Yadda ‘yan Arewa ke harkar kayan lambu a Ibadan

Ana sauke manyan motoci 5 dauke da buhu 300 zuwa 400 na kayan abincin duk rana.

Yadda ‘yan Arewa ke harkar kayan lambu a Ibadan

Shugaban Kasuwar Kayan Gwari ta Benjamin Eleyele a Ibadan babban birnin Jihar Oyo, Walin Ibadan Alhaji Dauda Shehu ya ce, jihohin Filato da Kaduna da Kano da Sakkwato ne suke samar da nau’o’in kayan gwari masu gina jiki ga Kudu maso Yamma.

Alhaji Dauda Shehu ya ce Jihar Filato ce kan gaba a fannin samar da irin wadannan kayan abinci da suka hada da kabeji da kokumba da latas da tumatir da karas da Dankalin Turawa da koren attarugu da danyen wake ‘green beans’ da sauransu.

Ya fadi haka ne a lokacin da yake zagayawa da Aminiya sassan kasuwar.

Kan amfanin kasuwar ga ’yan Arewa, Walin na Ibadan, ya ce “Sai godiya ga Allah domin akalla manyan motoci 5 dauke da buhu 300 zuwa 400 na irin kayan abincin da suka dauko daga jihohin 4 ne suke saukewa a kasuwa a kowace rana.

“Bayan sauke kayan akwai kananan ’yan kasuwa daga garuruwan Kudu maso Yamma da suke zuwa sarin kayan don sayarwa ga mabukata a garuruwansu.

“Haka kuma akwai masu shaguna da rumfuna da kuma masu tura baro da suke shiga cikin gari da masu dauka a kawunansu suna talla, dukkansu mutanenmu ne Hausawa da suke amfana da kasuwancin kayan gwarin a jihar,” in ji shi.

Ya ce, “A kowace shekara a lokacin kaka muna samun mutanen da suka fito daga jihohin 4 na Arewa da yawansu ya kai 2,000 da suke zuwa kasuwar don yin kasuwancin kayan gwari na tsawon wata 3 zuwa 4 kafin su koma garuruwansu idan damina ta sauka.

“Sai dai a bana an samu karancin kayan gwarin da ake kawowa daga Jihar Filato dalilin tashe-tashen hankali da jihar ke fama da su.”

Da yake magana kan farashin kayan, Alhaji Dauda Shehu ya ce “Matsalar janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi a bara ya haifar da tashin farashin kayan da muke sayarwa.”

Shugaban ya ce “A irin wannan lokaci a bara muna sayar da buhun Dankalin Turawa a kan Naira dubu 17 zuwa dubu 18, amma a bana farashinsa ya kai Naira dubu 48.

“Shi ma karas da muke sayar da buhu daya a kan Naira 10,000 a bara, yanzu farashin shi ya tashi zuwa Naira 25,000. Tsadar man fetur ce ta haifar da tashin farashin kayan.”

Alhaji Dauda Shehu ya ce “Mun fara gwajin noman rani a nan Kudu bayan Ma’aikatar Gona ta Jihar Oyo ta ba mu filayen noman rani a kusa da wuraren samar da ruwa.

“Mun gayyaci wasu kwararrun manoma daga Arewa suna koya mana yadda ake yin noman kayan gwarin a nan, kuma suna ba mu shawarar yadda za mu cim ma nasara.

“Ita ma Ma’aikatar Gonar tana taimaka mana ta fannin samar mana da takin zamani a farashi mai sauki.”

A kasuwar Aminiya ta ga wasu shaguna da rumfunan da ake kasuwancin wasu abubuwa daban bayan kayan gwarin.

Misali akwai sashen masu kiwon kifi da kantunan sayar da abinci da kayan marmari da shagunan masu aski da sashen ’yan Okada da na leburori dukkansu ’yan Arewa da suka mamaye kasuwar.

A game da tsaro, Alhaji Dauda Shehu ya ce, “Akwai yaranmu da suke aikin hadin gwiwa da ’yan sanda domin kare kasuwar daga miyagu.

“Haka a cikin gari akwai mutanenmu da suke aikin shiga tsakanin kananan ’yan kasuwa da jama’ar gari.”

Aminiya ta yi kicibis da jami’an kiwon lafiya da suka je kasuwar don lura da yadda ake tsaftace kayan abincin da ake sayar wa jama’a.

Alhaji Dauda Shehu ya ce “Wadannan jami’an kiwon lafiya sun saba kawo mana ziyara inda suke ba mu shawara kan yadda za mu tsaftace kasuwar don yaki da kazanta a kasuwanni da gidajen jama’a a jihar.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja