Yadda yajin aiki ya tsayar da harkoki a Kaduna
Tun da safiya masu yajin aikin suka rufe ma’aikatun Gwamnatin Jihar Kaduna.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) na gangami bayan ta fara yajin aiki saboda korar ma’aikata da wasu tsare-tsaren Gwamnatin Jihar Kaduna da ta ce kuntatawa ne ga ma’aiakta.
NLC ta fara yajin aikin ne bayan Gwamnatin Jihar ta ce babu gudu, babu ja da baya a sallamar da ta yi wa dubban ma’aikatanta a baya-bayan nan.
- Yayin aikin Kaduna: Jami’an tsaro sun bude Sakatariyar Gwamnati
- Yadda za a magance matsalar tsaro a Najeriya — IBB
- Yadda rikicin Falasdinawa da Isra’ila ya tada hankulan shugabannin duniya
Tun da sanyin safiyar Litinin NLC ta rufe tashar jirgin kasa da ke Rigasa, da Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da Sakatariyar Gwamnatin Jihar, wadda a cikinta 10 daga cikin Ma’aikatu n Gwamantin Jihar suke.
Kafin su fara tattaki a kan tituna bisa jagorancin Shugaban NLC na Kasa Ayuba Wabba, jami’an kungiyar sun bi ofisoshin Gwamnatin Jihar suna kullewa da zimmar tabbatar da tsayawar harkoki ci a ma’aikatun.
Ga wasu hotunan yajin aikin: