Yadda wutar lantarki ta kashe wata amarya a Jos
Fatima Abubakar Hassan, mai shekara 30 da haihuwa, ta kasance cike da farin ciki da annashuwa, kuma tana da dalilin hakan. Dalilin kuwa shi an kammala shiri tsaf, rana kawai ake jira a daura mata aure da tsohon saurayinta, Ibrahim Musa (wanda aka fi sani da Baban Abba), mai shekara 40 da haihuwa. Za ta […]
Fatima Abubakar Hassan, mai shekara 30 da haihuwa, ta kasance cike da farin ciki da annashuwa, kuma tana da dalilin hakan.
Dalilin kuwa shi an kammala shiri tsaf, rana kawai ake jira a daura mata aure da tsohon saurayinta, Ibrahim Musa (wanda aka fi sani da Baban Abba), mai shekara 40 da haihuwa.
Za ta auri Baban Abba wanda ya neme ta tun tana budurwa shekara 10 da suka wuce ne bayan da tsohon mijinta, wanda ta haifi ’ya’ya biyu—mace da namiji—da shi, ya sake ta.
Sai dai kuma masu iya magana kan ce ana bikin duniya ake na kiyama; saura kwana shida a daura auren tsautsayi ya gitta, wutar lantarki ta yi sanadin mutuwar Amaryar wacce ke zaune a Unguwar Rogo a Jos, babban birnin jihar Filato.
- Yadda wani matashi ya rasa ransa garin ceto ’yan mata
- ‘Yadda za ki zama cikin matan da mazan yanzu ke so’
Tsautsayi ba ya wuce ranarsa
Da take bayani a kan yadda wannan al’amari ya faru, wata ’yar uwar marigayiyar wacce abin ya faru a kan idonta, ta ce Fatima ta kammala wanke-wanke ne, sai ta mike ta kama wani karfen satellite da aka kafa a gidan.
“Ashe wannan karfe yana hade da kwanon rufin gidan, kuma akwai babbar wayar lantarki da ta fado kan rufin. A lokacin akwai wuta, don haka nan take wutar lantarkin ta ja ta, ta fadi kasa.
Da ma dai, a cewar ’yar uwar Amaryar, an yi kwanaki hudu babu wata a unguwar, sakamakon wata takaddama da aka yi a tsakanin wasu matasa da ma’aikatan kamfanin wutar lantarki.
“A daidai wannan lokaci ne wannan wayar wutar ta fado kan kwanon rufin, ba tare da mutanen gidan sun sani ba, har aka warware matsalar aka kawo wutar ba a gyara ba. Ta dalilin haka wannan mummunan al’amari ya faru”, inji ta.
Shi ma da yake nasa bayanin, wani dan uwan marigayiyar mai suna Mas’ud Abubakar Hassan, ya ce a ranat ya raka Fatima ta sayi kujeru da sauran kayayyakin daki, don wannan aure da za ta yi.
Mugun labari
Ya ce bayan da suka dawo gida ya sake fita zuwa cikin gari, don gudanar da wasu harkokinsa.
“Ina cikin gari sai na ji an kira ni a waya daga gida ana bukatar na zo da gaggawa, domin akwai abin da ya faru ga marigayiyar.
“Nan take na rugo zuwa gida na tambaya mene ne ya faru? Sai aka shaida mani cewa ga abin da ya faru ga marigayiyar.
“A lokacin da na isa gidan na samu marigayiyar kwance a kasa ba ta motsi, nan take na dauke ta zuwa wani asibiti da ke kusa da mu, suka tabbatar da cewa ta rasu.
“Daga nan muka dauko ta, muka kawo ta gida aka yi mata jana’iza, kamar yadda addinin Musulunci ya umarta”, inji Mas’ud.
‘Ba na iya barci’
Da yake bayani a kan yadda ya samu labarin rasuwar marigayiyar, Angon da aka yi niyyar daura masa aure da ita, Ibrahim Musa, ya ce ya yi matukar kaduwa.
Ya ce a ranar bai iya cin abinci ba, kuma sai da ya yi kwana da kwanaki, ba ya iya barci.
“A duk lokacin da na tuna wannan al’amari sai na zubar da hawaye, saboda irin son da muke yi wa juna da marigayiyar.
“Mun kai shekara 10 muna soyayya da ita, tun tana budurwa. Ana gobe faruwar wannan al’amari, sai da muka yi awa biyu muna magana da ita a waya” inji Ibrahim.
Angon ya kuma bayyana yadda suka fara soyayya da marigayiyar.
“Mun hadu da marigayiyar ne a garin Tilden Fulani da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi; tana zuwa garin saboda akwai kanwar mahaifiyarta a can”.
Soyayya gamon jini
Ibrahim Musa ya kara da cewa lokacin da suka hadu shekara 10 da suka gabata, ta yarda za ta aure shi, don haka ya yi iyakar kokarinsa, amma saboda matsalolin rayuwa na rashin kudi abin bai yiwu ba.
Saboda haka ya ba ta shawara idan ta samu wani, ta yi aure.
Ya ce daga nan ta samu wani ya aure ta, har suka haifi yara biyu namiji da mace, sai mijin ya sake ta a shekarar da ta gabata.
“Da na samu labarin cewa aurenta ya mutu na nemi lambar wayarta, muka yi magana da ita a kan cewa idan ta amince zan aure ta a matsayin matata ta biyu, zan yi matukar farin ciki”.
Ya kara da cewa da ya je gidansu ta karbe shi hanu bibbiyu tare da iyayenta kuma ta amince da bukatarsa aka sanya masa sadaki ya biya aka sanya ranar da za a daura masu aure.
Ya kuma ce ya yi iyakar kokarinsa don ganin ya hada kyakyawar hulda tsakanin matarsa da marigayiyar.
“Don haka a lokacin da matar tawa ta samu labarin rasuwar marigayiyar da kyar na iya lallashinta, saboda kukan da take yi sakamakon kaduwar da ta yi da rasuwar marigayiyar”, inji Baban Abba.