Yadda ya kamata ki yi kwalliya
Shin kina cikin kuruciyarki kuma fuskarki ba ta yi miki yadda kike so saboda kuraje? Kada ki da mu, domin idan har kin bude wannan shafin namu na kwalliya, to ki san cewa matsalolinki sun kusa karewa in sha Allahu. Wadannan irin kurajen matasan na faruwa ne saboda canjin da jikinki ke samu a wannan […]
Shin kina cikin kuruciyarki kuma fuskarki ba ta yi miki yadda kike so saboda kuraje? Kada ki da mu, domin idan har kin bude wannan shafin namu na kwalliya, to ki san cewa matsalolinki sun kusa karewa in sha Allahu. Wadannan irin kurajen matasan na faruwa ne saboda canjin da jikinki ke samu a wannan lokacin. A wannan makon mun kawo miki yadda za ki magance wadannan matsalolin kamar haka:
· Idan kina sha’awar samun fuska mai laushi kuma marar kuraje, to ya kamata a kullum ki tuna abubuwa uku; wanke fuska da ruwan ‘face wash’ da goge fuska da sinadarin ‘cleanser’ da kuma shafa man da ya dace da fatarki.
· Ki zama mai kula da hannayenki a kodayaushe. Idan kina da kurajen fuska, kada ki dame su da yawan matsa, domin yin hakan na janyo tabo mai wuyar bacewa.
· Ki rika amfani da man shafawa mai dauke da sinadarin ‘sunscreen’ minti 15 kafin ki shiga rana.
· Domin yin kwalliya mai inganci, ki rika shafa man gashi kafin ki wanke gashin kanki. Yin hakan zai fitar da dattin da ya makale a cikin gashin.
· Kada ki rika kwanciya da kwalliya a fuska. Ki tabbata kin wanke fuskarki kafin ki kwanta barci; walau na rana ne ko na dare. Kwanciya da kwalliya a fuska na janyo fesowar kuraje.
· Abu na karshe shi ne, ki rika amfani da turare idan kin yi wanka domin ba da kamshi a jiki, kasancewar a wannan lokacin idan ba ki rika shafa turare ba jikinki zai rika wari.