Yadda wata mata ta kamu da cutar rashin jin muryar maza sai dai jinsinta

Wata mata me suna Chen `yar birnin Diamen, da ke shiyyar Gabas ta kasar China ta kamu da cutar al`ajabi a kunnuwanta ta yadda ta ke zama kurma idan har maza suka yi magana da ita, ba ta iya jin muryarsu gaba ki daya. An dai gano wannan cutar ne bayan da likitoci suka yi […]

Yadda wata mata ta kamu da cutar rashin jin muryar maza sai dai jinsinta

Wata mata me suna Chen `yar birnin Diamen, da ke shiyyar Gabas ta kasar China ta kamu da cutar al`ajabi a kunnuwanta ta yadda ta ke zama kurma idan har maza suka yi magana da ita, ba ta iya jin muryarsu gaba ki daya. An dai gano wannan cutar ne bayan da likitoci suka yi bincike akan abin da ke damunta a kunne.

Chen ta ce, a lokacin da ta fara wannan rashin lafiyan ta na jin wani irin kara kamar kararrawa a kunnenta da daddare kafin ta kwanta barci, a wannan lokacin sai ta fara neman agajin larurar da ke damunta.

Bayan gari ya waye da safe sai ta razana saboda ta ka-sa jin muryar saurayinta lokacin da yake magana da ita.

Chen ta je asibitin Kianpu da ke birnin Diamen, Gabashin China, saboda tana jin muryar `yar uwarta likita sosai. Wata kwararriyar likitan kunne, hanci da makogoro mai suna Lin Diaoking ta ce, Chen na iya jin muryata idan na yi magana da ita, amma idan mara lafiya namiji ya shigo dakin ya yi magana ba ta jin muryarsa gaba ki daya.

A binciken Dakta Lin akan larurar rashin jin muryar jinsin maza da Chen ba ta yi, ta gano cewa akwai matsalar saurin daukar sauti da kuma halittar da take baiwa kwakwalwa sakon jin sauti ba ta aiki. Yayin da kuwa Chen ta ce, a yanzu tana aiki a kurarran lokaci wanda hakan yake wahalar da jikinta da rashin samun isashshen barci.

A cewar Dakta Lin ta ce, wahalar da jikin da Chen ke yi ne ya haifar mata da yanayin da take ciki a yanzu, wanda ya haddasa rashin jin sautin sai dai kawai idan sautin mai karfi ne zata iya ji, wannan sautin kuma sai dai idan ya kasance na jinsin mace ne kawai. Likitoci sun bayar da shawarar cewa, ya nada muhimmanci a magance wannan larurar da sauri kuma suna fatan Chen zata warke nan gaba kadan.

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas