Yadda ya kamata rayuwar Kirista ta kasance (4)
Da yake kan zama da wahala ka iya karanta abin da ke cikin zuciyar mutum daga fuskarsa. Yawancin lokaci abin da bakinmu yake fadi ba shi ne a cikin zuciyarmu ba, mu sani Allah Yana duba dukan tunanin da kowane dayanmu yake yi. Gaskiyar ita ce, ga mutane da yawa, su ma za su yi […]
Da yake kan zama da wahala ka iya karanta abin da ke cikin zuciyar mutum daga fuskarsa. Yawancin lokaci abin da bakinmu yake fadi ba shi ne a cikin zuciyarmu ba, mu sani Allah Yana duba dukan tunanin da kowane dayanmu yake yi. Gaskiyar ita ce, ga mutane da yawa, su ma za su yi fatar wani abu mummuna ya faru da shi ko kuwa wani kusa da shi; wannan ita ce tunanin dan Adam. Amma sai mu tuna cewa an rigaya an sabunta tunaninmu ta wurin zubar da jinin Yesu Kiristi bisa gicciye, mun zama sababbin halitta.
Koyarwar da muka samu daga wurin Ubangijinmu da mai cetonmu shi ne – mu albarkaci irin wadannan mutane. Ba mu da iznin mu yi gaba da su, ba mu da izinin mu yi musu fatar mugunta ko bala’i, ba mu da ’yancin mu ce za mu yi kiyayya da su, babu yadda za mu yi musu keta, ba don komai ba, sai dai don sanin cewa muna dauke da Ruhun Allah a cikinmu. Abin da ya sa muke da bambanci da sauran jama’ar da ke kewaye da mu. Idan har mun soma tunanin mugunta game da wadanda suke yi mana mugunta, to, sai mu sani cewa mun soma barin tafarkin Allah, ko kuwa ban-gaskiyarmu ba cikakkiya ba ce kuma muna aikin banza ne.
Maganar Allah na koya mana yadda za mu yi da irin wadannan mutanen, ta ce: “Ku albarkaci masu zaginku.” Albarka a takaice dai ita ce fatar alheri ga wani, kana son mutumin ya ci gaba sosai cikin duk abin da ya sa hanunsa a ciki; ko wurin kasuwancinsa ko kuwa wurin aikinsa na gwamnati, kai dai kana so ya ci gaba, kuma gaskiya daga cikin zuciyarka ne wannan fata. Lokacin da ka je yin addu’a ga Allah, kana tunawa da shi, kana rokon Allah a madadinsa cewa Allah Ya nuna masa alheri, ba lallai sai ya sani ba, wannan tsakaninka da Allah kawai, duk inda ka ga zarafin taimakonsa, sai ka taimake shi ba don komai ba amma domin kauna irin ta Allah. Kada ka yarda ka mai da mutum dan Adam mai gaba da kai, wannan zai zama kuskure ne ga kowane mai bin Yesu Kiristi. Ka sani cewa magabcinka daya ne kawai kuma shi ne Shaidan ko Iblis. Gaskiya Shaidan yakan yi amfani da mutane amma ba mutanen ba ne magabtanka, shi wanda ke aiki da su, shi ne ainihin magabcin. Nauyin da ke bisa kanka shi ne ka ci gaba da yi wa irin wadannan mutane addu’a domin Allah Ya sa su iya gane hanyarSa da kuma gaskiyarSa.
Bayyana irn wannan halin ne zai sa haskenmu ya haskaka kamar yadda Yesu Kiristi ya yi koyarwa a cikin Littafin Matta:5:14–16 cewa “Ku ne hasken duniya. Birnin da ke kafe bisa tudu ba shi boyuwa. Kuma ba a kan kunna fitila, a sa karkashin akushi ba, amma bisa tebur; sai ta haskaka wa dukan wadanda ke cikin gida. Hakan nan ku kuma ku bari haskenku ya haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su girmama Ubanku Wanda ke cikin Sama.” Idan har haskenmu yana haskakawa; abin da mutane za su gani shi ne kyawawan ayukanmu, ba domin gwanintarmu ba, amma domin ikon ruhunsa mai tsarki wanda yake aikinsa a cikinmu. Zama a matsayinmu na HASKEN DUNIYA na da muhimmanci sosai, domin duk mai bi wanda bai yi rayuwar haske ba, to a gaskiya ya ci amanar da Allah Ya damka a hanunsa, duniyar nan za ta ci gaba da zama cikin duhu har sai lokacin da masu sun gane cewa Allah Ya rigaya Ya b asu amanar haskaka wannan duniya. Hasken nan kuwa zai nuna ne kawai a lokacin da muka soma aikata irin wannan umarnin da Allah Ya ba mu.
Kada mu yarda da jarabobin da suke kewaye da mu a yau da kullum, Shaidan yana kokari ne ya ga cewa mun ki bin umarnin Allah, haka ya saba yi tun daga farko a zamanin Adamu da Hauwa’u. Koda yake wani lokaci za mu tsammaci cewa umurnin nan na da wahalar bi, amma ta wurin aikata su ne za mu ci nasara bisa Shaidan- ka gwada ka gani.
Ubangiji Allah Ya taimake mu Ya kuma ba mu hikimar cin nasara bisa dukan dabarun Shaidan. Kada mu manta da ci gaba da addu’a domin wannan kasa; musamman domin mu samu zaman lafiya Allah Ya kuma tsare mu daga miyagun mutane, amin.
Wadanda suke wulakanta ku; ku yi musu addu’a:
“Ku albarkaci masu zaginku; wadanda suke wulakanta ku, ku yi musu addu’a” (Luka 6 : 28)Wannan umarnin daga bakin Yesu Kiristi da kansa tana da kamar wuya. Ta ina mutum zai soma? Mutum wanda zai iya wulakanta ka ba aboki ba ne, mutum ne mai tsananin kiyayya gare ka, ba ya son ganinka ko da wasa, mutum ne cike da tsegumi da kuma keta. Irin wadannan mutane ba cikin sauki ake iya kaunarsu ba. Amma ga irin su ne Yesu Kiristi yake cewa mu yi musu addu’a. Babu yadda mutum zai iya aikata wannan idan babu sahihiyar kauna a cikinsa. Yin addu’a cikin kauna ba cikin fushi ko haushi ba. Sau da dama mutane suna cike da fushi domin muguntar da wani ya yi musu, shi ya sa koda za su yi addu’a; addu’arsu ta son kai ne, suna fatar wani bala’i ya auko wa wadanda suka yi musu mugunta, a cikin komai da suke yi; suna addu’a ga Allah Ya ziyarce su cikin fushinSa, Ya nuna musu azaba mai tsanani sosai. Amma duk wannan ba shi ne tunanin Allah ba. Babu yadda za mu nuna wa sauran mutane cewa daban muke a cikin wannan duniya da sauran mutane; kodayake muna cikin wannan duniya Littafi Mai tsarki ya koya mana cewa mu ba na duniya ba ne.