Yadda wata kabila a Kamaru ke gudanar da bikin mutuwa
Ya danganta da yadda iyalan mamaci suke bin koyarwar addini ko kuma irin tanade-tanaden da al’adun gargajiya wajen gunadar da bukukuwa idan mutum ya mutu. Dalili da wannan ya sa kabilar ‘Garfawa’ wanda wasu ke kira ‘Yahundawa’ da ke kasar Kamaru, bisa al’ada, suke gudanar da gagarumin biki a kowane lokacin da daya daga cikinsu […]
Ya danganta da yadda iyalan mamaci suke bin koyarwar addini ko kuma irin tanade-tanaden da al’adun gargajiya wajen gunadar da bukukuwa idan mutum ya mutu. Dalili da wannan ya sa kabilar ‘Garfawa’ wanda wasu ke kira ‘Yahundawa’ da ke kasar Kamaru, bisa al’ada, suke gudanar da gagarumin biki a kowane lokacin da daya daga cikinsu ya rasu.
Da farko dai, ba’a gaggawar binne mamacin. Ana kai gawar ne asibiti inda za a adanata a kankara, daga bisani kuma dangi su dawo gida don yin shawara da tattaunawa kan yadda za su tafiyar da shagulgular bikin binneta. Ma’ana za su tsaida wa’adin da gawar za ta yi a cikin sanyi, irin shirin da za a yi wurin tafiya daukota, da kuma tsare-tsaren da za a yi don kwanan keso wanda zai ba da damar yin addu’o’i gabanin binneta. Sa’annan kuma har idan wanda ya mutu mai hannu da shuni ne, ana jinkirta komai har sai duk ‘ya’yansa da kuma wasu makusantarsa da suke nesa sun komo gida domin a yi bikin da su.
Irin kudin da za a kashe wurin yi wa jama’a hidima a wurin makokin ba zai lissafu ba. Saboda ana sayan gawar a akwatin kasaita da kuma sayan sauran abubuwa don ganin an suturata wanda hakan ke lashe makudan kudi, ban da kayan abinci da za a saya da kuma na abin sha kamar su barasa da dai sauransu. Duk ana yin wannan ne don karrama wanda aka rasa. Sannan kuma akwai taimakon kudi da ake karba daga ’yan uwa da abokan arziki don ganin an fitar da iyalansa kunya.
Idan akai rashin sa’a mamacin ya bar mata. Mai dakin tasa kan kasance cikin wani hali na kaskanci. Da fari dai ana aske wa matar suma da ke kanta baki daya, sannan ba a barin ta sanya takalmi a kafa, ba ta kuma kwanciya a kan katifa, ko tabarma sai dai a kan dabe. Sai kuma hana ta wanke hannayenta gabanin cin abinci.
Daga wannan ne kuma sai a nufi bakin rafi da ita da misalin karfe 12:00 na dare don a yi mata wankan shiga takaba. Sai kuma a tambayeta dalilin da ya sa mijinta ya mutu. Idan kuma aka yi dace marigayin mai hannu da shuni ne, za a tambayeta inda ma’ajiyarsa take da kuma bayanai kan kaddarorin da ya mallaka. Sannan kuma a tunatar da ita cewa ba mutum daya da za ta iya aura face daga danginsa. Ma’ana bayan ta kammala wa’adin da aka deba mata na yin takaba, ba za ta iya sake auran kowa ba sai dai daga cikin ’yan uwan mijinta da ya rasu. Wanda ta aura ne kuma zai gaji kaddarorin da ya bari da da kuma ’ya’yan da mamacin ya bari.
Akwai dalilai da dama da suke sa mutane bin irin wadannan al’adun wanda suka hada da yin imani da al’adun iyaye da kakanni. Na biyu kuma, shi ne yadda ake tsorata matar da mamacin ya bari da cewa idan har ba su amince da tanade-tanaden da al’adar gargajiya ta shumfida, to za ta wayi gari dukkannin jikinsu a kumbure. Wanda hakan kuma ka iya kaiwa ga rasa rayuwarsu. Na uku kuma shi ne barazanar cewa la’antar magabata na iya fada masu, ko kuma cewa za ta iya asarar ’ya’yanta gaba daya. Dalili da wannan ne kan sa matan ke ba da kai bori ya hau.
Sai dai takwarorinsu maza ba sa fuskantar irin wannan kaskancin idan matansu na aure suka mutu. Abin da ke faruwa shi ne, idan miji ya rasa mai dakinsa wanda ke dauke da juna-biyu. Ana tilasta masa zuwa rafi don yin wanka, kuma ya yi kwana biyu a wani gari na daban wanda ba garinsu ba.
Abin damuwa dai shi ne, har yanzu ba wata doka a kasar da ta haramta wadannan al’adun saboda dari-darin da gwamnati ke yi na kutse ga al’adun gargajiyan kasar. Amma kuma kungiyoyin kare hakkin mata na ta kokarin ganin gwamnati ta dauki matakan da suka dace don kare mata daga wadannan al’adun.