemi yardar aurenta.  Ta yi addu’ar Allah dai Ya zaba musu mafi alheri.

  Tafiya ta yi nisa har ya gana da iyayenta kuma suka amince masa da ya nemi auren A’isha saboda sun fahimci mutum ne mai mutunci da sanin yakamata.  Suka nemi ya gabatar da mabukatansa, inda ya shaida wa mahaifiyarsa (kannuwar mamansa) wacce ta rike shi inda ta yi murna da abin da ta ji ya yi.  Nan take suka hada kai da makwabtansu suka aika su zuwa gidansu A’isha da niyyar a sanya ranar bikin aure.  Haka kuwa aka yi.  Tafiya ta yi nisa amma iyayen A’isha da ita kanta A’isha ba su gano cewa Abdullahi mai kudi ba ne. Sun dauke shi ne a matsayin talaka mai mutunci kuma sun gamsu da shi da kuma gidan da ya fito.

 A lokacin bikin ne sai kawar amarya (Halima) ta halarci bikin.  Halima dai ita ce budurwar da ya fara cin karo da ita tun da farko ta yi masa wulakanci sannan saboda yaudara ta ba shi lambar wayar kawarta ba tare da saninta ba.

Bayan an yi biki an kare ango ya tare da amaryarsa a wani daki ciki da falo a wata unguwa sai ya yanke shawarar shaidawa matarsa cewa shi fa  mai kudi ne, kuma hasalima ya yi mata haka ne don ya gwada don ya gano ko tana son sa tsakani da Allah ne ko a’a.  Nan take amarya abin ya ba ta mamaki sannan ta yi farin ciki da cin jarrabawar da ya yi mata tun da farko don da ma ba don kudinsa ta aure shi ba, ta aure shi ne saboda Allah.

Za mu ci gaba insha Allah

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883