Yadda wata mata ta sace jaririn kwana 10 ta sake masa suna
Kimanin kwanaki goma da haihuwarsa, aka sace jariri Abdulshakur. Ana zargin wata mata mai suna Hajiya Lanti danfulani da laifin sace yaron a kauyen Maitangadi da ke karamar Hukumar Soba a Jihar Kaduna.Hajiya Lanti ta je kauyen ne a matsayin mai bayar da maganin gargajiya kafin ta sace jaririn, ta koma Saminaka da ke karamar […]

Kimanin kwanaki goma da haihuwarsa, aka sace jariri Abdulshakur. Ana zargin wata mata mai suna Hajiya Lanti danfulani da laifin sace yaron a kauyen Maitangadi da ke karamar Hukumar Soba a Jihar Kaduna.
Hajiya Lanti ta je kauyen ne a matsayin mai bayar da maganin gargajiya kafin ta sace jaririn, ta koma Saminaka da ke karamar Hukumar Lere, a inda ta canja masa sifa, sannan ta sanya masa sunan Hasan.
Hasana Badamasi, ainihin mahaifiyar yaron, ta fada wa Aminiya cewa Abdulshakur shi ne danta na takwas, kuma an sace shi a ranar 7 ga watan Mayu, 2013, aka gane shi a Saminaka, bayan watanni uku da bacewarsa.
A Saminaka, Hajiya Lanti, wadda ta dade da barin gidan mijinta, abin mamaki, sai ga shi ta koma da yaro ta ce ta haifi tagwaye ne, amma dayan ya rasu.
Hasana ta fada wa Aminiya cewa, “Hajiya Lanti ta zo gidanmu ta bayyana mini irin hadarin da yaron yake ciki, saboda haka ta ba ni magani kala uku. Ta ce in yi wanka da daya; in yi turare da daya a cikin daki, kuma kada in rufe kofar dakin, idan na kunna; sannan in yi wa yaron wanka da dayan. Wanshekare na kunna magani da misalin karfe 8 na dare, sai barci ya dauke ni. Ko da na farka, sai ba yaro. Mahaifinsa ma ba ya gida a lokacin, kuma ba wata sutura a jikinsa, don lokacin da ya yi fitsari, saboda nauyin barcin da ya rufe ni, ban iya sanya masa kaya ba. Sai na fito daga daki ina kururuwar ban ga dana ba. Kishiyata ta fito, sannan jama’a suka taru, aka fada wa maigari, ya ce kowa ya yi ta addu’a”.
Bayan ’yan watanni, sai jita-jitar zargin wata mata a Saminaka da takan ziyarci Maitangadi ita ta sace jaririn ta bayyana.
“Wasu daga cikin mutanen kauyenmu suka tafi Saminaka bincike. Suka gano cewa matar da takan ziyarci kauyen namu tana bayar da maganin gargajiya, tana tare da wani yaro. Yayin da suka tuntube ta game da yaro, sai ta ce danta ne, amma mutunenta suka ce ba su san lokacin da ta haihu ba, saboda haka suka karbe yaro suka ba mutanen kauyenmu. Matar ta abodare cewa danta ne, wanda ta haifa a wani waje daban”. Inji Hasana.
Lokacin da aka mika wa Hasana yaron, sai da ta dade tana dubansa, kafin da hakkake lallai danta ne, musamman saboda karin tsagar fuskar da Hajiya Lanti ta yi masa.
Hajiya Lanti ta ce, “Na je kauyensu ne don yi musu ta’aziyyar wata tsohuwa da ta rasu. A lokacin ne na hadu da mahaifin yaron, wanda ya yi min alkawarin zai ba ni Naira dubu ashirin (N20,000), na wani magani da na ba shi, saboda wani irin motsi da ya ji, wanda bai taba jin irinsa ba a bayan gidansa, saboda haka ya bukaci in dauki yaron in tafi da shi, saboda yana tsoron wani abu na iya afkuwa. Wanshekaren ranar sunan yaron na koma na dauke shi na hau babur na tafi”.
Aminiya ta gano cewa ashe Hajiya Lanti ta yi wa mijinta danfulani karyar ta haifi tagwaye dayan ya rasu. “Na bar gidansa ina da ciki, amma sai na yi barinsa. Na fada masa cewa dan nasa ne don ya bar ni in zauna a gidan. Har ma na fada masa likitoci sun ce kada yaron ya sha ruwa, sai dai na kwalba, muka yi masa suna Hasan, muka yi masa tsagar danginsa.
“Bayan ’yan watanni, sai wasu mutane suka kira ni, suka tambayi ko dan wane ne, na ce musu nawa ne, saboda yarjejeniyar da muka yi da mahaifinsa a kauyen Maitangadi, amma suka ce sai mun je gida sun ga yaron. Ko da muka isa gidan, kafin in ce uffan, wani daga cikinsu ya fizge yaron daga hannuna,” inji Hajiya Lanti.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Kaduna, Aminu Lawan ya tabbatar da an kai wa ’yan sanda rahoto a Saminaka game da bacewar jariri kuma sun yi bincike sun gano shi. Matar da ake tuhuma ta ce da sanin mahaifin yaron, shi kuma ya ce bai san da magana ba, kuma ba abin da zai sa ya bayar da dansa saboda kowane irin dalili. “Ban ma fahimci ainihin abin da take fadi ba,” inji mahaifin yaron.
Kakakin ’yan sandan ya ce, “Muna bincike kuma da zarar mun kammala, za mu gufanar da lamarin gaban kotu”.