Yadda wata budurwa ta yaudari kanta (3)
A yau na kawo karshen wannan labari da muka shafe kimanin makwanni uku ana buga shi a wannan shafi. Jama’a da dama sun kira ko aiko da sakonnin tes inda suka yaba da wannan labari. Fatarmu dai shi ne a yi amfani da darasin da aka koya a wannan labari. Ga karshen labarin kamar haka: […]
A yau na kawo karshen wannan labari da muka shafe kimanin makwanni uku ana buga shi a wannan shafi. Jama’a da dama sun kira ko aiko da sakonnin tes inda suka yaba da wannan labari. Fatarmu dai shi ne a yi amfani da darasin da aka koya a wannan labari. Ga karshen labarin kamar haka:
Ba a dade ba ya koma da amaryarsa katafaren gidan da ya gina kafin auren. Sannan ya saya wa amaryar dankareriyar mota kuma ya biya mata kudin aikin Hajji. Ba a dade ba ya saya wa iyayen matarsa yalwataccen gida, tun da dama haya suke yi. Baya ga haka ya biya musu kudin sauke farali wato Hajji. Wannan abu da angon ya yi ya ba iyayen amarya matukar mamaki da farin ciki kuma suka yi wa Allah godiya. Duk labarin abin da wannan bawan Allah ya yi ya baza gari, aka yi ta shi masa albarka ana yi masa fatan alheri.
A kan haka ne labari ya iske (Halima) cewa kawarta A’isha da suka yi bikinta kwanakin baya, mijinta ya yi arziki, don ya sai mata mota kuma ya biya mata kudin zuwa Hajji. A lokacin bikin ba su yi ido biyu da angon ba, don haka ba ta san angon kawarta A’isha ba, kuma ko ta ganshi ma ba ta gane shi ba.
Isar Halima ke da wuya sai ta cika da mamakin irin katafaren gidan da kawarta amarya ke ciki. Sai ta rika fadi a ranta “ina ma a ce mijina ne ya mallaki irin wannan katafaren gida?”.
Ta yi sallama, kawarta amarya (A’isha) ta tarbe ta da hannu bibbiyu. Suka dade suna hira kuma ta shaida mata yadda ta hadu da mijinta tun da farko da kuma irin yadda ya nuna mata cewa shi talaka ne alhaki mai kudi ne tun da farko. Ta ce ya yi mata haka ne don ya gwada ya ga ko tana son sa tsakaninta da Allah. Abin ya ba Halima mamaki da ta ji yadda angon kawarta ya fito mata, yau ga shi ta auri katafaren mai kudi irin wanda take mafarkin ta aura.
Halima ta yi mamakin yadda hakan ya faru, kuma ta yi mata addu’ar fatan alheri. Nan amarya ta ce bari ta kira mijinta (Abdullahi) don su gaisa, don ita ma ta yi masa godiya a matsayinta na kawarta.
Ango Abdullahi ya iske matarsa A’isha da Halima a falo, inda ya yi musu sallama. Zamansa ke da wuya sai ya hada ido da Halima nan take gabansa ya fadi. Ya kalle ta da kyau, sai ya gane cewa lallai ita ce yarinyar da ta wulakanta shi har ta ba shi lambar wayar karya da ya yi sanadiyyar auren amaryarsa ta yanzu.
Halima na kallonsa sai gabanta ya fadi, ta gane cewa shi ne saurayin da ta wulakanta a wancan lokaci. Nan fa idonta ya raina fata.
Abdullahi ya tambaya ta ko ta gane shi? Sai ta kada kai ta ce lallai ta gane shi. Nan take ya shaida wa amaryarsa A’isha ai wannan ita ce yarinyar da na taba ba ki labari wacce ta ba ni adireshi da kuma lambar karya.
Nan fa idon Zainab (Halima) ya raina fata, don burinta a rayuwa shi ne ta auri mai kudi sai ga shi ta yi wa kanta sakiyar da babu ruwa. Nan take ta yi nadama a kan abin da ta aikata shi kuma Abdullahi ya yi mata nasiha. Kafin ta bar gidan ya yi mata kyauta mai yawa sannan ya sa direbansa ya kai ta har gida.
A karshe Zainab (Halima) ta auri wani talaka ne don ta dade a gida ba ta samu irin mijin da take son ta aura ba, wato mai kudi. Ta gane kurenta inda hakan ya zame mata ishara don a kokarin yaudararar wani sai ta kare da yaudarar kanta! Don haka jama’a sai mu yi hattara. Ina fata wannan labari zai zama darasi a garemu baki daya.
Za a iya tuntubar Ahmed Garba Mohammed a 08028797883