Yadda ‘yan ƙasahen waje ke rububin kasuwar Ore don sayan nau’ukan goro – Sarkin Hausawan Ore

Kasuwar garin Ore a Jihar Ondo, wacce aka kafa ta shekara 30 da suka gabata a Unguwar Sabo mazaunin Hausawa a garin na Ore ta yi fice wajen hada-hadar goro a ciki da wajen Nijeriya. “Wannan kasuwa ce a kan gaba fiye da sauran kasuwanni a Jihar Ondo baki ɗaya, ta fannin samar da kuɗaɗen […]

Yadda ‘yan ƙasahen waje ke rububin kasuwar Ore don sayan nau’ukan goro – Sarkin Hausawan Ore

Kasuwar garin Ore a Jihar Ondo, wacce aka kafa ta shekara 30 da suka gabata a Unguwar Sabo mazaunin Hausawa a garin na Ore ta yi fice wajen hada-hadar goro a ciki da wajen Nijeriya.

“Wannan kasuwa ce a kan gaba fiye da sauran kasuwanni a Jihar Ondo baki ɗaya, ta fannin samar da kuɗaɗen shiga da bunƙasa tattalin arziƙin jihar da ƙasa baki ɗaya,” in ji Sarkin Hausawan Ore, Alhaji Abdullahi Bagobiri.

Da yake yi wa Aminiya ƙarin haske, Sarkin Hausawan kuma Sa’in Garo a Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano ya ce, masu cinikin goro a Nijeriya da ƙasashen Ghana da Nijar da Benin da Chadi da Sudan da Libya da Saliyo a wancan zamani sun riƙa rububin shigowa cikin wannan kasuwa domin sayen nau’in goro irin wanda ake nomawa a yankin Ore da suke fataucin fita da shi zuwa ƙasashen duniya daban- daban.

Ya ce, hakan ne ya ɗaukaka martabar kasuwar daga cinikin goro zuwa hada-hadar dukkan nau’in kayan abinci da buƙatun yau da kullum da ake fataucin su a tsakanin Arewaci da Kudancin ƙasa.

Da yake zagayawa da wakilin Aminiya sassa daban-daban na kasuwar, Sarkin Hausawan ya ce, “babbar matsalar da ake fuskanta tsawon shekara 30 da kafuwar kasuwar shi ne lalacewar hanyar shiga cikin wannan kasuwa  mai nisan kilomita 3 kaɗai da mahukunta suka ƙi ɗaukar matakin gyara.

“Wannan abun kunya ce ga Ƙaramar Hukumar Odigbo da ita kanta Gwamnatin Jihar Ondo da suka ƙi ɗaukar matakin gyaran wannan hanya da mayar da kasuwar ta zamani’.’

Sarkin Hausawan ya ce, “a kowace shekara, ’yan kasuwar ne suke tara kuɗi kimanin Naira miliyan 3 domin sayan marmarar duwatsu da hayar motocin tifa masu kwasowa da biyan leburori ladan aikin cike manyan ramukan hanyar da mahukuntan suka kasa gyarawa.

An sha samun haɗarin manyan motoci ɗauke da kaya da suke faɗawa cikin gidaje a gefen wannan hanya.

A duk lokacin da irin haka ya auku muna ɗaukar hoton wuraren da motocin, inda muke miƙawa ga shugabannin ƙaramar hukumar da Gwamnatin Jihar domin su kawo mana ɗauki, amma har yanzu babu wata gwamnati da ta taɓa yin kataɓus a kan wannan lamari.

Titin kwalta da aka gina shekara 30 da suka gabata sam sam babu alamarsa a yanzu. Hana ƙarya Gwamna Rotimi Akeredolu kafin ya mutu ya taɓa kawo ziyara unguwar Sabo, inda ya yi min alƙawarin yi wa fadarmu kwaskwarima.

A nan take na shaida masa cewa, ba wannan ne a gabana ba, domin Allah Ya hore mana abun yin wannan aiki. Na shaida masa a gaban kwamishinonin da suka rufa masa baya cewa, buƙatarmu ita ce gyaran wannan hanya ba gyaran fada ba, inda ya amince ya sake yin wani alƙawarin da bai iya cikawa ba har Allah ya karɓi ransa.

Dubunnan ƙanana da manyan ‘yan kasuwa maza da mata da matasa musamman Hausawa a garin Ore sun dogara da wannan lasuwa ne wajen samun abun da za su ci a kowace wayewar garin Allah,” in ji shi.

Da yake amsa wata tambaya, Abdullahi Bagobiri ya ce, “a baya wani tsohon wakili mai wakiltar mazaɓar Odigbo a Majalisar Sokoki ta Tarayya ya taɓa sanar da mu cewa, mahukunta sun riga sun damƙa alhakin gyaran wannan hanya ga Hukumar Kula da Yankin Naija Delta (NDDC) kuma har an bayar da kwangilar aikin shekara 5 da suka gabata, amma sai murnar da muka yi a wancan lokaci ta koma ciki domin har zuwa yau ɗin nan shiru kake ji kamar an shuka dusa.”

Sarkin Hausawan ya yi kira ga dukkan mai hannu a kan wannan lamari, musamman Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Ondo da Ƙaramar Hukumar Odigbo da Hukumar NDDC su taimaka wajen kawo ɗauki a kan gyaran wannan hanya da mayar da kasuwar ta zamani. Ya ce, Kasuwar ta Ore a cakuɗe take da ’yan kasuwa na ƙabilun Yarbawa da Ibo da suke ƙarƙashin jagorancin shugabannin Hausawa tun lpkacin da suka kafa kasuwar.

Kasuwar ta Ore tana ci ne a kullum, sai dai jama’a sun fi taruwa domin baje haja a ranakun Litinin da Talata da Laraba da Alhamis.

Kuma akwai nau’in goron cikin gida Nijeriya da na ƙasashen ƙetare a cikin wannan kasuwa kuma akwai nau’in ɗanyen kayan abinci na garin kwaki da hatsi da shinkafa da manja da man gyaɗa da kwakwa da lemo da abarba da ayaba da ƙanana da manyan dabbobi da fatu da ƙiraga da ake sarrafa su zuwa naman kwama sannan ga ɗimbinleburori majiya ƙarfi masu aikin lodin kaya da saukewa da ‘yan kamasho da direbobi, waɗanda aka tanadar wa kowanne sashe da shugaba da mataimakansa domin tsabtace Kasuwar daga rigingimu da kyautata zamantakewa tsakanin ’yan kasuwa da kwastamomi domin samar da zama lafiya da kwanciyar hankali.

’Yan Kasuwa mafi yawancinsu mata ne kowace xauke da kwandon Goro da ta kawo daga qauye domin sayarwa a Kasuwar ta Ore

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC