Yadda waya ta jawo kone-kone a Abuja
A ranar Larabar makon jiya ne zargin satar waya da kanikawa suka yi ya haifar da kone-kone a Jabi daki biyu da ke kusa da babbar tashar motoci da ke gundumar Jabi a Abuja, inda aka kona motoci masu tsada.Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa, wutar rikicin ta fara ruruwa ne lokacin da wadansu […]

A ranar Larabar makon jiya ne zargin satar waya da kanikawa suka yi ya haifar da kone-kone a Jabi daki biyu da ke kusa da babbar tashar motoci da ke gundumar Jabi a Abuja, inda aka kona motoci masu tsada.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa, wutar rikicin ta fara ruruwa ne lokacin da wadansu kanikawa, wadanda Yarabawa ne, suka zargi wadansu matasa da ake lira ’yan bola da sace musu waya kirar Samsung Galady, inda al’amari ya kazance ya haifar da kone-konen motoci da kuma wuraren kwanan matasan da ake kira bacoci.
Wani dan bola mai suna Kabiru dan Halas ya ce, “An ji Yarabawa suna ta daga jijiyar wuya suna cewa ’yan bola ne suka sace musu wayarsu kirar Samsung Galady, muka ce musu ba mu dauka ba, a nan suka ci gaba da fakonmu. Bayan wadansu ’yan kwanaki sai suka ga wayar a hannun wani dan bola.”
Ya ce bayan sun ga wayar ne suka kama shi, sannan suka tambaye shi me ya sa ya sace musu waya, inda ya fada musu cewa tsinta ya yi, suka kwace wayar, sannan suka bubbuge shi. “Wannan al’amari ya ba mu haushi, aka yi ’yar hatsaniya har ’yan sanda suka shigo, inda aka mayar da al’amarin ofishin ’yan sanda na Utako, a can aka ci gaba da batun sasantawar. Sai dai kuma a yayin da al’amarin ke wurin ’yan sanda sai kawai suka sanya wa bococinmu wuta, hakan ya bata mana rai, inda muma muka dauki matakin da ya dace.”
Wani mai suna Ibrahim da ke sana’ar faci a kusa da wurin da al’amarin ya faru ya ce, dama akwai tsattsamar dangantaka tsakanin ’yan bola da kuma kanikawan.
“Dangantaka tsakanin Yarabawa kanikawa da ’yan bola ta yi tsami, duk da cewa a wuri daya suke zama. Kanikawan suna zargi ’yan bola da sace musu batirin motocin da ake kawo musu gyara da kuma kananan karafa, inda ’yan bola ke musanta batun. Hakan ya sanya suke yi wa juna kallon hadarin-kaji, bayan Yarabawan sun zargi ’yan bola da sace musu waya sai rikici ya balle, inda Yarabawa suka kone musu bacocinsu, su kuma ’yan bola suka kona musu motoci kusan biyar da aka kawo musu gyara.” Inji shi.
Olusola Daniel daya daga cikin kanikawan ya ce bayan an sasanta su a ofishin ’yan sanda ne sai kawai ’yan bola suka yi gangami sannan suka kone motoci biyar da aka kawo musu gyara.
Ya ce, “Ina karkashin wata mota ina gyara sai na ji ihu, hakan ya sanya na mike da sauri, bayan na ga ’yan bola dauke da makamai da jarkar mai, sai na gudu, inda kafin ka ce wani abu sun fara dukan wadanda suka samu a wurin, duk kanikawa da wadanda suka kawo gyaran motocinsu suka gudu, daga nan suka fara kona motocin da aka kawo mana. Daga baya ’yan sanda suka zo, al’amarin da ya sanya kurar ta lafa.”
Ya ce a cikin motocin da ’yan bola suka kona musu akwai Jeep da Honda da Starlet da sauransu.
Baba Musa wanda ya ce yana kusa lokacin da al’amarin ya faru, ya ce yana tsaye a kusa da wurin sai ya ga wani mutum ya wuce a guje yana cewa ’yan bola za su kasha kanikawa, “ban ankara ba sai na ga hayaki na tashi, daga baya ne na gane wadansu motoci aka kona.”
Wani dan bolar da ya ki bayyana sunansa ya ce, duk a cikin abubuwan da aka kona masa bai ji takaici kamar yadda wata atamfa da kuma shaddar da ya saya wa mahaifansa suka kone ba.
“Na ji takaici bayan atamfar da na saya wa mahaifiyata da kuma shaddar da na saya wa mahaifina sun kone, mun yi asara mai yawa. Mun dade muna kwadago muna tara kudi da dukkan kayayyakin da muka tara, amma suka kone mana su.” Inji shi.
A lokacin da Wakilin Aminiya ya ziyarci wurin da al’amarin ya faru ne ya ga wata mata da ’yan sanda biyu, inda ya ji tana cewa motarta kirar Jeep na daya daga cikin motocin da aka kona, inda ta ce ta kawo a gyara mata burki ne sai wani dan uwanta ya kira ta sakamakon wani abu mai muhimmanci da ya taso, don haka ta bar motar ta shiga tasi, daga baya ne ta ji labarin abin da ya faru.Ta ce tun da al’amarin yana wurin hukuma ba za ta ce komai ba.
Wakilin Aminiya ya je ofishin ’yan sanda na Utako don tuntubar halin da ake ciki game al’amarin, sai DPO ya sanar da shi tabbas an kawo karar ofishinsa, amma ba shi ikon yi wa ’yan jarida karin bayani, amma tuni ya tura rahoton abin da ya faru zuwa gaba.
Mai magana da yawun ’yan sanda DSP Hyelhira Altine Daniel ta tabbatar da faruwar al’amarin, ta ce,
“Muna da labarin rikicin da ya barke tsakanin kanikawa da ’yan bola, mun tura jami’anmu wurin sun kwantar da tarzomar da ta tashi, muna kuma bincike a kan al’amarin.” Inji ta.