Yadda wata mata take kiwon kyanwa 122 a gidanta

Wata mata mai ’ya’ya biyu ta bayyana cewa tana kashe Yuro dubu 90 (kimanin naira miliyan 20) a kowace shekara wajen kulawa da kyanwoyinta fiye da 120, kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito ranar Litinin. Matar mai suna, Silbana balentino-Locke, mai shekara 55, tana biyan wasu ma’aikata biyu domin kulawa da magunan a gidanta […]

Yadda wata mata take kiwon kyanwa 122 a gidanta
Yadda wata mata take kiwon kyanwa 122 a gidanta

Wata mata mai ’ya’ya biyu ta bayyana cewa tana kashe Yuro dubu 90 (kimanin naira miliyan 20) a kowace shekara wajen kulawa da kyanwoyinta fiye da 120, kamar yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito ranar Litinin.

Matar mai suna, Silbana balentino-Locke, mai shekara 55, tana biyan wasu ma’aikata biyu domin kulawa da magunan a gidanta da ke birnin Landan da ke kasar Birtaniya.
Silbana ta ce maigidanta mai suna, Tony ba ya nuna wata damuwa da wannan al’amarin musamman ma idan aka yi la’akari da yadda yake dade wa a wurin aikinsa kafin ya dawo gida, kamar yadda jaridar ta ruwaito. Har ila yau, ta ce tana kashe Yuro 500 (kimanin naira dubu 120) a kowane mako wajen ciyar da kyanwoyin. “Babu wurin da wadannan kyanwoyin ba sa shiga a cikin gidan nan,” inji ta.
Misis balentino-Locke ta fara kiwon magunan ne a gidanta kimanin shekara 20 da suka wuce, amma babban burinta ya fara cika ne a shekarar 1998, lokacin da aka sanya wa gidan sunan Romney House Cat Rescue, wato Gidan Ceto Kyanwa. “Na fara tara kyanwoyin ne a shekarun 1990 kuma ina hakan ne saboda tsananin kaunar da nake musu, ” inji ta.