Yadda ya kamata mu kasance a rayuwarmu ta yau da kullum II

Kamar kullum, yau ma dai muna tafe da sallama, assalamu alaikum; ya ku masu bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, yau kuma ga mu dauke da wani sabon maudu’i, inda za mu duba wasu hikimomi domin su yi mana jagorar yadda za mu tafiyar da rayuwarmu, irin yadda za mu kasance masu amfani […]

Yadda ya kamata mu kasance a rayuwarmu ta yau da kullum II
Yadda ya kamata mu kasance a rayuwarmu ta yau da kullum II

Kamar kullum, yau ma dai muna tafe da sallama, assalamu alaikum; ya ku masu bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, yau kuma ga mu dauke da wani sabon maudu’i, inda za mu duba wasu hikimomi domin su yi mana jagorar yadda za mu tafiyar da rayuwarmu, irin yadda za mu kasance masu amfani ga kawunanmu kuma masu amfani ga sauran al’umma.
A wannan karon, zan ja hankalinmu ne zuwa ga wani mashahurin gwarzo, mai hikima; wanda ya kasance jagora ga al’umma. Wannan gwarzo kuma sadauki, shi ne Aliyu dan Abi dalibi (Allah Ya kara masa yarda). Shi ne ya sassaita al’umma da tarin hikima da falsafar rayuwa. An ruwaito shi yana cewa, a rayuwarmu ta yau da kullum, mu kasance kamar kudan zuma.
Da yake kara bayani game da wannan batu, fasihin sai ya ce, a rayuwar kudan zuma, duk wani abu da zai ci mai kyau ne kuma mai tsarki. Ba ya cin wani abu mai datti ko wanda ya kasance najasa. Haka kuma duk wani abu da kudan na zuma ya aje ko ya jefar, abu ne mai dadi kuma mai dadadawa. Wani abu na uku game da shi kuma shi ne, duk inda zai zauna, wuri ne mai kyau kuma mai karfi, wanda ba ya karyewa.
Ko ina ma’ana da tasirin haka? Na farko dai, idan mutum ya kasance kamar zuma, babu shakka zai zama mai amfani ga kansa, kuma ya amfanar da sauran al’imma. Mutum zai kasance mai tsantsani ga abin da zai ci, domin kuwa duk abin da zai ci, zai kasance mai kyau ne kuma mai tsarki. Idan haka ta faru, ka ga mutum ba zai yi kokarin cin abincin haram ba, ba zai ci abin da shari’a ta hana shi ba, madamar ya yi koyi da halin zuma. Madallah kuwa da mutumin da ya kaurace wa cikinsa daga haram, ya kaurace wa cikinsa daga datti, domin kuwa zai kasance mutum mai lafiya a karan kansa, sannan kuma ya kasance mai amfanar da sauran al’umma da yake zaune a cikinsu.
Kamar kuma yadda bayani ya gabata, cewa duk abin da kudan zuma zai aje ko zai jefar, abu ne mai dadi kuma mai dadadawa. Idan mutum ya ce zai yi koyi da kudan ta wannan fanni, babu shakka zai kasance mutum marar rowa, mai rarraba alheri ga sauran al’umma. Mu duba, duk abin da zuma ta zubar ko ta kasayar, abu ne da zai amfani al’umma. Zai kasance magani, zai kasance abinci, da sauransu.
Madalla da mutumin da zai zama kamar zuma ta fuskar rarraba alheri. Domin kuwa a duk lokacin da zai aiwatar da wani abu, zai aiwatar da shi da inganci, idan ma ya kasance dan kasuwa, to ba zai sayar da gurbatattun kaya ga mai saye ba, sai dai ya mika kyakkyawa kuma mai inganci, kamar dai yadda kudan zuma yake yi. Idan aka samu haka cikin al’umma kuwa, da shi ke nan, babu cuta kuma babu cutarwa.
Abu na gaba da ke bukatar bayani shi ne, yadda aka ce kudan zuma ba ya zama wuri sai mai karfi, wanda ba ya karyewa. Idan mutum ya so ya yi koyi da kudan ta wannan fanni, ke nan zai kasance mai gaskiya, wanda ya kama hanyar gaskiya, wacce ba ta tsinkewa ko alama. A duk lokacin da mutum ya durfafi hanyar gaskiya, babu inda za ta kai shi sai ingantaccen wuri, inda zai samu tsira. Madamar mutane sun kasance kamar kudan zuma, suka rika zama a wuri mai karfi, suka rika kama reshe, suna sakin ganye, babu shakka al’umma za su kasance cikin ni’ima a kowane lokaci. Babu cuta babu cutarwa, sai gaskiya da gaskiya da zaman gaskiya.
Wasu darussa da za mu kara dorawa bisa wannan hikima ta fasihin gwarzo su ne: Mu kasance masu yawan yin afuwa ga juna, musamman ma a lokacin da muka fusata, muka harzuka. Mun kasance masu dauriyar yin kyauta a lokacin da muke cikin matsatsi. Mu kasance masu kamewa daga aikata barna a lokacin da muka samu kanmu cikin kadaici da damar yin haka. Haka kuma, mu lizimci fadin gaskiya koda a gaban wane ne, koda a gaban wadanda muke tsoro ne.
Fa’idojin da ke tattare da aikata haka suna da dimbin yawa. Misali, a lokacin da muka lizimci yin amfuwa a lokacin da muke cikin fushi, babu shakka za mu kunyata Shaidan. Daga nan sai al’umma su kasance cikin aminci da juna. Idan kuwa muka saba da kamewa daga aikata barna a lokacin da muke da aikon aikatawa. Nan ma sai tasirin haka ya amfani jama’a. A lokacin da muke yin kokarin kyauta a lokacin da muke cikin matsatsi, to idan muka samu budi, ya kake zaton al’umma za ta kasance? A lokacinn da muka saba da fadin gaskiya koda ga wadanda muke tsoro ne, shi ke nan, duniya ta yi kyau kuma ta gyaru.
Muna addu’ar Allah Ya yi mana jagora, Ya kuma ba mu karfin gwiwar dabbaka wadannan kyawawan dabi’u a rayuwarmu, amin.

Dausayin kauna

kalubale, matsala ko cikas da muke fuskanta a harkar soyayya (6)

A ci gaba da maudu’inmu, za mu fara da sakon Yusuf Haruna (08139618011) angon Khadeeja, in Allah Ya so kuma uban Abdoulmerleeyk; ya ce: “Fatan alheri ga FDk da sauran ma’abota karatun Dausayin kauna gaba daya. A gaskiya maganar A’isha Abubakar Jos da ta yi, take cewa maza mu ji tsoron Allah mu daina zina; a gaskiya mata kuma kuna da taku gudunmuwar da kuke ba da wa wajen zina da ku. Kina ga maganar da kika yi cewa Allah Ya kare ki daga saurayinki, to kin ga Allah Ya ga zuciyarki ba yaudara a ciki ne, shi ya sa bai hada ki da wanda bai dace da ke ba.
Matsalar da ake samu yanzu, kawaye mata suna yi wa kawayensu kwacen saurayi. Kin ga da yake Allah ba azzalumin kowa ba ne sai Ya hada ta da daidai ita, domin yaudarar ki ta yi kuma mata yawancinku kudi kuka fi bi. Shi kuma namiji idan ya ga abin hannunsa kike so sai ya nemi ya yi zina da ke, domin shi ma ya fanshe kudinsa. Allah Ya ba mu ikon gyara halayenmu, amin.”
Sai kuma Haruna Uba Ringim (08035938460), wanda ya ce: “An gaida FDk, tare da fatan kana lafiya. Hakika a da na fuskanci matsala a kan soyayya, wadda ta sa har na ji na tsani soyayya, kamar na yi hauka wallahi saboda cin amana da aka yi mani kuma babbar matsalar ma ita ce, son abun duniya ga iyaye. Sai mai kudi kuma yarinya ta nuna ba wanda take so sai ni. Ka ga wannan kalmar tana bata mini rai sosai amma a yanzu alhamdu lillahi, don kuwa abin sai san barka. Kun ga amfanin hakuri ke nan.”
Shi kuwa Muhammad Bello Muhammad Abuja (08029597910) cewa yake: “Gaisuwa tare da jinjinar ban girma ga dukkanin daliban wannan makaranta mai albarka da gwarazan likitocin da ke aiki dare da rana don taimaka wa ma’abota wannan babban zaure (FDk) da maganin cututtukan da ke damun su. Allah Ya kara wa jagoran FDk daukaka da hakurin jure wa tafiyar da filin. Ta wannan filin mun hadu da abokai maza da mata, wadanda muke tamkar ’yan uwa na jinni. Wasu ma sun yi aure ta hanyar filin nan na FDk. Ni ma ina jin kanshin tawa matar, ta nan za ta fito. In har hakan ta tabbata kuwa to kai ne waliyin ango. Allah Ya kara mana so da kaunar junanmu. Amin.”
To fa! Malam Muhammad, a ce FDk ne waliyin ango, yaya za ka ga filfila fuka-fukai? Allah Ya tabbatar da alheri, amin. – FDk.
Sai kuma sakon Sardaunan Matasa (08091673531) wanda ya ce: “Jama’a, abin da Sardauna ya jira shekara goma sha uku, ga shi yau ya samu Ummin da ake tunanin ba ya samu. Haka Allah ke naSa ikon! To jama’a ku taya Sardaunan Matasan Dutsin-ma murna, Allah Ya ba shi Ummi, wadda ya yi shekara goma sha uku yana jira sanyi, zafi da ruwa, duk ya daure. Na gode, na gode.”
Dama duk abin da ka nema, ka daure da hakuri, idan dai rabonka ne sai ka same shi. Allah sa mu dace, amin! – FDk.
Daga Mista Tsari Sakkwato (08143853321): “FDk, ina mika dubun gaisuwata a gare ka da fatan alheri kuma ina jaddada godiyata a gare ka, Allah kuma Ya kara dankon zumunci amin.
Don Allah FDk, ina son ka ba ni dama a karo na biyu, domin na mai da martani ga Fatima Abuja. Don tsoron shiga tarkonku mai wuyar fita, shi ya sa kuma a kullum nake rokon Allah kada ya cusa main irin matsananciyar soyayya ga wata ’ya mace, wadda har za ta sa ta samu damar yaudara ta. Haba mata, don Allah a rage kwadayi saboda Hausawa sun ce kawadayi mabudin wahala.
Daga karshe kuma nake mika ta’aziyata ga Kanawa game da babban rashin da suka yi na magari Alhaji Ado Bayero, Allah Ya jikansa, Ya yi masa rahama. Allah kuma Ya ba ku mafificinsa. Mu kuma idan tamu ta zo Allah Ka sa mu cika muna masu imani, amin.”
Sakon wani mai lamba (08094791726) yana cewa: “Ina yi maka fatan alheri. Don Allah FDk, ka taya ni dubawa; wai kuwa Na’ima tana sona kuwa? Idan na yi mata maganar so takan nuna ta amince, har ma mukan yi hira da ita amma ba ta ba ni kulawa irin wadda soyayya ta tanadar. Ba ta damu dani ba.”
Ikon Allah! To Malam, ni ma tambaya zan yi maka kafin in san inda ka dosa da taka tambayarka. Ka ce Na’ima takan amince da batunka na so, tana kuma amincewa ku yi hira amma kuma ka ce ba ta ba ka kulawar da soyayya ta tanada. Shin wadanne abubuwa ne soyayya ta tanada kuma?” – FDk.
Daga Fateemah Abdullahi ’Yar Lajawa (08112538490): “Aminci ga ma’abota wannan fili. Gaskiya ne batun da Fatima ta fada, cewa maza sun faye son kudi. Gyaran kawai da kawai zan mata shi ne, ba maza ne kawai suke da son kudi ba, har da mu matan. Don a tawa fahimtar, yanzu tsakanin samari da ’yan mata ba wata soyayya face kudi. Eh, mana haka ne! Ku yi duba ku gani, a wannan zamanin namu za ka ga namiji in dai yana da kudi, duk muninsa duk, munin halinsa ’yan mata bibiyarsa suke. Haka su ma mazan, in dai yarinya suka ga alamar za su yi auren jari; duk wulakanci, duk munin halinta makale mata suke yi! Gaskiya babban kalubale da ake fuskanta shi ne, mugun kwadayi tsakanin samari da ’yan mata. Abin da muka manta da shi shi ne cewa Allah ne mai azurtawa. Idan muka yi duba, a unguwarku talakawa nawa              ne suka yi arziki kuma masu kudi nawa ne suka talauce? Ya kamata mu tsaya mu lura. Allah Ya sa mu gyara halayyenmu baki daya, Ya zaba mana mazaje nagari kuma samarin Ya ba ku mata nagari ba ‘lashe money’ ba.”
Haka ne ’yar mutanen Lajawa, ni ma na amince da wannan batu naki. Allah Ya ganar da mu gaskiya kuma mu bi ta ba da gardama ba, amin. – FDk.