Yadda wata hatsabibiyar gobara ta addabi mutanen Soro

Kimanin kusan wata daya ke nan da mutanen garin Soro da ke yankin karamar Hukumar Ganjuwa a Jihar Bauchi suka samu kansu a cikin mawuyacin hali a sakamakon wata hatsabibiyar gobara da ta addabe su, inda ta lashe daruruwan gidaje a cikin garin. Wakilinmu ya yi tattaki zuwa garin inda ya tattauna da wadansu daga […]

Yadda wata hatsabibiyar gobara ta addabi mutanen Soro

Kimanin kusan wata daya ke nan da mutanen garin Soro da ke yankin karamar Hukumar Ganjuwa a Jihar Bauchi suka samu kansu a cikin mawuyacin hali a sakamakon wata hatsabibiyar gobara da ta addabe su, inda ta lashe daruruwan gidaje a cikin garin.

Wakilinmu ya yi tattaki zuwa garin inda ya tattauna da wadansu daga cikin wadanda gobarar ta lashe musu gidaje tare da kayayyakin amfanin yau da kullum.
Adamu Usman daya daga cikin mazauna garin Soro ne kuma yana daya daga cikin wadanda gobara ta lashe musu gidaje a wannan gari, ya bayyana wa Aminiya cewa, “cikin ’yan kwanakin nan muna fama da wata matsala ta annobar gobara wacce haka kawai sai ka ga daki ya kama da wuta. Misali, ni yanzu haka a cikin gidana wutar ta kona mini daki daya babu abin da aka dauka a cikin dakin, muna fatan Allah Ya kawo mana karshen wannan masifa.”
“Na yi asarar dukiya ta sama da Naira dubu ashirin, kuma har zuwa wannan lokaci da muke zantawa da kai babu wani gudunmawa da muka samu daga wajen hukumomi, amma kwanaki mun ji cewa gwamnatin tarayya tana shirin kawo mana gudunmawa. Babban abin da muke bukata a halin yanzu shi ne gudunmawa na kwanon rufi, domin mun kusa shiga hunturu.”
Da Aminiya ta tuntubi Auwalu S. Yakubu, wanda shi ne Sarkin Soro ya wakilta ya yi magana a madadinsa sai ya ce, “Kusan kullum sai wutar ta kona gidaje, muna ci gaba da yin addu’o’i Allah Ya kawo mana karshen wannan masifa. Hakika akwai sama da gidaje dari 200 da suka kone kurmus sakamakon wutar. Babu wanda ya rasa ransa, sai dai akwai dabbobi da dama da suka mutu. Mun rubuta takarda ga karamar hukuma game da batun kuma muna fata za ta cigaba da kawo mana gudunmawa domin tallafa wa wadanda annobar ta shafa.”
Ya kara da cewa, “An yi asarar sama da Naira miliyan 10 a cikin wannan gari na Soro sakamakon wannan annoba ta gobara.”
Malam Muhammadu Al-Mustapha shi ne babban limamin garin Soro, ya bayyana wa Aminiya cewa, ‘’Na yi asarar dukiya ta sama da Naira dubu dari biyu a cikin gidana sakamakon wutar, Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Bauchi (SEMA)ta kawo dauki kwanakin baya kuma ina daya daga cikin ‘yan kwamitin raba kayayyakin agajin. Daga cikin kayayakin da hukumar ta kawo akwai buhunan masara da bargo da kwanon rufi da tabarmi da shinkafa da turaman shadda da zannuwa na mata da siminti da makamantansu.’’
Limamin ya bayyana cewa, da yawa daga cikin wadanda gobarar ta lashe musu dakuna suna zauna ne a gidajen ‘yan uwansu, wadansu kuma sun bar garin sun koma wajen ‘yan uwansu a wadansu garurruwan.
Malam Muhammadu ya yi nuni da cewa, ‘’tabbas a wannan gari na Soro kwanaki mun fuskanci hare-hare na ‘yan bindiga, amma a halin yanzu muna zaune lafiya babu wata matasala, sai annobar gobarar da ta addabe mu.’’
Malam muhammadu Habibullahi, shi ma gobarar ta lashe masa dakuna biyar, ya bayyana cewa, ‘’kamar yadda muka gudanar da bincike, haka kawai ana zaune sai ka ga wuta ta tashi a cikin daki. A cikin gidana akwai dakuna biyar da suka kone kurmus, kuma akwai sama da mutum 30 da suke cin abinci a wannan gida, akwai kanina wanda dakunansa guda bakwai ne suka kone kurmus, mun rasa mene ne yake haddasa wannan wuta.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘’Gidajen da suka kone sun haura dari biyu, kusan kullum sai ka ji gobatar ta sake tashi, akwai masu yada jita-jitar cewa wai mutane suna gudu daga garin Soro saboda annobar gobara. Wannan labarin ba gaskiya ba ne dukkan wadanda gidajensu suka kone babu mutum daya da ya fice daga garin Soro, a iya binciken da muka gudanar.’’
‘’A cikin gidana wutar ta tashi sama da sau hudu, yanzu haka da muke magana da kai mai dakina ba ta nan gidan saboda wutar ta cinye dakinta da kayayyakin da ke ciki, Naira dubu dari biyu ba zai iya gyara abubuwan da muka yi asara ba.’’
‘’Akwai masu cewa watakila aljanu ne suke haddasa wannan gobara, to babban limamin garin Soro ma wutar ta tashi a gidansa sama da sau 12 ana kashewa. A rana daya akan samu sama da gida hamsin wanda wutar ke addabarsu. Tunda muke bamu taba ganin masifa a nan garin ba sai a wannan karon . Ba ma zargin kowa da haddasa wannan gobara, kuma za mu cigaba da yin addu’o’i Allah Ya kawo mana karshen wannan masifa.’’