Yadda wurin tsare bayi ya zama wajen yawon bude ido
kasar Senegal, daya ce daga cikin kasashen Afirka inda aka yi cinikin bayi zuwa yammacin duniya.Wani wuri da ake ajiye bayin shi ne Tsibirin Goree, wanda a yanzu ya zama wani wurin yawon bude ido da Turawa da kuma wasu bakaken fata daga sassan Afirka da dama. Tsibirin mai nisan Kilomita 35 daga babban birnin […]
kasar Senegal, daya ce daga cikin kasashen Afirka inda aka yi cinikin bayi zuwa yammacin duniya.
Wani wuri da ake ajiye bayin shi ne Tsibirin Goree, wanda a yanzu ya zama wani wurin yawon bude ido da Turawa da kuma wasu bakaken fata daga sassan Afirka da dama.
Tsibirin mai nisan Kilomita 35 daga babban birnin kasar, Dakar, yana samun ziyarar bakin da ba za a iya lissafawa ba.
Duk da cewa karamin jirgin ruwan da jama’a suke amfani da shi domin shiga wannan tsibiri an tanadeshi domin daukan mutane 350, amma kuma ana wuce wannan adadi ganin cewa a wani lokaci ba a lissafa yara kananan da ake tafiyar da su. A kullum wannan karamin jirgin na kwasar mutane da dama a ko wace rana.
Jirgin yana aiki ba tare da tsayawa ba. A wani lokaci ma idan jama’a suka yawaita kamar a karshen mako, akan kara wani jirgi don su zama biyu. Saboda haka wannan yawon bude idon da jama’a suke yi yana samar wa karamar hukumar tsibirin Goree dimbin kudin shiga. Baya ga wannan kuma, wadanda suke so a yi musu jagora na daukan hayar jagora su biya shi, ya shigar da su sako-sako na wannan tsibiri ya yi musu bayanin abin da ya kunsa.
Da farko duk wani mutum da aka kama aka kai fursunar mace ko namiji, ana ajiye shi ne ko kuma ita ne a dakin auna bayi. Akalla ana bukatar mutum ya kai nauyin Kilo 60 (wato ya kara nauyin buhun Siminti da kilo 10).
Har ila yau, idan mutum bai cika ba, ana ciyar da shi wani abinci da zai gina mishi jiki. Ana ciyar da shi na wasu watanni. Daga an samu biyan bukata kuma sai a canza mishi mazauni ya koma zama a gidan yari a daure shi a cikin sarka. Wannan ya nuna ke nan ya cika sharadin tafiya yin noma a gonan rake a kudancin Amurka.
Ana ciyar da bayin abinci a kullum so daya a yini kuma a kwancesu so daya. Suna da sarkoki a kafa da kuma wuya. Akan hada mutum biyu a cikin sarkar guda. Maza daban, mata daban, yara kanana daban.
Gabannin tafiyar Amurka kowane fursuna na zama a inda aka ajiye shi na tsawon watanni uku. Dagan nan ne ba shi da ikon yin rashin lafiya, kuma kada ya nuna alamun kasawa na kwazon aiki. Har idan aka tadda haka daga wurin wani bawa, ana jefa shi teku ne, manyan kifaye su cinye shi danye. Mai gardama kuma ana saka shi a wata fursuna ta daban na masu taurn kai, a ba shi wahala sosai. Ana lakada masa duka a kullum wayewar gari. Matan da suke dinga yin sa’a su kubuta su ne wadannan da suke haihuwa da Turawa iyayen gidansu.
A wata ziyarar da marigayi PapaRoma John Paul na II ya kai tsibirin, ya nemi afuwa ga jama’a da su yafe wa darikar Katolika wadda ta ba da gudunmawa wurin cinikin bayin. Amsar da ya samu ita ce an amince a yafewa cocin Katolika, amma kuma ba za a taba manta wa da irin cutar da jama’a da gallaza musu da cocin ta sa aka yi ba. Hakazalika, marigayi tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela, a lokacin da ya kai ziyara kasar Senegal ya kai ziyara tsibirin, inda ya kutsa kai cikin fursunar kangararru duk da irin takurar da take da shi, ya fito da hawaye a idanuwarsa yana kuka yana tuna lokacin da ya yi zaman gidan yarin.